Baftisma Tana Wajabta wa Kiristoci Su Zama Masu Tsarki

Bayan ya nuna cewa ta wurin laifin Adamu guda ɗaya an yanke wa dukan mutane hukuncin mutuwa, Bulus ya tambaya ko zai dace a yi wa’azi, kamar yadda aka zarge su da yi (Romawa 3:6), cewa idan mutane suka ci gaba da zunubi, za a ƙara ba su alherin Allah na kyauta zuwa rai na har abada. Domin ya ƙaryata wannan kuskuren da ya yaɗu, ya tabbatar daga bikin baftisma cewa wajibi ne Kirista ya zama mai tsarki. Baftisma ta koya wa Kiristoci cewa, kamar yadda aka gicciye Kiristi kuma ya ba da jikinsa hadaya domin zunubi, haka waɗanda aka yi wa baftisma cikin sa su ɗauki jikinsu a matsayin wanda ya mutu ga zunubi kuma aka binne shi tare da shi, aka kuma tashe shi tare da shi zuwa sabuwar rayuwa ta wurin wannan Ruhu mai ba da rai wanda ya ta da mataccen jikin Kiristi daga kabari. Da yake an kashe tsohon mutum, wato halin mutum na ɗabi’a, tare da Kiristi, an rushe ikon zunubi, an kuma ’yantar da mutum daga mulkinsa. Waɗanda suka mutu ga zunubi tare da Kiristi za su rayu tare da shi domin Allah har abada. An ƙarfafa Romawa su yi la’akari da waɗannan abubuwa.

58 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Romawa 6:1–11

1 Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba da yin zunubi domin alheri yă haɓaka? 2 Sam, ko kaɗan! Mun mutu ga zunubi; ta yaya za mu ci gaba da rayuwa a cikinsa kuma? 3 Ko ba ku sani ba cewa dukanmu da aka yi wa baftisma a cikin Kiristi Yesu an yi mana baftismar ne zuwa cikin mutuwarsa? 4 Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.

5 In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu. 6 Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi 7 domin duk wanda ya mutu an ’yantar da shi daga zunubi ke nan.

8 To, in mun mutu tare da Kiristi, mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma. 9 Gama mun san cewa da yake an tā da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa. 10 Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda yă shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah.

11 Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.

Kada Ku Bar Zunubi Ya Sake Yin Mulki

Yanzu da mutuwar Kiristi ta fanshe su daga mulkin zunubi, Bulus ya ƙarfafa Romawa kada su bar zunubi ya sake yin mulki bisa jikinsu mai mutuwa, sai dai su mallaki jikinsu. Ya kira su su yi tsayayya da ƙarfin zunubi mai jarabtarwa, su kuma miƙa ruhohinsu da jikinsu ga hidimar adalci domin Allah. Domin ba sa ƙarƙashin Dokar kuma, wadda take neman biyayya marar zunubi ba tare da jinƙai ba, amma an kawo su ƙarƙashin bishara, wadda take ba da gafara da alheri.

Romawa 6:12–14

12 Saboda haka kada ku bar zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa yă sa ku zama masu biyayya ga mugayen sha’awace-sha’awacensa. 13 Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci. 14 Gama zunubi ba zai zama maigidanku ba, domin ba kwa ƙarƙashin doka, sai dai ƙarƙashin alheri.

Alheri Ba Ya Ba da Izinin Yin Zunubi

Sai Bulus ya tambaya ko daidai ne a ɗauka, kamar yadda waɗansu suka yi, cewa zunubi zai iya yawaita domin an ’yantar da Yahudawa daga Dokar (wadda take neman cikakkiyar biyayya, ba tare da tanadin gafara ba), aka kawo su cikin tsarin jinƙai. Akasin haka, ya tabbatar cewa a ƙarƙashin kowane tsari, waɗanda suke ci gaba da zunubi bayin zunubi ne, kuma suna ƙarƙashin mutuwa ta har abada. Waɗanda suke biyayya ga bangaskiyar bishara kaɗai ne suke samun ladar adalci, wato kyautar rai na har abada. Ya yi farin ciki cewa Romawa, waɗanda a dā suke bayin zunubi, yanzu sun yi biyayya ga tsarin koyarwar da aka ba su a baftisma, wadda ta ’yantar da su daga bautar zunubi, suka kuma zama bayin adalci.

Romawa 6:15–18

15 Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan! 16 Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan? 17 Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. 18 An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.

Bulus Ya Kwatanta Mulkin Zunubi da Bautar Romawa

Sa’ad da yake yin bayani ga Romawa, Bulus ya yi amfani da kwatance daga al’adunsu (domin sun san dokokin bauta), don su fi fahimtar zaluncin da zunubi ya yi wa jikinsu. Yanzu da suka kuɓuta daga zunubi, kamar yadda a dā suka kasance ba su da alaƙa da adalci, ya ƙarfafa su su miƙa gaɓoɓin jikinsu ga hidimar adalci, wadda ƙarshenta rai ne na har abada, maimakon hidimar zunubi da suka yi amfani da su a dā, wadda ƙarshenta mutuwa ce.

Romawa 6:19–23

19 Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki. 20 Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci. 21 Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne! 22 Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne. 23 Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Doka Takan Ƙare da Mutuwa Kamar Aure

Domin ya ƙara tabbatar wa Yahudawa cewa Dokar ba ta iya kuɓutar da mutum daga laifi, Bulus ya tabbatar cewa Dokar Musa, kamar dokar aure, takan warware idan ɗaya daga cikin ɓangarorin biyu ya mutu. Tun da an kashe su ta wurin Dokar a cikin jikin Kiristi, sun sami ’yancin auren wani miji, wato wanda, ko da yake an kashe shi, aka tashe shi daga matattu, domin tare da shi su rayu domin Allah. Ya bayyana cewa kafin su mutu tare da Kiristi a jiki, mugayen sha’awoyinsu, waɗanda Dokar ta bayyana, sun sa su ƙarƙashin mutuwa. Amma yanzu an ’yantar da su daga ikon Dokar, da yake tare da Kiristi sun rabu da jikin zunubi na ɗabi’ar jiki wanda ya riƙe su ƙarƙashin la’anarta, domin su bauta wa Allah cikin biyayyar ruhaniya ta bishara, ba cikin tsofaffin bukukuwa da rubutacciyar Dokar ba.

Romawa 7:1–6

1 Ba ku sani ba, ’yan’uwa, ina magana ne fa da mutanen da suka san doka, cewa dokar tana da iko a kan mutum muddin yana a raye ne kawai. 2 Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure. 3 Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.

4 Saboda haka ’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah. 5 Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa. 6 Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.

Dokar Ba Ita Ce Sanadin Zunubi Ba

A nan Bulus ya yi tunanin wani Bayahude yana tambaya ko Dokar ce sanadin zunubi. Ya amsa cewa ba za ta iya zama sanadin zunubi ba, domin ta hana zunubi. Muguwar sha’awar tana cikin mutum ne, Dokar kuwa ta bayyana ta kawai. Domin kada ya ɓata rai, Bulus ya yi amfani da kansa wajen bayyana yanayin Bayahuden da ba a sake haifa ba a ƙarƙashin Dokar. Ya nuna cewa Dokar ta bayyana abin da yake mugu kuma ta hana shi, wannan kuma ya zuga halin zunubi na mutum ƙwarai ya ƙi biyayya ya kuma yi tawaye ga umarnanta. Saboda haka Dokar da umarnin, tun da sun hana zunubi, masu tsarki ne, masu adalci kuma masu kyau. Duk da haka, kamar yadda Bulus ya nuna a kaikaice, suna kaiwa ga hukunci, ba ceto ba.

Romawa 7:7–12

7 Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.” 8 Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne. 9 Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu. 10 Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce.

11 Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni. 12 Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau.

Halaye Biyu Suna Yaƙi da Juna a Ƙarƙashin Dokar

Yanzu an yi tunanin Bayahuden yana tambaya ko Dokar, wadda take da kyau da tsarki haka, ita ce sanadin mutuwarsu. Bulus ya amsa cewa ba Dokar ba ce take jawo mutuwa, zunubi ne, kuma ana ganin tsananin muguntar zunubi sa’ad da ya sa masu zunubi ƙarƙashin mutuwa ta wurin dokar da take mai tsarki, mai adalci kuma mai kyau. Ya tabbatar cewa Dokar kanta tana inganta rayuwar ruhaniya. Amma domin ya nuna cewa, idan babu taimakon da ya fi ƙarfin ɗan Adam, ba ta da ikon sa kowa ya zama mai tsarki, ya ci gaba da amfani da kansa wajen kwatanta Bayahuden da ba a sake haifa ba a ƙarƙashin Dokar a matsayin wanda aka sayar wa zunubi ya zama bawansa, wato wanda ba shi da ikon kuɓuta daga hidimarsa. Ya bayyana ƙa’idoji biyu masu gāba da juna cikin halin ɗan Adam, waɗanda kullum suke yaƙi da juna. A ƙarƙashin Dokar, halin jiki yakan rinjayi mutumin ciki, wato halin ruhaniya. Dokar Musa tana sa mutum ya san wajibinsa ba tare da ba shi ikon aikata shi ba, sai a sa shi ƙarƙashin dokar zunubi da mutuwa. A cikin wannan mummunan yanayi Bulus ya yi kuka ya ce, “Wa zai cece ni daga wannan jikin mutuwa?”, wato jikin da aka sayar wa zunubi kuma ya zama mallakinsa. Ya bayyana da farin ciki cewa hanya guda tak ta ceto ita ce alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

Romawa 7:13–25

13 Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.

14 Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. 15 Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. 16 In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. 17 Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. 18 Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. 19 Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi. 20 To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.

21 Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22 Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23 amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24 Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25 Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu!

Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.