Bulus Ya Tsauta wa Yin Hukunci Bisa ga Kamanni

Bulus ya tsauta wa malamin ƙaryar saboda yin hukunci bisa ga kamannin waje. Ya kuma nemi a amince da shi a matsayin mai hidimar Kiristi, yana yin alfahari da ikon da aka ba shi domin gina su. Ya sake ambaton rahotannin ɓatanci na abokin hamayyarsa cikin salon ba'a, yana kuma kiransa ya gane, daga sakamakon ikon Bulus da aka riga aka gani sa'ad da ba ya nan wajen hukunta mutumin da ya yi lalata da danginsa, cewa ikon zai kasance mai girma haka ma sa'ad da yake tare da su.

58 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Korintiyawa 10:7–11

7 Kuna duban abubuwa bisa-bisa ne kawai. In wani ya ganin cewa shi na Kiristi ne, ya kamata yă sāke lura cewa kamar yadda yake na Kiristi, haka mu ma muke. 8 Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki. 9 Ba na so yă zama kamar ina ƙoƙari in tsorata ku ne da wasiƙuna. 10 Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.” 11 Ya kamata irin waɗannan mutane su gane cewa abin da muke faɗa a cikin wasiƙunmu sa’ad da ba ma nan tare da ku, shi muke aikatawa sa’ad da muke nan.

Yin Alfahari Cikin Iyakokin da Allah Ya Kafa

Da yake ci gaba da maganarsa ta habaici, Bulus ya bayyana cewa ba ya kuskura ya kwatanta kansa da malamin ƙarya, wanda yake auna kansa da kansa kaɗai, yana kuma yabon kansa saboda abin da ya yi a Korint. Bulus kuwa yana so ya yi farin ciki ne kawai a cikin iyakokin da Allah ya kafa masa, waɗanda biyayyarsa gare su ta sa har ya kai ga Korintiyawa. Ya ƙi yin fahariya da aikin waɗansu, kamar yadda malamin ƙarya yake yi, yana kuma fatan yin wa’azin bishara a ƙasashen da ba a taɓa yin wa’azinta ba. Domin ba wanda yake taƙama da aikin waɗansu ne ake amincewa da shi ba, sai dai wanda yake wa’azi domin ɗaukakar Allah, yake kuma samun yabo daga Allah, wanda baye-bayen Ruhu suke nunawa.

2 Korintiyawa 10:12–18

12 Ba za mu yi ƙarfin halin lissafta kanmu, ko mu kwatanta kanmu da waɗansu masu yabon kansu ba. Sa’ad da suke gwada kansu da kansu, da kuma kwatanta kansu da kansu, ba su da hikima. 13 Amma mu kam, ba za mu yi taƙama mu zarce iyakarmu ba, sai dai za mu yi taƙama cikin filin da Allah ya ƙayyade mana, filin kuwa ya kai har zuwa wurinku. 14 Ba mu wuce gona da iri a taƙamarmu ba, kamar yadda zai zama, da a ce ba mu zo wurinku ba, gama mun kai har wurinku da bisharar Kiristi. 15 Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba tă kuma shafi aikin waɗansu ba. Sai dai muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku yă riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske. 16 Saboda mu iya yin wa’azin bishara a yankunan da suke gaba da ku. Gama ba ma so mu yi taƙama game da aikin da aka riga aka yi a sashen wani. 17 Amma, “Duk mai yin taƙama, sai ya yi taƙama da Ubangiji.” 18 Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.

Bulus Yana Tsoron Ana Ɓatar da Korintiyawa

Da aka zarge shi da yabon kansa, Bulus ya roƙi Korintiyawa su haƙura da hakan a wannan karon, domin yana tsoron cewa malamin ƙarya ya raba waɗanda ya jawo ga Kiristi da shi. Ya yi ɗokin gabatar da su a ranar shari’a kamar budurwa tsarkakakkiya ga mijin da aka yi mata alkawari. Ya ce da a ce wanda suke kira manzo ya yi musu wa’azin wani Mai Ceto ko wata bishara dabam, ko ya ba su wani Ruhu dabam, da za su iya haƙura da da’awarsa. Ya tabbatar da cewa yana daidai da manyan manzannin Kiristi, kuma ko da yake ba ƙwararre ba ne a magana, ya nuna musu cewa bai rasa ilimin da mai hidimar bishara yake bukata ba.

2 Korintiyawa 11:1–6

1 Ina fata za ku yi haƙuri da ’yar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri. 2 Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla. 3 Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. 4 Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai. 5 Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba. 6 Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.

Dalilin da Ya Sa Bulus Bai Karɓi Lada daga Korint Ba

Bulus ya bayyana dalilin da ya sa ba zai karɓi tallafi daga Korintiyawa ba. Ya ce ba don rashin ƙauna ba ne, kamar yadda maƙiyansa suka nuna, sai dai don ƙaunarsa gare su, da kuma hana malamin ƙarya yin da’awar cewa Bulus yana aiki ne don samun ribar duniya. An kuma yi hakan ne don tilasta wa malamin ƙarya, wanda yake karɓar kyaututtuka a ɓoye, ya daina wannan hali ya bi misalin Bulus. Tun da Shaiɗan da kansa yana ɗaukar kamannin mala’ikan haske, bai kamata a yi mamakin yadda bayin Shaiɗan suke ɗaukar matsayin masu hidima ko manzannin Kiristi ba.

2 Korintiyawa 11:7–15

7 Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta? 8 Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima. 9 Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka. 10 Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa. 11 Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku!

12 Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su. 13 Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. 14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

Bulus Yana Fahariya da Ayyukansa da Wahalolinsa

Bulus ya sake roƙon Korintiyawa su haƙura da fahariyarsa. Tun da waɗanda ba manzanni ba suke fahariya da abubuwan jiki, shi ma dole ne ya yi fahariya da kaciyarsa da asalinsa na Bayahude don ya kāre matsayinsa na manzo. Ya nuna cewa Korintiyawa sun yi haƙuri fiye da kima da danniyar waɗansu, ya kuma bayyana yadda malamin ƙarya yake bi da su. Game da zargin cewa shi mai ƙasƙantaccen asali ne, marar ƙarfi, wanda bai cancanci zama manzo ba, ya tabbatar da cewa idan wani yana da dalilin yin fahariya, shi ma yana da shi. Ya kwatanta kansa da malamin ƙarya a waɗannan fannoni, ya kuma nuna fifikonsa ta wurin nuni ga ayyukansa da wahalolinsa, da kuma yadda yake kula ƙwarai da ikkilisiyoyi da kowane mutum, yana tausaya wa marasa ƙarfi, yana aiki da himma don dawo da waɗanda aka ɓatar. Yana fahariya da rauninsa, musamman yadda ya tsere daga Damaskus, domin a nuna ikon Allah.

2 Korintiyawa 11:16–33

16 Ina sāke faɗa, kada wani yă ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama. 17 A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa. 18 Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi. 19 Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna! 20 Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska. 21 Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba!

Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne. 22 In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka. 23 In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. 24 Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. 25 Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. 26 Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. 27 Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. 28 Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi. 29 Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?

30 In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina. 31 Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. 32 A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni. 33 Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.