Yohanna Ya Rubuta Ru’uyar da Aka Yi Masa

Manzo Yohanna ya rubuta Ru’uyar da Aka Yi Masa (mai yiwuwa a shekara ta 96 bayan haihuwar Kiristi) domin ta maye gurbin annabawa masu ci gaba da maye gurbin juna a ikilisiyar Kirista har zuwa zuwan Kiristi na biyu domin ya yi wa duniya hukunci.

96 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

An Faɗa wa Kowa Ya Yi Nazarin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna

An umurci dukan ’yan Adam su yi nazarin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna.

Ru’uya ta Yohanna 1:1–3

1 Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna, 2 wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi. 3 Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa.

Yohanna Ya Gai da Ikilisiyoyi

Yohanna ya gai da ikilisiyoyi, ya kuma tabbatar da allahntakar Mai Cetonsu, wanda zai zo ya yi wa duniya hukunci.

Ru’uya ta Yohanna 1:4–8

4 Daga Yohanna,

Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya.

Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa, 5 da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya.

Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa, 6 ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin.

7 “Duba, yana zuwa cikin gizagizai,

kowane ido kuwa zai gan shi,

har da waɗanda suka soke shi”;

dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.”

Bari yă zama haka nan! Amin.

8 “Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.”

Kiristi Ya Bayyana ga Yohanna a Fatmos

Yohanna ya ba da labarin yadda Kiristi ya bayyana gare shi a tsibirin Fatmos, da kuma aikin da aka ba shi a matsayin annabi.

Ru’uya ta Yohanna 1:9–20

9 Ni, Yohanna, ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku cikin wahala da mulki, da kuma haƙurin jimrewa da suke namu cikin Yesu, ina can tsibirin Fatmos saboda maganar Allah da kuma saboda shaidar Yesu. 10 A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho, 11 wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.”

12 Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya. 13 A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa. 14 Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta. 15 Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu. 16 A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.

17 Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe. 18 Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.

19 “Saboda haka, ka rubuta abin da ka gani, abin da yake yanzu, da abin da zai faru nan gaba. 20 Asirin taurari bakwai da ka gani a hannuna na dama da kuma na alkukan fitilu bakwai na zinariya shi ne, Taurarin bakwai ɗin nan, mala’ikun ikkilisiyoyi bakwai ne; alkukan fitilu bakwai ɗin nan kuma ikkilisiyoyi bakwai ne.

Zuwa ga Afisa da Dukan Ikilisiyoyin da Suke Ja da Baya Daga Bangaskiya

Saƙo zuwa ga ikilisiyar da take Afisa, da dukan ikilisiyoyin da suka fara ja da baya daga bangaskiya.

Ru’uya ta Yohanna 2:1–7

1 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta,

Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya.

2 Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne. 3 Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.

4 Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko. 5 Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake. 6 Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi.

7 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.

Zuwa ga Simirna da Dukan Ikilisiyoyin da Ake Tsananta wa

Saƙo zuwa ga ikilisiyar Simirna, da dukan ikilisiyoyin da suke cikin tsanantawa da wahala.

Ru’uya ta Yohanna 2:8–11

8 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta,

Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.

9 Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne. 10 Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.

11 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.

Zuwa ga Fergamum da Ikilisiyoyin da Suke Barin Koyarwar Ɓata Ta Shigo

Saƙo zuwa ga ikilisiyar Fergamum, da dukan ikilisiyoyin da suka sassauta horonsu, har suka bar malaman koyarwar ɓata su shigo.

Ru’uya ta Yohanna 2:12–17

12 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Fergamum, ka rubuta,

Waɗannan su ne kalmomin wannan wanda yake da takobi mai kaifi biyu.

13 Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama.

14 Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci. 15 Haka ma kana da waɗanda suke riƙe da koyarwar Nikolaitawa. 16 Saboda haka ka tuba! In ba haka ba, zan zo wajenka ba da daɗewa ba in yaƙe su da takobin bakina.

17 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.

Zuwa ga Tiyatira da Ikilisiyoyin da Suke Ƙyale Lalata

Saƙo zuwa ga ikilisiyar da take Tiyatira, da dukan ikilisiyoyin da suke ci gaba da shaidar bangaskiya ta gaskiya kuma suke da yalwar ayyuka nagari ta hanyoyi da yawa, amma duk da haka suna ƙyale lalata da bautar gumaka su ci gaba a cikinsu.

Ru’uya ta Yohanna 2:18–29

18 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Tiyatira, ka rubuta,

Waɗannan su ne kalmomin Ɗan Allah, wanda idanunsa suna kama da harshen wuta wanda kuma ƙafafunsa suna kama da tagullar da aka goge.

19 Na san ayyukanka, ƙaunarka da bangaskiyarka, hidimarka da daurewarka, kuma cewa kana yin abubuwa a yanzu fiye da abin da ka yi da farko.

20 Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka. 21 Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya. 22 Don haka zan jefa ta a kan gadon wahala, zan kuma sa waɗanda suke zina da ita, su sha azaba ƙwarai, sai dai in sun tuba daga hanyoyinta. 23 Zan kashe ’ya’yanta. Sa’an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne mai bincika zukata da tunani, zan kuwa sāka wa kowannenku gwargwadon ayyukansa.

24 Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba. 25 Sai dai ku riƙe abin da kuke da shi har sai na zo.’

26 Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai. 27 ‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’ kamar yadda na karɓi iko daga Ubana. 28 Zan kuma ba shi tauraron asubahi. 29 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.