Gargaɗe-gargaɗe Cewa Zaman Talala Tabbatacce Ne (continued)
Annabce-annabce da kiraye-kiraye iri-iri ga Yahudawa, suna bayyana cewa lallai za a kai su zaman bauta, a kuma hallaka Urushalima.
609 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa,
2 “Yahuda tana makoki
biranenta suna fama;
suna kuka saboda ƙasar,
kuka kuma tana tasowa daga Urushalima.
3 Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa
a maɓulɓulai amma babu ruwa.
Suka dawo da tulunansu haka nan;
da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe.
4 Ƙasa ta tsattsage
saboda babu ruwan sama a ƙasar;
manoma sun sha kunya
suka kuma rufe kawunansu.
5 Har barewa a kurmi ma
ta gudu ta bar ’ya’yan da ta haihu sababbi
saboda babu ciyawa.
6 Jakan jeji suna tsaye a kan tuddai
suna haki kamar diloli;
idanunsu sun kāsa gani
saboda rashin makiyaya.”
7 Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu,
Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka.
Gama jan bayanmu ya yi yawa;
mun yi maka zunubi.
8 Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila,
Mai Cetonsa a lokutan wahala,
me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar,
kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce?
9 Me ya sa kake yi kamar mutumin da aka far masa kwasam ba zato,
kamar jarumi marar ƙarfin ceto?
Kana a cikinmu, ya Ubangiji,
da sunanka ake kiranmu;
kada ka yashe mu!
10 Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane,
“Suna son yawace-yawace ƙwarai;
ba sa hana ƙafafunsu yawo.
Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba;
yanzu zai tuna da muguntarsu
zai kuma hukunta su saboda zunubansu.”
11 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin zaman lafiyar mutanen nan. 12 Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.”
13 Amma na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, annabawa sun riƙa ce musu, ‘Ba za ku ga takobi ko ku yi fama da yunwa ba. A maimako, zan ba ku madawwamiyar salama.’ ”
14 Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne. 15 Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su. 16 Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko ’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su.
17 “Ka yi musu wannan magana,
“ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye
dare da rana kada su daina;
saboda ’yata budurwa, mutanena,
sun sha wahalar babban rauni,
an yi musu bugu mai ragargazawa.
18 In na shiga cikin ƙasar,
na ga waɗanda takobi ya kashe;
in na shiga cikin birni,
na ga waɗanda suke fama da yunwa.
Da Annabi da firist duk
sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’ ”
19 Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan?
Kana ƙyamar Sihiyona ne?
Me ya sa ka buge mu
don kada mu warke?
Mun sa zuciya ga salama
babu abin alherin da ya zo,
mun sa rai ga lokacin warkarwa
amma sai ga razana.
20 Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu
da kuma laifin kakanninmu;
tabbatacce mun yi maka zunubi.
21 Saboda sunanka kada ka ƙi mu;
kada ka ƙasƙantar da kursiyoyinka mai ɗaukaka.
Ka tuna da alkawarinka da mu
kada ka tā da shi.
22 Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama?
Sararin sama kansu sukan yi yayyafi?
A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu.
Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka,
gama kai ne kake yi wannan duka.
15:1 Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi! 2 In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“ ‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su;
waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su;
waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su;
waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’
3 “Zan aika musu da iri masu hallakarwa guda huɗu,” in ji Ubangiji, “takobi zai kashe, karnuka za su kwashe, tsuntsaye da namun jeji kuma su cinye su kuma hallaka. 4 Zan sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manasse ɗan Hezekiya sarkin Yahuda ya aikata a Urushalima.
5 “Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima?
Wa zai yi makoki dominki?
Wa zai dakata ya tambayi lafiyarki?
6 Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji.
“Ki ci gaba da ja da baya.
Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki;
ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba.
7 Zan sheƙe ki da abin sheƙewa
a ƙofofin birnin ƙasar.
Zan kawo baƙin ciki da hallaka a kan mutanena,
gama ba su canja hanyoyinsu ba.
8 Zan ƙara yawan gwaurayensu
su fi yashin teku yawa.
Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa
a kan iyaye mata na samarinsu;
farat ɗaya zan kawo musu
wahala da razana.
9 Mahaifiya ’ya’ya bakwai za tă suma
ta ja numfashinta na ƙarshe.
Ranarta zai fāɗi tun lokacin bai yi ba;
za tă sha kunya a kuma wulaƙanta ta.
Zan sa a kashe raguwa da takobi
a gaban abokan gābansu,”
in ji Ubangiji.
10 Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni,
mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi!
Ban ba da bashi ko in ci bashi ba,
duk da haka kowa yana zagina.
11 Ubangiji ya ce,
“Tabbatacce zan cece ka don alheri;
tabbatacce zan sa abokan gābanka su yi roƙo gare ka
a lokacin masifa da kuma lokacin wahala.
12 “Mutum zai iya karye ƙarfe
ƙarfe daga arewa, ko tagulla?
13 “Dukiyarku da arzikinku
zan ba da su ganima, babu tara,
saboda duka zunubanku
ko’ina a ƙasar.
14 Zan bautar da ku ga abokan gābanku
a ƙasar da ba ku sani ba,
gama fushina zai yi ƙuna kamar wuta
da za tă yi ƙuna a kanku.”
15 Ka gane, ya Ubangiji;
ka tuna da ni ka kuma lura da ni.
Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini.
Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni;
ka tuna yadda na sha zagi saboda kai.
16 Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su;
suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna,
gama ana kirana da sunanka,
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.
17 Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba,
ban taɓa yi murna da su ba;
na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina
ka kuma sa na cika da haushi.
18 Me ya sa wahalata ba ta ƙarewa
mikina kuma ba ya warkuwa?
Za ka zama mini kamar rafi mai yaudara ne,
kamar maɓulɓulan da ta kafe ne?
19 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa,
“In ka tuba, zan maido da kai
don ka bauta mini;
in ka ambaci maganganu masu kyau, ba marasa kyau ba,
za ka zama kakakina.
Bari wannan mutane su juyo gare ka,
amma kada ka juye gare su.
20 Zan mai da kai katanga ga wannan mutane,
katanga mai ƙarfi na tagulla;
za su yi yaƙi da kai
amma ba za su yi nasara a kanka ba,
gama ina tare da kai
don in kuɓutar in kuma cece ka,”
in ji Ubangiji.
21 “Zan cece ka daga hannuwan mugaye
in ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.”