Yahuda Ya Rubuta wa Ikilisiya

Yahuda ya rubuta wasiƙarsa domin ya gargaɗi ikilisiyar Kirista game da koyarwar haɗari ta malaman ƙarya waɗanda suka bayyana a lokacin, suna mai da koyarwar alheri abin ƙarfafa lalata, kuma domin ya ƙarfafa su su riƙe bangaskiya da tsarki da ƙarfi.

66 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Yahuda Ya Gai da Waɗanda Aka Kira

Yahuda ya aika wasiƙarsa zuwa ga dukan waɗanda aka kira, aka kiyaye, aka kuma keɓe domin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kiristi. Ya albarkace su.

Yahuda 1:1–2

1 Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub,

Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye.

2 Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace.

Yahuda Ya Ƙarfafa Su Su Yi Gwagwarmaya Domin Bangaskiya

Bayan ya ji labarin koyarwar cutarwa ta malaman ƙarya, Yahuda ya ƙarfafa Kiristoci ƙwarai su yi gwagwarmaya domin bangaskiyar da Yesu Kiristi ya ba wa manzanni da annabawa ta wurin Ruhu. Gama wasu mutane marasa tsoron Allah sun kutsa cikin ikilisiya a ɓoye. Suna koyar da cewa alherin Allah yana da yawa har mutanen da suke da bangaskiya za su iya yin zunubi ba tare da an hukunta su ba, kuma sun musunci Uba da Ɗa duka (1 Yohanna 2:22). Tun daga farko dokar Allah ta riga ta bayyana hukuncinsu. Domin ya ƙaryata waɗannan koyarwar haɗari, Yahuda ya tuna musu da hukuncin da aka yi wa zaɓaɓɓun mutanen Allah ma saboda zunubansu (a kwatanta Ƙidaya 14:23 da Ibraniyawa 3:18–19); da hukuncin da aka tanada domin mala’ikun da ba su gamsu da matsayinsu ba, suka yi ƙoƙarin ɗaukaka kansu, suka bar wuraren zaman da aka ƙayyade musu; da kuma hallakar biranen Sodom da Gomorra gaba ɗaya har abada. Ya nuna cewa waɗannan malaman ƙarya da mabiyansu, ta wurin irin waɗannan zunubai na rashin bangaskiya, rashin biyayya da lalata, za su jawo wa kansu irin wannan hukunci. Suna ɓata suna, ko zagin, duk wata kafaffiyar hukuma, alhali Mika’ilu shugaban mala’iku, wanda ya fi su girma ƙwarai, bai yi wa shaidan ma zargi na ɓata suna ba, amma ya bar shi ga hukuncin Allah. Suna zagin dokoki da mahukunta, ba tare da sanin amfaninsu da asalinsu ba. Kamar dabbobi marasa hankali, suna bin ilhami ne kawai, suna kuma halaka kansu ta wurin biyan sha’awoyinsu na dabba. Sun bi misalin Kayinu, suna hallaka rayukan ’yan’uwansu; da na Bala’am, ta wurin gurɓata maganar Allah domin riba; da na Kora da ƙungiyarsa, ta wurin adawa da manzanni da masu hidimar Kiristi, kamar yadda ƙungiyar Kora ta yi adawa da Musa da Haruna. Lalle za su hallaka kamar yadda Kora da mabiyansa suka hallaka.

Yahuda 1:3–11

3 Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak. 4 Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.

5 Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba. 6 Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan. 7 Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.

8 Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama. 9 Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!” 10 Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su.

11 Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora.

Malaman Ƙarya Gizagizai Ne Marasa Ruwa

Yahuda ya gaya wa Kiristoci cewa waɗannan malamai abin kunya ne a bukukuwan ƙaunarsu, suna shagaltar da kansu da biyan sha’awoyinsu. Ya kwatanta su da gizagizai marasa ruwa (Maimaitawar Shari’a 32:2): matsayinsu yana ba da begen koyarwa mai kyau, amma ba sa ba da ita, kuma sha’awoyinsu suna kai su ko’ina. Su kansu sun kamu da cuta sosai har koyarwarsu ba za ta zama ba sai gurɓatacciya. Sun mutu a zahiri da kuma a ruhaniya, an tumɓuke su saboda rashin ’ya’ya. Suna da zafin hali da tashin hankali kamar raƙuman teku, suna fitar da muguntarsu kamar kumfa, kuma ba su da natsuwa ko tsari a halayensu (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 1:16; 2:1). Da yake ba su da haske, an tanadar musu duhu na har abada. Bisa ga tsohuwar al’ada, Enok, na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kansu (an kira shi haka domin a bambanta shi da Enok ɗan Kayinu, wanda yake na uku), sa’ad da ya faɗa tun da wuri hukuncin mugaye a zamaninsa da hallakarsu ta wurin Ruwan Tsufana. Gama waɗannan malaman ƙarya, kamar mutanen da suka rayu kafin Ruwan Tsufana, suna gunaguni game da abin da Allah ya raba musu cikin kulawarsa da kuma iyakokin da aka sa musu. Su ma masu girman kai ne da tawaye, suna yi wa mutane maganganun yabo domin ribar kansu.

Yahuda 1:12–16

12 Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. 13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.

14 Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa 15 don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.” 16 Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.

Ku Tuna da Abin da Manzanni Suka Faɗa Tun da Wuri

Maimakon su bi malaman ƙarya, Yahuda ya ƙarfafa su su tuna da koyarwar da manzanni suka ba su. Manzannin sun kuma riga sun faɗa game da zuwan waɗannan masu izgili masu bin sha’awa (2 Bitrus 3:2), waɗanda suke ware kansu daga almajiran Kiristi na gaskiya, suna da’awar cewa sun fi samun hasken fahimta, amma su mutanen duniya ne kawai, marasa Ruhu. Amma Kiristoci su gina kansu da juna cikin koyarwar Kiristi da manzanni, wadda take sa mutane su zama masu ruhaniya da tsarki. Su yi addu’a ga Allah ƙarƙashin jagorancin Ruhu Mai Tsarki, su ci gaba da ƙaunar Allah kullum, su kuma sa zuciya ga samun gafara daga Kiristi tare da rai madawwami. Su bambanta tsakanin waɗanda aka ɓatar saboda jahilci da rauni da waɗanda suka karkace saboda girman kai da gurɓatacciyar zuciya. Su gyara na farkon cikin taushi, su kuma ceci sauran daga halakar zunubi ta wurin ƙarfin tsoro, suna ƙin zunubansu matuƙa, domin kada su kansu su kamu da su.

Yahuda 1:17–23

17 Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā. 18 Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.” 19 Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.

20 Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.

22 Ku ji tausayin waɗanda suke shakka; 23 ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.

Yahuda Ya Miƙa Su ga Allah

Yahuda ya ƙare da miƙa su ga Allah, wanda shi kaɗai yake iya kiyaye su daga kamuwa da zunubi da ɓata, tare da yabonsa ga Allah Mai Cetonmu, wanda ɗaukakarsa da ikonsa za su dawwama a dukan zamanai har abada.

Yahuda 1:24–25

24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.