Wahayoyi da Abubuwan da Aka Bayyana wa Bulus
Bulus ya bayyana cewa idan aka tilasta masa yin fahariya saboda su, zai yi fahariya da abubuwan da aka bayyana masa da wahayoyin da ya gani. Amma game da kansa, ya ƙuduri niyyar yin fahariya da rauninsa da wahalolinsa kaɗai. Ko da yake zai iya yin fahariya yana faɗar gaskiya sarai, ya kame kansa don kada wani ya ɗauke shi fiye da yadda yake.
58 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Dole in ci gaba da yin taƙama. Ko da yake ba za tă amfane ni ba, zan yi magana a kan ru’uyoyi da wahayoyi waɗanda na karɓa daga Ubangiji. 2 Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani. 3 Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani, 4 an ɗauke shi ne zuwa aljanna. Ya ji waɗansu abubuwa waɗanda ba zai iya faɗarsu da kalmomi ba, abubuwan da ba a ba wa mutum damar faɗi. 5 Zan yi taƙama game da mutum irin wannan, sai dai ni ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan rashin ƙarfina. 6 Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata.
Ikon Allah Yana Cika Cikin Rauni
Bulus ya bayyana cewa ciwon jikinsa, wanda ƙungiyar masu adawa ta zarge shi a kansa, Allah ne ya aiko shi don kada ya yi girman kai saboda wahayoyi masu ɗaukaka da aka ba shi. Ba za a kawar da ciwon ba, domin ikon Allah yana cika ta wurin rauninsa. Saboda haka yana jin daɗin tsanantawa, rauni, da makamantansu, domin gwargwadon rauninsa ne alherin Allah da yake zaune a cikinsa yake ba shi ƙarfi. Halin Korintiyawa ya tilasta masa yin fahariya ba da son ransa ba. Da ya kamata su kāre matsayinsa na manzo, domin sun san cewa bai gaza manyan manzanni ta kowace hanya ba.
7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. 10 Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
11 Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kāsa waɗannan mafiffitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.
Ziyarar Bulus Mai Zuwa da Fargabarsa
Bulus ya ci gaba da tabbatar da matsayinsa na manzo ta wurin mu’ujizozinsa da baye-bayen ruhaniya da ya ba su. Ya tambaye su ta wace hanya ya mai da su ƙasa da sauran ikkilisiyoyi, in ban da cewa shi kansa bai zama musu nauyi ba. Ya bayyana niyyarsa ta ziyarce su ba tare da ya zama musu nauyi ba har yanzu, domin a matsayinsa na ubansu na ruhaniya, ba kayan ’ya’yansa na ruhaniya yake nema ba, sai dai cetonsu. Ya musanta zancen da abokan adawarsa suke yi na cewa da wayo ya ƙi karɓar kuɗi daga wurinsu, ta wurin nuna halin rashin son kai na Titus da mataimakinsa. Ya tabbatar da cewa ya aika Titus gare su ba don ya ba da uzurin rashin zuwa da kansa ba (2 Korintiyawa 1:23), sai dai don ya ba marasa biyayya lokaci su gyara rayuwarsu. Yana tsoron cewa idan ya ziyarce su, dole ne ya yi baƙin ciki a kan waɗanda ba su tuba daga zunubai da ƙazantar da suka aikata ba, ya kuma hukunta su.
12 Abubuwan da suke tabbatar da manzo, alamu, abubuwa da kuma ayyukan banmamaki, an aikata su a cikinku da matuƙar nacewa. 13 Ta yaya ne darajarku ba tă kai ta sauran ikkilisiyoyi ba, ko kuwa don dai ban nawaita muku ba ne? Ku gafarta mini wannan laifi!
14 Yanzu a shirye nake in ziyarce ku sau na uku, ba zan kuma nawaita muku ba, don ba kayanku nake so ba, ku nake so. Gama ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran. 15 Don haka ina farin ciki in kashe dukan abin da nake da shi a kanku, har in ba da kaina ma dominku. In na ƙaunace ku fiye da haka, za ku rage ƙaunarku gare ni ne? 16 To, shi ke nan, ban nawaita muku ba. Ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara! 17 Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku? 18 Na roƙi Titus ya zo wurinku. Na kuma aiki ɗan’uwanmu tare da shi. Ko Titus ya cuce ku ne? Ba ruhu ɗaya yake bi da mu ba? Ba kuma hanya guda muka bi ba?
19 Ko tun dā can, kuna tsammani muna kāre kanmu a gare ku ne? A gaban Allah muke magana, kamar waɗanda suke cikin Kiristi. Ƙaunatattuna, kome da muke yi, muna yi ne don inganta ku ne. 20 Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi. 21 Ina tsoro kada sa’ad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba.
Bulus Ba Zai Ƙyale Waɗanda Suke Yin Zunubi Ba
Bulus ya ci gaba da tabbatar wa Korintiyawa cewa sa’ad da ya sake ziyarce su, za a hukunta su bisa ga shaidar shaidu biyu ko uku, kamar yadda Doka da bishara suka tanada. Ya tunatar da su game da barazanar da ya yi a dā da kuma hukuncin mutumin da ya aikata lalata tsakanin dangi. Ya tabbatar wa duk waɗanda suka riga suka yi zunubi, da duk waɗanda suke ci gaba da yin zunubi, cewa ba zai ƙyale su su ma ba, musamman da yake suna neman shaidar cewa Kiristi yana magana ta wurinsa. Kiristi ya riga ya bayyana kansa ta wurin Bulus, ba cikin rauni ba sai cikin ƙarfi, ta wurin manyan ayyukan da ya ba shi ikon yi. Ko da yake an gicciye Kiristi cikin raunin yanayinsa na ɗan Adam, har yanzu yana rayuwa ta wurin ikon Allah. Mu ma muna da raunin jiki tare da shi, amma Bulus zai nuna cewa suna rayuwa tare da shi ta wurin ikon Allah, wanda zai bayyana a cikin hukuncin da za su yi wa Korintiyawa.
1 Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.” 2 Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan, 3 da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku. 4 Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima.
An Ce Korintiyawa Su Binciki Kansu
Tun da ƙungiyar masu adawa ta nemi shaidar cewa Kiristi yana tare da Bulus, yanzu ya kira su su binciki kansu su ga ko suna da baye-bayen ruhaniya da suke tabbatar da kasancewar Kiristi. Yana fatan cewa ko da sun rasa wannan shaida, ba za a tarar shi ya rasa iko na mu’ujiza ba, idan yana bukatar amfani da shi don hukunta su sa’ad da ya zo. Yana roƙon Allah su yi halin kirki, domin ya fi ɗokin tubansu nesa da samun damar amfani da shaidunsa don ya nuna ƙarfinsa. Ya tabbatar da cewa ana iya amfani da iko na mu’ujiza ne kawai don goyon bayan gaskiya. Bulus ya rubuta waɗannan abubuwa domin kamalarsu, don kada idan yana tare da su ya zama dole ya yi amfani da tsanani da ikon mu’ujiza da aka ba shi domin gina ikkilisiya.
5 Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin. 6 Ina fata za ku gane cewa ba mu fāɗi gwajin ba. 7 Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne. 8 Kai, ba dama mu saɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar. 9 Murna muke sa’ad da ba mu da ƙarfi, ku kuwa kuna da ƙarfi. Addu’armu ita ce, ku zama cikakku. 10 Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
Bankwana da Albarkar Bulus
Bayan ya gama tsawata wa ƙungiyar masu adawa, Bulus ya yi magana da dukan ikkilisiya, ya ba su umarnai iri-iri. Ya ƙare da gaisuwa da albarkarsa a matsayinsa na manzo.
11 A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.
12 Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.
13 Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
14 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.
Bulus Ya Juya Daga Korint Ya Koma Makidoniya
Bulus ya dawo daga Akayya da Korint zuwa Makidoniya, yana aika abokan tafiyarsa su riga shi zuwa Toruwas.
4 Sai Sofater ɗan Fairrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tessalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi. 5 Waɗannan mutane suka sha gaba suka kuma jira mu a Toruwas.