Ibrahim Ya Sami Kuɓuta Kafin A Yi Masa Kaciya

Bulus ya tabbatar cewa Ibrahim bai sami kuɓuta ta wurin ayyukan Doka ba. Ba shi da abin da zai yi taƙama da shi. Ya sami kuɓuta ta wurin bangaskiya, ta wurin alheri da tagomashi, ba a matsayin bashi ba, wato ladan da ake bin sa saboda ayyukansa. Dawuda ya shaida wannan hanyar samun kuɓuta, kamar yadda gaskiyar cewa Ibrahim ya sami kuɓuta tun bai yi kaciya ba ta nuna, kuma daga baya ya karɓi alamar kaciya a matsayin hatimin kuɓutarsa ta wurin bangaskiya, domin ya zama uban ruhaniya na Bayahude da Ba’al’umme, waɗanda za su sami haƙƙin kuɓuta daidai bisa ga sharaɗi guda ɗaya na bangaskiya kaɗai.

58 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Romawa 4:1–12

1 To, me za mu ce Ibrahim kakan kakanninmu ya gani game da wannan batu? 2 In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan, amma ba a gaban Allah ba. 3 Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.”

4 To, sa’ad da mutum ya yi aiki, ba a lissafta ladan aikinsa a matsayin kyauta, sai dai a matsayin hakkinsa. 5 Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne. 6 Dawuda ya faɗi haka sa’ad da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya lissafta adalci a gare shi, ba don yă yi ayyuka ba.

7 “Masu albarka ne

waɗanda aka gafarta laifofinsu,

waɗanda aka kuma rufe zunubansu.

8 Mai albarka ne mutumin

da Ubangiji ba zai taɓa lissafta zunubansa ba.”

9 Shin, wannan albarkar a kan masu kaciya ne kawai, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Mun sha faɗi cewa an lissafta bangaskiyar Ibrahim adalci ne a gare shi. 10 A kan wane hali ne aka lissafta masa? Bayan da aka yi masa kaciya ne, ko kuwa kafin kaciyar? Ba bayan an yi masa kaciya ba ne, amma kafin a yi masa kaciya! 11 Ya kuma karɓi alamar kaciya, hatimin adalcin da yake da shi ta wurin bangaskiya tun yana marar kaciya. Saboda haka fa, ya zama mahaifin dukan waɗanda suka gaskata domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba. 12 Ya kuma zama mahaifin masu kaciya waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba amma har ma suna bin gurbin bangaskiyar da mahaifinmu Ibrahim yake da ita kafin aka yi masa kaciya.

Alkawarin da Aka Yi wa Ibrahim Ya Haɗa da Al’ummai

Bulus ya ci gaba da hujjarsa ta wurin bayyana wa Yahudawa cewa alkawarin da aka yi wa Ibrahim da kansa ya nuna cewa dukan duniya za ta zama magadansa ta wurin bangaskiyarsa. Amma idan Yahudawa kaɗai za su zama magadan alkawarinsa, to an mai da bangaskiya banza, an kuma soke alkawarin da aka bayar bisa ga sharaɗin bangaskiya. Domin Doka, ba tare da jinƙai ba, tana sa mai zunubi ya fuskanci hukunci, kuma idan babu Doka ba za a sami ƙa’idar abin da ya wajaba a yi ba, don haka babu zunubi. Saboda haka aka ba da alkawarin ta wurin bangaskiya, alherin Allah na kyauta yana haɗa da ’ya’yan Ibrahim na jiki da na ruhaniya. Samun kuɓutar Ibrahim tun bai yi kaciya ba ya tabbatar da cewa ana karɓar Al’ummai. Shi kansa alkawarin da aka tabbatar wa Ibrahim a matsayin uban al’ummai da yawa ya tabbatar da haƙƙin Al’ummai na samun dukan albarkun fansa.

Romawa 4:13–22

13 Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya. 14 Gama da a ce masu kiyaye doka ne magāda, ai, da bangaskiya ba ta da amfani, alkawarin kuma ya zama banza, 15 domin doka tana jawo fushi ne. Kuma inda babu doka babu keta umarni ke nan.

16 Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka. 17 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.

18 Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za tă zama.” 19 Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne, da yake yana da shekara wajen ɗari, mahaifar Saratu kuma matacciya ce. 20 Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah, 21 yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika abin da ya yi alkawari. 22 Shi ya sa, “aka lissafta adalci a gare shi.”

An Rubuta Bangaskiyar Ibrahim Domin Mu

An rubuta cewa Allah ya karɓi Ibrahim ta wurin bangaskiya domin mu. Wannan yana nuna mana cewa hanya ɗaya tilo ta samun ceto a wurin Allah ita ce ta wurin bangaskiya ga Ɗansa, wanda ya sha wahala saboda zunubanmu, ya kuma tashi daga matattu a matsayin tabbacin sulhuntawarmu, ko kuɓutarmu.

Romawa 4:23–25

23 Kalmomin nan, “aka lissafta a gare shi” ba a rubuta su saboda shi kaɗai ba ne, 24 amma saboda mu ma, mu da Allah zai lissafta adalci, mu da muka ba da gaskiya gare shi da ya tashe Yesu Ubangijinmu daga matattu. 25 An miƙa shi ga mutuwa saboda zunubanmu, aka kuma tashe shi zuwa rai saboda Allah zai same mu marasa laifi.

Albarkun da Suke Biyo Bayan Samun Kuɓuta

Bulus ya ci gaba da lissafa manyan albarku da gatan da suke biyo bayan samun kuɓuta ta wurin bangaskiya. Ruhu Mai Tsarki da aka ba Al’ummai yana nuna ƙaunar Allah gare su, wadda mutuwar Kiristi dominsu tun suna arna ta tabbatar. Saboda haka Al’ummai suna da begen ceto ta wurin Kiristi iri ɗaya, da kuma dalilai iri ɗaya na yin farin ciki cikin Allah, kamar zuriyar Ibrahim ta jiki, domin an sulhunta su da Allah ta wurin kafara ɗaya.

Romawa 5:1–11

1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

6 Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. 7 Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

9 Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! 10 Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa! 11 Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.

Zunubi na Asali Ta Wurin Adamu, Rai Ta Wurin Kiristi

Yanzu Bulus ya bayyana koyarwar zunubi na asali. Ya nuna cewa ta wurin laifin mutum ɗaya zunubi ya shiga duniya, hukuncin mutuwa kuma ya hau kan dukan mutane, domin dukan waɗanda aka haifa daga baya an haife su da halin zunubi. Mutuwa ta yi mulki ta wurin gurɓacewar halinmu tun kafin a san Dokar Musa. Adamu, wanda yake abin koyi na wanda zai zo kuma shugaban ’yan Adam na duniya, ya gadar da zunubi. Kiristi, wanda ya cika wannan abin koyi kuma yake shugaban ruhaniya, ya ba kowa rai da kuɓuta daga laifi. Sakamakon biyayyar Kiristi ya fi sakamakon rashin biyayyar Adamu girma. Ta wurin laifi ɗaya Adamu ya kawo saɓo da mutuwa cikin duniya. Ta wurin biyayyarsa Kiristi ya kawar da muguntar zunubi, ta wurin adalcin bangaskiya kuma ya mayar wa dukan ’yan Adam da kyautar rai da gafarar laifin mutum, na zunubi na asali da na zunubin da mutum yake aikatawa. Dokar ta shigo ne domin ta sa a san alhakin zunubi. Alheri da kyautar Allah sun yalwata domin su cece mu daga hukuncin Dokar. Kamar yadda zunubi ya yi mulki bisa kowa, ya sa dukan ’yan Adam ƙarƙashin mutuwar ruhu da ta jiki, haka kuma alherin Allah zai yi mulki, yana haifar da tsarkin da yake kaiwa ga rai na har abada.

Romawa 5:12–21

12 Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi.

13 Gama kafin a ba da doka, zunubi yana nan a duniya. Amma ba a lissafin zunubi inda babu doka. 14 Duk da haka, mutuwa ta yi mulki tun Adamu har yă zuwa Musa, ta yi mulki har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi ta wurin taka umarni kamar yadda Adamu ya yi ba. A wata hanya dai Adamu shi ne kwatancin wani mutumin nan mai zuwa.

15 Amma kyautan nan dabam take da laifin nan. Gama in mutane da yawa sun mutu saboda laifin mutum ɗayan nan, to, ai, alherin Allah da kuma kyautan nan mai zuwa ta wurin alherin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi, ya shafi mutane da yawa! 16 Kyautar Allah kuwa ba kamar sakamakon da ya bi zunubin mutum gudan nan ba ne, Hukuncin ya bi zunubin mutum gudan nan, ya kuma kawo hallaka, amma kyautar ta bi laifofin masu yawa ta kuma sa Allah ya gan mu a matsayin marasa laifi. 17 Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.

18 Saboda haka, kamar yadda sakamakon laifin mutum guda ya jawo hallaka ga dukan mutane, haka ma sakamakon aikin adalci guda ya sa Allah ya same mu marasa laifi, wannan kuwa kawo rai ga dukan mutane. 19 Gama kamar yadda ta wurin rashin biyayyar mutum guda, mutane masu yawa suka zama masu zunubi, haka kuma ta wurin biyayyar mutum guda, mutane da yawa za su zama masu adalci.

20 An ba da dokar don mu ga yadda laifi yake da girma. Amma da zunubi ya ƙaru, sai alheri ya ƙaru sosai, 21 domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.