Bulus Ya Kwaɗaitar da Bayarwa Cikin Karimci Domin Yahudiya

Ta wurin misalin ikilisiyoyin Makidoniya, waɗanda suke cikin mawuyacin hali ƙwarai, Bulus ya kwaɗaitar da Korintiyawa su bayar cikin karimci don taimakon 'yan'uwa Kiristoci a Yahudiya. Ya ce ba ya bayar da wannan a matsayin umarni, domin dole ne ayyukan alheri su kasance na son rai, amma yana fatan za su yawaita yin su saboda misalin Kiristi da ƙaunarsa. Ya kira su su kammala tara gudummawar da suka riga suka fara ba tare da ɓata lokaci ba, gwargwadon ƙarfinsu, domin Allah yana daraja yardar mai bayarwa fiye da girman kyautar. Abin da suka bayar za a yi amfani da shi ne kawai don 'yan'uwa matalauta a Yahudiya, waɗanda su ma a nasu lokacin za su iya biya wa Korintiyawa bukatunsu.

58 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Korintiyawa 8:1–15

1 To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya. 2 Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci. 3 Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, 4 sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. 5 Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah. 6 Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi. 7 To, da yake kun fiffita a kowane abu cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin dukan ƙwazo, da kuma cikin ƙaunarku dominmu, sai ku fiffita a wannan aikin alheri ma.

8 Ba umarni nake ba ku ba, sai dai ina so in gwada gaskiyar ƙaunarku ne, ta wurin kwatanta ta da aniyar waɗansu. 9 Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.

10 Ga shawarata a kan abin da ya fi muku kyau a wannan al’amari. Bara ku kuka fara bayarwa, kuka kuma zama na farko wajen niyyar yin haka. 11 Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, ku yi haka gwargwadon ƙarfinku. 12 Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.

13 Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai 14 a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari, 15 kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”

An Aika Titus da 'Yan'uwa Biyu zuwa Korint

Bulus ya gode wa Allah saboda ya sa Titus ya damu da su kamar yadda shi ma ya damu. Himmar Titus ta sa ya ɗauko wannan wasiƙa. Bulus ya gaya musu cewa yana aika wani ɗan'uwa mai kyakkyawan suna ƙwarai tare da Titus, wanda ikilisiyoyin mutanen Makidoniya suka zaɓa domin ya zama shaida kan yadda ake kula da kyaututtukansu, don kada a yi wani zargin laifi game da yadda aka kashe kuɗi masu yawa da aka danƙa musu. Ana kuma aika wani abokin aiki, wanda yake da himma ta musamman a wannan lokaci saboda labarin kyakkyawar zuciyarsu. Bulus ya koya musu yadda za su amsa tambayoyin ƙungiyar 'yan adawa, yana kuma kwaɗaitar da su su nuna wa waɗannan manzanni da ikilisiyoyi shaidar ƙaunarsu da kuma dalilin amincewar Bulus da su.

2 Korintiyawa 8:16–24

16 Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku. 17 Ba kawai ya yarda yă je wurinku kamar yadda muka roƙe shi yă yi ba, amma ya so yă zo kamar yadda ya riga ya yi niyya. 18 Ga shi mun aiko ɗan’uwanmu nan tare da shi, wanda ikkilisiyoyi duka suna yabo saboda hidimarsa ga bishara. 19 Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu. 20 Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake. 21 Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.

22 Ban da wannan kuma, mun aiko da ɗan’uwanmu tare da su, wanda ya sha tabbatar mana da ƙwazonsa ta hanyoyi iri-iri, musamman yanzu, domin ya amince da ku da gaske. 23 Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da ’yan’uwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne. 24 Saboda haka, ku nuna wa waɗannan mutane shaidar ƙaunarku, da kuma dalilin taƙamarmu da ku, domin ikkilisiyoyi su gani.

An Aika Titus a Gaba Domin Ya Shirya Gudummawar

Bulus ya ci gaba da tunatar da Korintiyawa cewa ya yi wa Makidoniyawa alfahari da shirinsu na bayarwa shekara guda da ta wuce. Tun daga lokacin, da ya ji daga wurin Titus cewa sun yi sakaci a wannan, yana aika Titus da abokan tafiyarsa su shirya gudummawar kafin ya iso, don kada ya ji kunyar alfaharin da ya yi da su, kuma don su bayar da abin da za su bayar da yardar rai, ba kamar an tilasta wa masu haɗama su bayar ba.

2 Korintiyawa 9:1–5

1 Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka. 2 Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki. 3 Amma ina aika ’yan’uwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan al’amari ta zama a banza, sai dai domin yă zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance. 4 Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku. 5 Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.

Ku Shuka a Yalwace, Ku Bayar da Farin Ciki

Bulus ya kwaɗaitar da Korintiyawa su zama masu karimci, domin za a sāka mana a wata duniya gwargwadon ayyukanmu a nan. Ya kwaɗaitar da su su bayar da farin ciki. Allah yana da ikon sa wa ayyukansu albarka, ya kuma wadata su da isassun kayan wannan duniya, domin bukatunsu da kuma ayyukansu na taimakon mabukata. Waɗanda aka taimaka wa suna farin ciki, suna gode wa Allah, suna kuma addu'a ga waɗanda suka bayar.

2 Korintiyawa 9:6–15

6 Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. 7 Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. 8 Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. 9 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Ya ba gajiyayyu hannu sake,

ayyukansa na alheri madawwama ne.”

10 To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. 11 Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.

12 Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. 13 Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. 14 A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. 15 Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!

Bulus Ya Yi Gargaɗi Cewa Zai Iya Nuna Ƙarfin Hali a Gabansu

Yanzu Bulus ya yi magana musamman ga malamin ƙaryar da mabiyansa, waɗanda suka ɓata masa suna ta wurin cewa shi mai ladabi ne kawai sa'ad da yake tare da su, amma mai ƙarfin hali ne a wasiƙunsa sa'ad da ba ya nan. Ko da yake ba ya nan, yanzu yana roƙon waɗanda suke zarginsa da yin rayuwa bisa ga jiki, cikin salon ba'a, kada su ba shi dalilin nuna ƙarfin halinsa sa'ad da yake tare da su. Ya bayyana iko na musamman da Allah ya ba shi domin ya rushe duk abin da yake gāba da bishara, yana kuma tabbatar cewa yana shirye ya nuna ikonsa na mu'ujiza don hukunta rashin biyayya da zarar biyayyar waɗanda suka tuba daga laifinsu a cikinsu ta cika.

2 Korintiyawa 10:1–6

1 Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da sanyin hali na Kiristi, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” a cikinku, amma “mai matsawa” sa’ad da nake rabe da ku! 2 Ina roƙonku cewa sa’ad da na zo kada ku tilasta ni in matsa muku, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha’anin duniya ne. 3 Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi. 4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. 5 Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. 6 A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.