Gargaɗe-gargaɗe Cewa Zaman Talala Tabbatacce Ne (continued)

Annabce-annabce da kiraye-kiraye iri-iri ga Yahudawa, suna bayyana cewa lallai za a kai su zaman bauta, a kuma hallaka Urushalima.

609 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Irmiya 18–19

1 Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji. 2 “Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.” 3 Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen. 4 Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.

5 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 6 “Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila. 7 A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki, 8 in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata. 9 In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta, 10 in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.

11 “Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’ 12 Amma za su amsa su ce, ‘Ba amfani. Za mu ci gaba da shirye-shiryenmu; kowannenmu zai bi taurin muguwar zuciyarsa.’ ”

13 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Ku tattambaya a cikin al’ummai.

Wa ya taɓa jin irin wannan abu?

Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu

mafi banƙyama.

14 Dusar ƙanƙarar Lebanon

ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon?

Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa

sun taɓa daina gudu?

15 Duk da haka mutanena sun manta da ni;

sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani,

waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu

a hanyoyin dā.

Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi

a hanyoyin da ba a gina ba.

16 Ƙasarsu za tă zama kufai,

abin reni har abada;

dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki

su kaɗa kai.

17 Kamar iska daga gabas

zan warwatsa su a gaban abokan gābansu;

zan juya musu bayana, ba zan nuna musu fuskata ba

a ranar masifarsu.”

18 Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.”

19 Ka saurare ni, ya Ubangiji

ka ji abin da masu zargina suke cewa!

20 Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta?

Duk da haka sun haƙa mini rami.

Ka tuna cewa na tsaya a gabanka

na kuma yi magana a madadinsu

don ka janye fushinka daga gare su.

21 Saboda haka ka kawo wa ’ya’yansu yunwa;

ka miƙa su ga ikon takobi.

Bari matansu su zama marasa ’ya’ya da gwauraye;

bari a kashe mazansu,

a kuma kashe samarinsu da takobi a yaƙi.

22 Bari a ji kuka daga gidajensu

sa’ad da ka kawo masu hari a kansu farat ɗaya,

gama sun haƙa rami don su kama ni

suka kuma kafa tarko wa ƙafafuna.

23 Amma Ya Ubangiji,

ka san duk maƙarƙashiyarsu, na neman su kashe ni.

Kada ka gafarta musu laifofinsu

ko ka shafe zunubansu daga gabanka.

Bari a tumɓuke su a gabanka;

ka yi da su sa’ad da kake fushi.

19:1 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tafi ka sayo tulu a wurin mai ginin tukwane. Ka ɗauki waɗansu dattawan jama’a da kuma na firistoci 2 ku fita zuwa Kwarin Ben Hinnom, kusa da mashigin Ƙofar Kasko. A can ka furta maganganun da na faɗa maka, 3 ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya sarakunan Yahuda da kuma mutanen Urushalima. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku saurara! Zan kawo masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa. 4 Gama sun yashe ni suka kuma mai da wannan wuri ya zama na baƙin alloli; sun ƙone hadayu a cikinsa wa allolin da ko su ko kakanninsu ko sarakunan Yahuda ba su taɓa sani ba, suka kuma cika wannan wuri da jini marasa laifi. 5 Suka gina masujadai na kan tudu na Ba’al don su ƙona ’ya’yansu maza a cikin wuta a matsayin hadaya ga Ba’al abin da ban umarta ba, ban ambata ba, bai kuma zo mini ba. 6 Saboda haka ku lura, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara ce da wannan wuri Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma za su ce da shi Kwarin Kisa.

7 “ ‘A wannan wuri zan lalace dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji. 8 Zan ragargazar da wannan birni in mai da shi abin reni, duk wanda ya wuce zai yi mamaki ya kuma yi tsaki saboda dukan masifunsa. 9 Zan sa su ci naman ’ya’yansu maza da mata, za su kuma ci naman juna a lokacin damuwar ƙawanya da abokan gāban da suke neman ransu za su yi musu.’

10 “Sa’an nan ka fasa tulun yayinda waɗanda suka tafi tare da kai suna duba, 11 ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri. 12 Ga abin da zan yi wa wannan wuri da waɗanda suke zaune a nan, in ji Ubangiji. Zan mai da wannan birni kamar Tofet. 13 Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ”

14 Sa’an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don yă yi annabci, ya tsaya a filin haikalin Ubangiji ya ce wa mutane duka, 15 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa wannan birni da ƙauyukan da suke kewayensa kowace masifar da na furta a kansu, domin sun yi taurinkai, ba su kuwa saurari maganata ba.’ ”