Zuwa ga Sardis da Ikilisiyoyin da Kishinsu Yake Raguwa

Saƙo zuwa ga ikilisiyar Sardis, da dukan ikilisiyoyin da suke barin kishinsu da amincinsu su ragu.

96 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ru’uya ta Yohanna 3:1–6

1 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta,

Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake riƙe da ruhohi bakwai na Allah da kuma taurari bakwai.

Na san ayyukanka; ana ganinka kamar rayayye, amma kai matacce ne. 2 Ka farka! Ka ƙarfafa abin da ya rage wanda kuma yake bakin mutuwa, don ban ga ayyukanka cikakke ne ba a gaban Allahna. 3 Saboda haka, ka tuna fa, abin da ka karɓa ka kuma ji; ka yi biyayya da shi, ka kuma tuba. Amma in ba ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan zo maka ba.

4 Duk da haka kana da mutane kima cikin Sardis waɗanda ba su ɓata tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni, saye da fararen tufafi, don sun cancanta. 5 Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa. 6 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.

Zuwa ga Filadelfiya da Ikilisiyoyi Masu Aminci da Kishi

Saƙo zuwa ga ikilisiyar da take Filadelfiya, da dukan ikilisiyoyin da suke aiki da kishi da aminci, gwargwadon damar da suke da ita da ƙarfinsu.

Ru’uya ta Yohanna 3:7–13

7 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Filadelfiya, ka rubuta,

Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake mai tsarki da kuma gaskiya, wanda yake riƙe da mabuɗin Dawuda. Abin da ya buɗe ba mai rufewa, abin da kuma ya rufe ba mai buɗewa.

8 Na san ayyukanka. Duba, na sa a gabanka buɗaɗɗen ƙofa wadda ba mai iya rufewa. Na san cewa kana da ɗan ƙarfi, duk da haka ka kiyaye maganata ba ka kuwa yi mūsun sunana ba. 9 Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka. 10 Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya.

11 Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka. 12 Duk wanda ya ci nasara zan mai da shi ginshiƙi a haikalin Allahna. Ba kuwa zai sāke barin wurin ba. Zan rubuta a kansa sunan Allahna da kuma sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda take saukowa daga sama daga Allahna; ni kuma zan rubuta a kansa sabon sunana. 13 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.

Zuwa ga Lawodiseya da Ikilisiyoyi Masu Arziki, Masu Girman Kai, Masu Ɗumi-ɗumi

Saƙo zuwa ga ikilisiyar da take Lawodiseya, da dukan ikilisiyoyi masu arziki, masu girman kai, masu ɗumi-ɗumi.

Ru’uya ta Yohanna 3:14–22

14 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta,

Waɗannan su ne kalmomina Amin, amintaccen mashaidi mai gaskiya, da kuma mai mulkin halittar Allah.

15 Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi! 16 Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina. 17 Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara. 18 Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.

19 Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba. 20 Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.

21 Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa. 22 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”

Dukan Halitta Tana Bautar Yesu Kiristi

Ru’uyoyin Yohanna sun fara da hoton dukan halitta tana haɗa kai wajen bautar Yesu Kiristi, Allah na addinin Kirista.

Ru’uya ta Yohanna 4

1 Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.” 2 Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa. 3 Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin. 4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu. 5 Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah. 6 Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi.

A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya. 7 Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama. 8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,

“ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki

shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’

wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”

9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, 10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,

11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,

ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,

domin ka halicci dukan abubuwa,

kuma ta wurin nufinka aka halicce su

suka kuma kasance.”

Babu Mutumin da Zai Iya Buɗe Littafin Naɗaɗɗe Mai Hatimi

A cikin ru’uyarsa Yohanna ya ga littafin naɗaɗɗe mai hatimai bakwai, wanda ya ƙunshi tarihin ikilisiyar Allah na nan gaba, wanda babu wani ɗan Adam da ya iya buɗewa.

Ru’uya ta Yohanna 5:1–3

1 Sa’an nan na ga a hannun damar wannan wanda yake zaune a kursiyin naɗaɗɗen littafi da rubutu a ciki da wajensa an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. 2 Na kuma ga wani babban mala’ika yana shela da babbar murya cewa, “Wa ya cancanta yă ɓalle hatiman nan yă kuma buɗe naɗaɗɗen littafin?” 3 Amma ba wani a sama ko a ƙasa ko a ƙarƙashin ƙasan da ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin ko ma yă duba cikinsa.

Ɗan Rago Ya Buɗe Littafin Naɗaɗɗe

Ɗan Allah, wanda aka nuna a matsayin ɗan rago a lokacin da ake yanka shi hadaya, ya buɗe littafin naɗi don ya nuna wa ikkilisiya tarihin yadda kulawar Allah za ta mulke ta har zuwa ƙarshen zamani. Dukan halitta ta sāke miƙa yabo da girmamawa ga Ɗan Ragon Allah da aka yanka hadaya.

Ru’uya ta Yohanna 5:4–14

4 Na yi ta kuka domin ba a iya samun wanda ya cancanta yă buɗe naɗaɗɗen littafin ko yă duba cikinsa ba. 5 Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.”

6 Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya. 7 Ya zo ya karɓi naɗaɗɗen littafin daga hannun dama na wannan wanda yake zaune a kursiyin. 8 Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. 9 Suka rera sabuwar waƙa,

“Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin

ka kuma buɗe hatimansa,

domin an kashe ka,

da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,

daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.

10 Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,

kuma za su yi mulki a duniya.”

11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,

“Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,

don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi

da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”

13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,

“Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon

yabo da girma da ɗaukaka da iko,

sun tabbata har abada abadin!”

14 Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.