Bulus Ya Rubuta wa Romawa

A kan hanyarsa daga Akayya zuwa Makidoniya, Bulus ya rubuta wasiƙarsa daga Korint zuwa ga Yahudawa da Al’ummai na Roma. Ya nuna wa Al’ummai da hujjoji cewa ba falsafarsu da ake yabawa ƙwarai, ba ɗabi’arsu ta gari, ba kuma hasken hankalin ɗan Adam ne zai iya sa a ɗauke su masu adalci a gaban Allah ba. Ya nuna wa Yahudawa da hujjoji cewa ba saninsu na Dokar Musa ko biyayyarsu gare ta ne zai iya sa a ɗauke su masu adalci ba. Bangaskiya ga Kiristi kaɗai ce hanyar ceto ga dukan ’yan Adam, kuma haka yake a koyaushe.

58 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bulus Ya Gai da Romawa

Bulus ya tabbatar da ikonsa a matsayinsa na manzo. Ya nuna yanayin Kiristi na ɗan Adam ta wurin zuriyarsa daga Dawuda, da kuma yanayinsa na Allah ta wurin tashinsa daga matattu. Ya bayyana cewa ya karɓi aikinsa daga Kiristi don ya yi wa Al’ummai wa’azin bishara, waɗanda su ne mafi yawan ikkilisiyar Roma, don haka yana da ikon yi musu magana.

Romawa 1:1–7

1 Bulus, bawan Kiristi Yesu, kirayaye don yă zama manzo, keɓaɓɓe kuma domin bisharar Allah. 2 Bisharar da Allah ya yi alkawari tuntuni ta bakin annabawansa a cikin Nassosi Masu Tsarki 3 game da Ɗansa. Wanda bisa ga mutuntakarsa, zuriyar Dawuda ne. 4 Wanda bisa ga Ruhun tsarki, an shaida shi da iko cewa shi Ɗan Allah ne ta wurin tashinsa daga matattu. Wannan bishara kuwa game da Yesu Kiristi Ubangijinmu ne. 5 Ta wurinsa da kuma saboda sunansa, muka sami alheri muka kuma zama manzanni don mu kira mutane daga cikin dukan Al’ummai zuwa ga biyayyar da take zuwa daga bangaskiya. 6 Ku ma kuna cikin waɗanda aka kira ku zama na Yesu Kiristi.

7 Wannan wasiƙa ce zuwa ga dukanku da kuke a Roma waɗanda Allah yake ƙauna, waɗanda kuma ya kira domin su zama tsarkaka.

Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma daga Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Bulus Yana Ɗokin Ziyartar Romawa

Bulus yana farin ciki da bangaskiyarsu. Ya faɗi babban burinsa na ziyartarsu, domin ya ƙarfafa su ta wurin ba su wata baiwar ruhaniya, wadda za ta zama shaida da shi da su za su ƙarfafa juna, su kuma ta’azantar da juna cikin bangaskiya ga Kiristi. Da yake an naɗa shi ya yi wa dukan al’ummai wa’azin bishara, har yanzu yana so ya yi wa Romawa wa’azinta saboda dalilai uku. Na farko, ya tabbatar cewa ita ce ikon Allah domin ceton Bayahude da kuma Ba’al’umme. Na biyu, a cikin bishara kaɗai ake bayyana adalcin Allah, tare da sharaɗi guda ɗaya na samun kuɓuta da karɓuwa a wurinsa, wato ta wurin bangaskiya ba ta wurin ayyuka ba. Na uku, bishara ta fi Dokar Musa girma, ko haske ko dokar lamiri, waɗanda dukansu suke yanke wa dukan waɗanda suka yi zunubi hukuncin mutuwa ba tare da wani sharaɗi ba.

Romawa 1:8–18

8 Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya. 9 Allah, wanda nake bauta wa da dukan zuciyata cikin wa’azin bisharar Ɗansa, shi ne shaidata a kan yadda kullum ina tunawa da ku 10 cikin addu’o’ina a kowane lokaci; ina kuma addu’a cewa a ƙarshe in Allah ya yarda hanya za tă buɗe mini in zo wurinku.

11 Ina marmarin ganinku don in ba ku wata baiwar ruhaniya, don ku yi ƙarfi 12 wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu. 13 Ina so ku sani ’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai.

14 Ina da hakki ga Hellenawa da waɗanda ba Hellenawa ba, ga masu hikima da kuma marasa azanci. 15 Shi ya sa na yi himma sosai in yi muku wa’azin bishara ku ma da kuke a Roma.

16 Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai. 17 Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”

18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu,

Al’ummai Sun San Allah Amma Suka Juya Masa Baya

Bulus ya nuna cewa Al’ummai suna da isasshiyar shaida game da Allah da kamalarsa mai ɗaukaka a cikin ayyukan halitta. Domin ya nuna cewa babu wanda zai iya samun ceto ta wurin dokar halitta, ya lissafa munanan halayen Hellenawa, waɗanda suka kai matsayi mafi girma na ilimi da hikimar ɗan Adam. Ya tabbatar cewa sun san Allah amma suka ɓoye saninsu game da shi, har zukatansu suka daina ganin gaskiya, suka kafa bautar abin da aka halitta a maimakon Mahalicci. Saninsu game da Allah ya tabbatar musu da hukuncin da yake jiran laifofinsu, duk da haka suka ci gaba da aikata su, suka kuma ƙarfafa wasu su yi haka.

Romawa 1:19–32

19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.

21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. 25 Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.

26 Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. 27 Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.

28 Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. 29 Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, 30 da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; 31 su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. 32 Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.

Yahudawa Suna da Laifin Irin Waɗannan Zunubai

Bulus ya san sarai yadda Yahudawa suke saurin haɗa kai wajen yin Allah wadai da Al’ummai saboda zunubansu. Yanzu yana ƙoƙarin tabbatar wa Yahudawa cewa su masu zunubi ne, yana bayyana cewa su ma suna da laifin irin waɗannan ayyukan. An san cewa hukuncin Allah a kan irin waɗannan laifofi, wanda aka bayar a cikin Dokarsu, gaskiya ne, kuma dukan masu aikata su, ko Yahudawa ne ko Al’ummai, ba za su tsira daga hukuncin ƙarshe na Allah ba.

Romawa 2:1–3

1 Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa. 2 Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne. 3 Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?

Allah yana hukunta Yahudawa da Al’ummai daidai

Bulus ya gargaɗi Yahudawa cewa gatan da suke da shi zai ƙara musu hukunci idan ba su tuba ba. Ya musanta cewa hukuncin Allah yana bambanta tsakanin Yahudawa da Al’ummai, ya kuma tabbatar da cewa za a ba Yahudawa da Al’ummai azaba iri ɗaya da lada iri ɗaya daidai wa daida, domin Allah ba ya nuna son kai.

Romawa 2:4–11

4 Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne?

5 Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci. 6 Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.” 7 Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. 8 Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. 9 Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai, 10 amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai. 11 Gama Allah ba ya nuna bambanci.

Za a Yi wa Kowa Hukunci Bisa ga Hasken da Ya Samu

Bulus ya ƙara bayyana cewa za a yi wa dukan mutane hukunci bisa ga yawan haske da ilimin da suka samu. Ba Yahudawa waɗanda suke ikirarin bin Doka amma ba sa aikata ta ba, sai dai Al’ummai da dukan waɗanda suke rayuwa bisa ga Dokar ba tare da sun sami iliminta da aka bayar daga baya ba, su ne za su sami tagomashi a wurin Allah a babbar ranar, lokacin da za a yi wa dukan mutane hukunci ta wurin dokar lamiri da ta bangaskiya, bisa ga bisharar Allah.

Romawa 2:12–16

12 Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su. 13 Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci. 14 Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar. 15 To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su. 16 Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.