Hadad Ya Tsere (continued)

1040 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 108

Waƙa ce. Zabura ta Dawuda.

1 Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah;

zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.

2 Ku farka, garaya da molo!

Zan farkar da rana.

3 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;

zan rera game da kai cikin mutane.

4 Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai;

amincinka ya kai sarari.

5 A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai,

bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.

6 Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama,

domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.

7 Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki,

“Ciki nasara zan raba Shekem

in kuma auna Kwarin Sukkot.

8 Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne;

Efraim shi hulan kwanona,

Yahuda ne sandana na sarauta.

9 Mowab shi ne kwanon wankina,

a kan Edom zan jefa takalmina;

a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”

10 Wa zai kawo ni birni mai katanga?

Wa zai jagorance ni zuwa Edom?

11 Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu

ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

12 Ka ba mu taimako a kan abokin gāba,

gama taimakon mutum banza ne.

13 Tare da Allah za mu yi nasara,

zai kuma tattaka abokan gābanmu.

1 Tarihi 18:1–11

1 Ana nan sai Dawuda ya ci Filistiyawa ya kuma rinjaye su, ya ƙwace Gat da ƙauyukan kewayenta daga mulkin Filistiyawa.

2 Dawuda ya kuma ci Mowabawa, suka zama bayinsa suka kuma biya haraji.

3 Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer sarkin Zoba, har can Hamat, sa’ad da ya je don yă kafa mulkinsa a wajen Kogin Yuferites. 4 Dawuda ya kame keken yaƙinsa dubu ɗaya, da mahayan kekunan yaƙi dubu bakwai da sojojin kafa guda dubu ashirin. Ya yayyanke dukan agaran dawakansa, amma ya bar dawakai da suka isa jan kekunan yaƙi ɗari.

5 Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu. 6 Ya sa ƙungiyoyin sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus. Arameyawan kuwa suka zama bayinsa, suka kuma kawo haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.

7 Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima. 8 Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam.

9 Sa’ad da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci mayaƙan Hadadezer sarkin Zoba gaba ɗaya, 10 sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla.

11 Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek.

1 Tarihi 18:13–17

13 Ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.

14 Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa.

15 Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa;

Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci;

16 Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci;

Shafsha shi ne magatakarda;

17 Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa;

’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.