An Hana Dawuda Gina Haikali (continued)

1044 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 16

Miktam ne na Dawuda.

1 Ka kiyaye ni, ya Allah,

gama a cikinka nake samun mafaka.

2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana;

in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”

3 Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa,

su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.

4 Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli.

Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba

ko in ambaci sunayensu da bakina.

5 Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na;

ka kiyaye rabona,

6 Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi;

tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.

7 Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara;

ko da dare ma zuciyata kan koya mini.

8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;

jikina kuma zai zauna lafiya,

10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,

ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

11 Ka sanar da ni hanyar rai;

za ka cika ni da farin ciki a gabanka,

da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

Zabura 118

1 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;

ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

2 Bari Isra’ila yă ce,

“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

3 Bari gidan Haruna yă ce,

“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

4 Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce,

“Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

5 Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji,

ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.

6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.

Me mutum zai yi mini?

7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.

Zan yi nasara a kan abokan gābana.

8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

da in dogara ga mutum.

9 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

da in dogara ga sarakuna.

10 Dukan al’ummai sun kewaye ni,

amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.

11 Sun kewaye ni a kowane gefe,

amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.

12 Sun rufe ni kamar ƙudan zuma,

amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta;

a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.

13 An ture ni baya na kusa fāɗuwa,

amma Ubangiji ya taimake ni.

14 Ubangiji ne ƙarfina da waƙata;

ya zama mai cetona.

15 Sowa ta farin ciki da nasara

sun fito a cikin tentunan adalai,

“Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!

16 An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama;

hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!”

17 Ba zan mutu ba amma zan rayu,

zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi.

18 Ubangiji ya hore ni sosai,

amma bai ba da ni ga mutuwa ba.

19 Buɗe mini ƙofofin adalci;

zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji.

20 Wannan ne ƙofar Ubangiji

inda adalai za su shiga.

21 Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini;

ka zama mai cetona.

22 Zabura Dutsen da magina suka ƙi

ya zama mai amfani;

23 Ubangiji ne ya yi haka,

kuma abu mai daraja ne a idanunmu.

24 Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;

bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.

25 Ya Ubangiji, ka cece mu;

Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.

26 Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji.

Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.

27 Ubangiji shi ne Allah

ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu.

Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki

ku kai su ƙahoni na bagade.

28 Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya;

kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.

29 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;

ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

Zabura 110

Ta Dawuda. Zabura ce.

1 Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

“Zauna a hannun damana,

sai na sa abokan gābanka

su zama matashin sawunka.”

2 Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona

za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.

3 Rundunarka za su so yin yaƙi

a ranarka ta yaƙi.

Saye cikin ɗaukaka mai tsarki,

daga cikin ciki na safiya

za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.

4 Ubangiji ya rantse

ba zai kuma canja zuciyarsa ba,

“Kai firist ne har abada,

bisa ga tsarin Melkizedek.”

5 Ubangiji yana a hannun damanka;

zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.

6 Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki

yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.

7 Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya;

saboda haka zai ɗaga kansa sama.