Yaƙi da Al’ummomin da Ke Kewaye

1040 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Sama’ila 8:1–12

1 Ana nan, sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar, ya kuma ƙwace ƙasar Meteg Amma daga hannun Filistiyawa.

2 Haka kuma Dawuda ya ci Mowabawa. Ya sa suka kwanta a ƙasa, ya kuma auna su da igiya. Kowane awo biyu ya sa a kashe su, amma awo na uku sai yă sa a bar su da rai. Saboda haka Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka kuma kawo masa haraji.

3 Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba. Wannan ya faru a lokacin da Hadadezer yake kan hanyarsa zuwa Kogin Yuferites don yă sāke mai da wurin a ƙarƙashin ikonsa. 4 Dawuda ya kame keken yaƙinsa guda dubu, mahayan keken yaƙinsa dubu bakwai, da sojojin ƙasa dubu ashirin. Ya yayyanke agaran dawakan duka amma ya bar dawakai kekunan yaƙi ɗari.

5 Sa’ad da Arameyawan Damaskus suka zo don su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe dubu ashirin da biyunsu. 6 Ya ajiye ƙungiyoyi sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus, Arameyawa kuwa suka zama bayinsa, suka biya shi haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a duk inda ya tafi.

7 Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariya na shugabannin sojojin Hadadezer ya kawo Urushalima. 8 Daga Teba da Berotai, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Sarki Dawuda ya kwashe tagulla masu yawan gaske.

9 Da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer, 10 sai ya aiki ɗansa Yoram wurin Sarki Dawuda yă gaishe, yă kuma yi masa barka saboda nasarar da ya yi a kan Hadadezer, gama Hadadezer nan ya hana Towu sakewa. Yoram ya tafi ɗauke da kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.

11 Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan kayayyaki wa Ubangiji, yadda ya yi da zinariya, da kuma azurfa daga dukan al’umman da ya mallaka, 12 wato, azurfa da zinariyan mutanen Edom, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba.

1 Tarihi 18:12

12 Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.

2 Sama’ila 8:14–18

14 Ya ajiye rundunar sojoji ko’ina a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba wa Dawuda nasara a duk inda ya tafi.

15 Dawuda ya yi mulkin dukan ƙasar Isra’ila, yana yin wa dukan jama’arsa shari’ar gaskiya da adalci. 16 Yowab ɗan Zeruhiya ya zama shugaban sojoji; Yehoshafat ɗan Ahilud kuwa shi ne marubucin tarihi; 17 Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyatar, su ne firistoci; Serahiya kuma sakatare; 18 Benahiya ɗan Yehohiyada ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, wato, sojoji masu gadin Dawuda, sa’an nan ’ya’yan Dawuda maza su ne mashawartan sarki.

2 Sama’ila 8:13

13 Dawuda kuwa ya ƙara zama shahararre bayan ya dawo daga kai wa ƙasar Aram hari, daga nan sai ya je ya karkashe mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.

Hadad Ya Tsere

1 Sarakuna 11:15–20

15 A shekarun baya Dawuda ya ci Edom da yaƙi. Yowab, shugaban sojojinsa ya tafi can domin yă binne Isra’ilawa waɗanda suka mutu a yaƙi. Sa’ad da suke a can, sojojin Isra’ila suka kashe kowane ɗa namiji a Edom. 16 Yowab da dukan Isra’ilawa suka zauna a can, wata shida, sai da suka hallaka dukan mutane a Edom. 17 Amma Hadad yana ɗan yaro a lokaci, wanda ya gudu zuwa Masar tare da shugabannin mutanen Edom waɗanda suka yi wa mahaifinsa hidima. 18 Suka taso daga Midiyan suka tafi Faran. Sa’an nan suka ɗauki mutane daga Faran suka tafi Masar, zuwa wurin Fir’auna wanda ya ba wa Hadad gida da ƙasa, ya kuma tanada masa da abinci.

19 Fir’auna ya ji daɗin Hadad har ya ba shi ’yar’uwar matarsa, Sarauniya Tafenes, aure. 20 ’Yar’uwar Tafenes ta haifi masa ɗa wanda ya kira Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a fadan sarki. A can, Genubat ya yi zama da ’ya’yan Fir’auna.

Zabura 60

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri.

1 Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu;

ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!

2 Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta;

ka daure karayarta, gama tana rawa.

3 Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala;

ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.

4 Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta

don a buɗe gāba da baka. Sela

5 Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama,

domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.

6 Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki,

“Da nasara zan rarraba Shekem

in kuma auna Kwarin Sukkot.

7 Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne;

Efraim shi ne hular kwanona,

Yahuda kuma sandar mulkina.

8 Mowab shi ne kwanon wankina,

a kan Edom zan jefa takalmina;

a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”

9 Wa zai kawo ni birnin katanga?

Wa zai bishe ni zuwa Edom?

10 Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu

ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

11 Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba,

gama taimakon mutum banza ne.

12 Tare da Allah za mu yi nasara,

zai kuma tattake abokan gābanmu.