Sanin Doka Ba Zai Kuɓutar da Bayahude Ba

Bulus ya nuna cewa sanin addini kawai ba zai iya kuɓutar da Bayahude ba. Karya Dokar Musa a fili da malaman attaura da shugabannin Yahuda suke yi a halayensu, waɗanda aka naɗa su koyar da jama’a, ya tabbatar da cewa Dokar ba ta da ikon ceto. Ya tabbatar da zargin daga Nassosinsu.

58 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Romawa 2:17–24

17 To, kai, da kake kiran kanka mutumin Yahuda; in kana dogara ga doka kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah; 18 in ka san nufinsa ka kuma amince da abin da yake mafifici domin an koyar da kai bisa ga doka; 19 in ka tabbata cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga waɗanda suke cikin duhu, 20 mai koyar da masu wauta, malamin jarirai, domin a cikin dokar ce akwai sani da gaskiya 21 to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake wa’azi kada a yi sata, kana sata? 22 Kai da kake cewa wa mutane kada su yi zina, kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana wa haikali fashi? 23 Kai da kake taƙama da doka, kana nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin karya dokar? 24 Kamar yadda yake a rubuce, “Ana saɓon sunan Allah a cikin Al’ummai saboda ku.”

Kaciya Ba Ta da Amfani Ba Tare da Biyayya Ba

Bulus ya ci gaba da nuna cewa kaciya, wadda Yahudawa suke taƙama da ita a matsayin alamar zuriyarsu daga Ibrahim da kuma gatansu na musamman a matsayin zaɓaɓɓun mutanen Allah, ba za ta amfane su da kome ba sai sun kiyaye Doka. Ta wurin karya Doka, Bayahude ya rasa gatansa, bai kuma fi Ba’al’umme marar kaciya ba. Allah zai karɓi Al’ummai waɗanda suke cika wajibai na Doka, ya kuma shigar da su cikin zaɓaɓɓun mutanensa. Wanda yake ikirarin addini a zahiri kawai ba ɗan Ibrahim ba ne; sai mai tsarkin ruhaniya kaɗai ne ɗansa na gaskiya.

Romawa 2:25–29

25 Kaciya tana da amfani in kana kiyaye dokar, amma in kana karya dokar, ka zama kamar ba a yi maka kaciya ba. 26 In marasa kaciya suna kiyaye dokar, ashe, ba za a ɗauke su kamar an yi musu kaciya ba? 27 Wanda ba shi da kaciya ta jiki duk da haka yana biyayya da dokar zai iya hukunta ka, kai da kake karya dokar, ko da yake kana da rubutaccen tsarin dokar an kuma yi maka kaciya.

28 Mutum ba mutumin Yahuda ba ne in shi mutumin Yahuda ne kawai a jiki, haka kuma kaciya ba a waje ko a jiki kawai ba. 29 A’a, mutum mutumin Yahuda ne in shi mutumin Yahuda ne a zuci; kuma kaciya ita ce kaciya ta zuci, ta wurin Ruhu, ba ta wurin rubutaccen doka ba. Irin wannan mutum yana samun yabo daga Allah ne, ba ɗan adam ba.

Gatan Bayahude da Amincin Allah

Yanzu da Bulus ya tabbatar wa Yahudawa da Al’ummai duka cewa su masu zunubi ne, ya ci gaba da karyata son zuciyar Yahudawa. Ya kawo wani mai tambayar ta wace hanya, to, aka fi nuna wa ’ya’yan Ibrahim tagomashi fiye da Al’ummai. Bulus ya amsa, “An ba su amanar ainihin kalmomin Allah.” Sai Bayahuden ya tambaya ko, da yake wasu daga cikin al’ummarsu ba su gaskata waɗannan kalmomi ba, rashin bangaskiyarsu zai soke alkawuran Allah. A amsarsa Bulus ya nace cewa rashin bangaskiyarsu ya tabbatar da gaskiyar Allah da alkawuransa, domin raunin ɗan Adam ya karya sharuɗɗan da alkawuran suka dogara a kansu. Sai Bayahuden ya tambaya, “Idan rashin bangaskiyarsu yana ƙara nuna adalcin Allah, ashe, Allah ba zai zama marar adalci ba idan ya hukunta su?” Bulus ya nuna cewa Allah ba zai iya zama marar adalci ba, domin da haka ne, ta yaya zai iya hukunta duniya? Bayahuden ya sake maimaita hujjar. Bulus ya ƙi ta, yana cewa irin wannan hali zai zama koyar da mutane su aikata mugunta domin alheri ya fito. Waɗanda suke riƙe da irin wannan ra’ayi sun cancanci hukuncin da aka yanke musu.

Romawa 3:1–8

1 To, mece ce ribar zama mutumin Yahuda, ko kuwa mene ne amfanin kaciya? 2 Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah.

3 Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah? 4 Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana,

ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.”

5 Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.) 6 Sam, ko kusa! Da a ce haka ne, ta yaya Allah zai shari’anta duniya? 7 Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, ta yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?” 8 In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su.

Yahudawa da Al’ummai Duka Suna Ƙarƙashin Zunubi

Yanzu Bayahuden ya tambaya ko Yahudawa ba su da dalilai na samun gata fiye da Al’ummai. Bulus ya sake tabbatar da abin da ya riga ya faɗa, cewa Yahudawa da Al’ummai duka suna ƙarƙashin zunubi. An tabbatar da zunubin Yahudawa daga Nassosinsu, waɗanda suka yarda cewa hurarru ne daga Allah. Ba wanda za a iya kuɓutar da shi ta wurin doka, ko ta Musa ko ta halitta, wadda za ta iya ba da sanin zunubi da hukuncinsa kawai.

Romawa 3:9–20

9 To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi. 10 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya;

11 babu wani mai fahimta,

babu wani mai neman Allah.

12 Duk sun kauce gaba ɗaya,

sun zama marasa amfani;

babu wani mai aikata nagarta,

babu ko ɗaya.”

13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,

harsunansu suna yin ƙarya.”

“Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”

14 “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”

15 “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;

16 hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,

17 ba su kuma san hanyar salama ba.”

18 “Babu tsoron Allah a idanunsu.”

19 Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah. 20 Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.

Samun Kuɓuta Kyauta Ta Wurin Bangaskiya ga Yesu Kiristi

Da yake Doka ta kāsa kuɓutarwa gaba ɗaya, Bulus ya bayyana cewa hanya ɗaya tilo ta samun kuɓuta ita ce ta wurin bangaskiya ga Yesu Kiristi. Ana koyar da wannan a cikin Doka da Annabawa, kuma ana miƙa shi ga Bayahude da Ba’al’umme daidai, waɗanda aka tabbatar musu daidai cewa masu zunubi ne, domin a wurin Allah babu son kai. Kuɓuta kyautar Allah ce ga kowa, ta wurin bangaskiya, ta wurin hadayar kafara da fansar Kiristi Yesu, don haka babu wurin taƙama.

Romawa 3:21–27

21 Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.

27 To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya.

Bangaskiya Kaɗai Tana Kuɓutarwa Kuma Tana Tabbatar da Doka

Bulus ya kammala hujjar ta wurin bayyana cewa a ƙarƙashin bishara, Bayahude ko Ba’al’umme ba zai iya samun kuɓuta ba sai ta wurin bangaskiya kaɗai, ba tare da wani taimako daga ayyukan Doka ba. Da yake Allah yana ɗaukar Al’ummai da Yahudawa daidai, an tanadar musu hanya ɗaya ta samun kuɓuta. Ana tabbatar da Doka, ko ana cika ta, ta wurin bangaskiya.

Romawa 3:28–31

28 Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba. 29 Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma, 30 da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin. 31 To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.