Gargaɗe-gargaɗe Cewa Zaman Talala Tabbatacce Ne (continued)

Annabce-annabce da kiraye-kiraye iri-iri ga Yahudawa, suna bayyana cewa lallai za a kai su zaman bauta, a kuma hallaka Urushalima.

609 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Irmiya 16–17

1 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Kada ka yi aure ka haifi ’ya’ya maza da mata a wannan wuri.” 3 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da ’ya’ya maza da matan da aka haifa a wannan ƙasa da kuma game da matan da suke iyayensu da suke mazan da iyayensu. 4 “Za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi kuka dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba, amma za a bar su a juji. Takobi da yunwa ne za su hallaka su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji na duniya.”

5 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ka shiga gidan da akwai abincin makoki; kada ka tafi ka yi makoki ko ka nuna juyayi, domin na janye albarkata, ƙaunata da tausayina daga wannan mutane,” in ji Ubangiji. 6 “Manya da ƙanana duka za su mutu a wannan ƙasa. Ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi makokinsu ba, kuma ba wanda zai tsaga kansa ko ya aske kansa saboda su. 7 Ba wanda zai ba da abinci don yă ta’azantar da waɗanda suke makoki saboda matattu, kai, ko saboda mahaifi ko mahaifiya ma ba kuwa wani da zai ba da abin sha don yă ta’azantar da su.

8 “Kada kuma ka shiga gidan da ake biki ka zauna don ci da sha. 9 Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa a idanunka da kuma a kwanakinka zan kawo ƙarshen muryar farin ciki da murna da kuma muryoyin amarya da ango a wannan wuri.

10 “Sa’ad da ka faɗa wa waɗannan mutane wannan duka suka kuma tambaye ka, ‘Me ya sa Ubangiji ya ƙaddara irin wannan babban masifa a kanmu? Wace mugunta muka yi? Wane zunubi muka aikata wa Ubangiji Allahnmu?’ 11 Sai ka ce musu, ‘Wannan ya zama haka domin kakanninku sun rabu da ni,’ in ji Ubangiji, ‘suka bi waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Suka rabu da ni, ba su kuwa kiyaye dokata ba. 12 Amma kun yi laifi fiye da kakanninku. Duba yadda kowannenku yana bin taurin muguwar zuciyarsa a maimakon yin mini biyayya. 13 Saboda haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasar da ku da kakanninku ba ku taɓa sani ba, a can kuwa za ku bauta wa waɗansu alloli dare da rana, gama ba zan nuna muku tagomashi ba.’

14 “Amma fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga Masar,’ 15 amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su.’ Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba wa kakanninsu.

16 “Amma yanzu zan aiko a kira masunta masu yawa su zo,” in ji Ubangiji, “za su kuma kama su. Bayan wannan zan aiko a kira mafarauta su zo, su farauce su daga kowane dutse da tudu da kuma daga kogwannin duwatsu. 17 Idanuna suna a kan dukan hanyoyinsu; ba a ɓoye suke daga gare ni, kuma zunubansu ba a ɓoye suke a idanuna ba. 18 Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, suka kuma cika abin gādona da gumakansu na banƙyama.”

19 Ya Ubangiji, ƙarfina da katangana,

mafakata a lokacin damuwa,

gare ka al’ummai za su zo

daga iyakokin duniya su ce,

“Kakanninmu ba su mallaki kome ba sai allolin ƙarya,

gumakan banza da ba su yi musu amfani ba.

20 Mutane kan yi allolinsu ne?

I, amma waɗannan ba alloli ba ne!”

21 “Saboda haka zan koya musu

a wannan lokaci zan koya musu

ikona da ƙarfina.

Sa’an nan za su sani

cewa sunana Ubangiji ne.

17:1 “An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe,

an rubuta da tsinin dutse,

a kan allunan zukatansu

da kuma a kan ƙahonin bagadansu.

2 Har ’ya’yansu ma sun tuna

bagadansu da ginshiƙan Asheransu

kusa da itatuwa masu duhuwa

da kuma a kan tuddai masu tsayi.

3 Dutsena a ƙasar

da dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku

za a ba da su ganima,

tare da masujadanku na kan tuddai,

saboda zunubi ko’ina a ƙasarku.

4 Saboda laifinku za ku rasa

gādon da na ba ku.

Zan bautar da ku ga abokan gābanku

a ƙasar da ba ku sani ba,

domin kun husata ni,

zai kuwa ci har abada.”

5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,

wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi

wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.

6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;

ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.

Za su zauna a busassun wuraren hamada,

a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.

7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

ganyayensa kullum kore suke.

Ba shi da damuwa a shekarar fări

ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

9 Zuciya ta fi kome ruɗu

ta fi ƙarfin warkewa.

Wa zai iya gane ta?

10 “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya

in gwada tunani,

don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa,

bisa ga ayyukansa.”

11 Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba

haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba.

A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi,

a ƙarshe kuma zai zama wawa.

12 Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko,

shi ne wuri mai tsarkinmu.

13 Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila,

duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya.

Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura

domin sun yashe Ubangiji,

maɓulɓular ruwan rai.

14 Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;

ka cece ni zan kuwa cetu,

gama kai ne nake yabo.

15 Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take?

Bari tă cika yanzu!”

16 Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba;

ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba.

Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka.

17 Kada ka zama mini abin razana;

kai ne mafakata a ranar masifa.

18 Bari masu tsananta mini su sha kunya,

amma ka kiyaye ni daga shan kunya;

bari su tsorata,

amma ka kiyaye ni da razana.

Ka kawo musu ranar masifa;

ka hallaka su da hallaka riɓi biyu.

19 Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima. 20 Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi. 21 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima. 22 Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku. 23 Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba. 24 Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba, 25 sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada. 26 Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji. 27 Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ”