An Annabta Makomar Fashhur
609 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Da firist nan Fashhur ɗan Immer, babban ma’aikaci a cikin haikalin Ubangiji, ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan abubuwa, 2 sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji. 3 Kashegari, sa’ad da Fashhur ya fitar da shi daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashhur ba, amma ya ba ka suna Magor-Missabib. 4 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi. 5 Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon. 6 Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”
7 Ya Ubangiji, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu;
ka fi ni ƙarfi, ka kuwa yi nasara.
Na zama abin dariya dukan yini;
kowa yana yi mini ba’a.
8 Duk sa’ad da na yi magana, nakan tā da murya
ina furta hargitsi da hallaka.
Haka maganar Ubangiji ta kawo mini
zagi da reni dukan yini.
9 Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba
ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,”
sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta,
wutar da aka kulle a ƙasusuwana.
Na gaji da danne ta a cikina;
tabbatacce ba zan iya ba.
10 Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa,
“Razana ta kowace fuska!
Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!”
Dukan abokaina
suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa,
“Mai yiwuwa a ruɗe shi;
sai mu yi nasara a kansa
mu ɗau fansa a kansa.”
11 Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi;
saboda haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe ba kuwa za su yi nasara ba.
Za su fāɗi su kuma sha mummunar kunya;
ba za a taɓa manta da rashin bangirmansu ba.
12 Ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake gwada adali
kana bincika zuciya duk da tunani,
bari in ga sakayyarka a kansu,
gama a gare ka na miƙa damuwata.
13 Ku rera ga Ubangiji!
Ku yabi Ubangiji!
Ya kuɓutar da ran mabukaci
daga hannuwan mugaye.
14 La’ananniya ce ranar da aka haife ni!
Kada ranar da mahaifiyata ta haife ni ta zama mai albarka!
15 La’ananne ne mutumin da ya kawo wa mahaifina labari,
wanda ya sa shi ya yi murna cewa, “An haifa maka yaro, ɗa namiji!”
16 Bari mutumin ya zama kamar garuruwan
da Ubangiji ya tumɓuke ba tausayi.
Bari yă ji kuka da safe
kururuwan yaƙi kuma da tsakar rana.
17 Gama bai kashe ni a cikin ciki ba,
da ma ya sa cikin mahaifiyata ya zama kabarina,
cikinta ya fadada har abada.
18 Me ya sa na ma fito daga cikin ciki
in ga wahala da baƙin ciki
in kuma ƙare kwanakina da kunya?
An Annabta Makomar Shallum da Yehohiyakim
1 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce, 2 ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi. 3 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri. 4 Gama in ka lura da bin waɗannan umarnai, to, sarakunan da suke zaune a gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan fada, suna hawan kekunan yaƙi da dawakai, fadawansu da mutanensu suna musu rakiya. 5 Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’ ”
6 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da wannan fadar sarkin Yahuda,
“Ko da yake kina kamar Gileyad a gare ni,
kamar ƙwanƙolin Lebanon,
tabbatacce zan maishe ki hamada,
kamar garuruwan da ba mazauna.
7 Zan aika da mai hallakarwa a kanki,
kowane mutum da makamansa,
za su kuma yayyanka gumaguman al’ul na ki masu kyau
su jefa su cikin wuta.
8 “Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’ 9 Amsar kuwa za tă zama, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada suka kuma bauta wa waɗansu alloli.’ ”
10 Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa;
a maimako, ku yi kuka mai zafi saboda wanda aka kai zaman bauta,
domin ba zai ƙara dawowa ba
ko ya ƙara ganin ƙasarsa ta haihuwa.
11 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shallum ɗan Yosiya, wanda ya gāji mahaifinsa a matsayin sarkin Yahuda amma bai bar wurin nan ba, “Ba zai ƙara dawowa ba. 12 Zai mutu a inda suka kai shi zaman bauta; ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.”
13 “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci,
ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya,
yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza
ba ya biyansu wahalarsu.
14 Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada
da manyan ɗakuna.’
Ta haka sai ya yi musu manyan tagogi
ya manne musu al’ul
ya yi musu ado kuma da ruwan ja.
15 “Wannan zai mai da kai sarki ne
in kana da al’ul a kai a kai?
Mahaifinka bai kasance da abinci da abin sha ba?
Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai
saboda haka kome ya kasance da lafiya da shi.
16 Ya kāre muradin matalauta da mabukata,
ta haka kome ya tafi masa daidai.
Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?”
In ji Ubangiji.
17 “Amma idanunka da zuciyarka
sun kahu kawai a kan ƙazamar riba,
da a kan zub da jinin marar laifi
da kuma a kan danniya da zalunci.”
18 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda,
“Ba za su yi kuka dominsa ba,
‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’
Ba za su yi kuka dominsa ba,
‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’
19 Za a binne shi kamar jaki
za a ja shi a ƙasa a jefar
a bayan ƙofofin Urushalima.”
20 “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka,
bari a ji muryarka a Bashan,
yi kuka daga Abarim,
gama an murƙushe dukan abokanka.
21 Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya,
amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’
Wannan halinka ne tun kana matashi;
ba ka yi mini biyayya ba.
22 Iska za tă koro dukan makiyayanka
abokanka kuma za su tafi zaman bauta.
Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka
saboda dukan muguntarka.
23 Kai da kake zama a ‘Lebanon,’
kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul
za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka,
zafi kamar na mace mai naƙuda!