An Hana Dawuda Gina Haikali (continued)
1044 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki
mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?
2 Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi
masu mulki sun taru gaba ɗaya
suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.
3 Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu,
mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”
4 Mai zama a kursiyi a sama yana dariya;
Ubangiji yana musu ba’a.
5 Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa
ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,
6 “Na kafa Sarkina a kan kursiyi
a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”
7 Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji.
Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne;
yau na zama Mahaifinka.
8 Ka tambaye ni
zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka,
iyakokin duniya su zama mallakarka.
9 Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe;
za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”
10 Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo;
ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya.
11 Ku bauta wa Ubangiji da tsoro
ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.
12 Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi
ku hallaka a abubuwan da kuke yi,
gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya.
Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Lili.” Na ’ya’yan Kora maza. Maskil Waƙar Aure.
1 Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana
yayinda nake rera ayoyina wa sarki;
harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci.
2 Kai ne mafi kyau cikin mutane
an kuma shafe leɓunanka da alheri,
da yake Allah ya albarkace ka har abada.
3 Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi;
ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja.
4 Cikin darajarka ka hau zuwa nasara
a madadin gaskiya, tawali’u da adalci;
bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki.
5 Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki;
bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka.
6 Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin;
sandar adalci zai zama sandar mulkinka.
7 Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta;
saboda haka Allah, Allahnka, ya sa ka a bisa abokanka
ta wurin shafe ka da man farin ciki.
8 Dukan rigunanka suna ƙanshin turaren mur da na aloyes, da na kashiya;
daga kowace fadan da aka yi masa ado da hauren giwa
kaɗe-kaɗen tsirkiya kan sa ka murna.
9 ’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama;
a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya.
10 Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne,
Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki.
11 Sarki ya cika da sha’awar kyanki;
ki girmama shi, gama shi ne maigidanki.
12 Diyar Taya za tă zo da kyauta,
mawadata za su nemi tagomashinki.
13 Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun;
an saƙa rigarta da zaren zinariya.
14 Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki;
abokanta budurwai suna biye da ita
aka kuwa kawo su gare ka.
15 Aka bi da su cikin farin ciki da murna;
suka shiga fadan sarki.
16 ’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka;
za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar.
17 Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai;
saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda.
1 Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?
Me ya sa ka yi nisa da cetona,
ka yi nesa daga kalmomin nishina?
2 Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba,
da dare kuma ban yi shiru ba.
3 Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan;
kai ne yabon Isra’ila.
4 A gare ka ne kakanninmu suka sa bege;
sun dogara ka kuwa cece su.
5 Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto;
a gare ka suka dogara kuma ba su sha kunya ba.
6 Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba,
wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi.
7 Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a;
suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,
8 “Ya dogara ga Ubangiji;
bari Ubangiji yă cece shi.
Bari yă cece shi,
da yake yana jin daɗinsa.”
9 Duk da haka ka fitar da ni daga ciki;
ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata.
10 Daga haihuwa an jefa ni a kanka;
daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.
11 Kada ka yi nesa da ni,
gama wahala na kusa
kuma babu wani da zai taimaka.
12 Bijimai masu yawa sun kewaye ni;
bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.
13 Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama
sun buɗe bakunansu a kaina.
14 An zubar da ni kamar ruwa,
kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai.
Zuciyata ta zama kaki;
ta narke a cikina.
15 Ƙarfina ya bushe kamar kasko,
harshena kuma ya manne wa dasashina na sama;
ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.
16 Karnuka sun kewaye ni;
ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka,
sun soki hannuwana da ƙafafuna.
17 Zan iya ƙirga ƙasusuwana;
mutane suna farin ciki a kaina.
18 Sun raba rigunana a tsakaninsu
suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.
19 Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa;
Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.
20 Ka ceci raina daga takobi,
raina mai daraja daga ikon karnuka.
21 Ka cece ni daga bakin zakoki;
ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.
22 Zan furta sunanka ga ’yan’uwana;
cikin taron masu sujada zan yabe ka.
23 Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi!
Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi!
Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!
24 Gama bai rena ko yă ƙyale
wahalar masu shan wuya ba;
bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba
amma ya saurari kukansa na neman taimako.
25 Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro;
a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina.
26 Matalauta za su ci su ƙoshi;
su da suke neman Ubangiji za su yabe shi,
bari zukatanku su rayu har abada!
27 Dukan iyakokin duniya
za su tuna su kuma juya ga Ubangiji,
kuma dukan iyalan al’ummai
za su rusuna a gabansa,
28 gama mulki na Ubangiji ne
kuma yana mulki a bisa al’ummai.
29 Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada;
dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa,
waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba.
30 Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima;
za a faɗa wa zuriya na nan gaba game da Ubangiji.
31 Za su yi shelar adalcinsa
ga mutanen da ba a riga an haifa ba,
gama ya aikata shi.