Bitrus Ya Sake Rubuta wa Kiristocin Yahuda da na Ba’al’ummai

Bitrus, yana sa ran ba da daɗewa ba zai mutu shahidi, ya rubuta wa Kiristocin Yahuda da na Ba’al’ummai waɗanda suke warwatse a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya da waɗansu ƙasashe. Ya rubuta don ya tabbatar da koyarwa da umarnin wasiƙarsa ta fari, kuma ya gargaɗe su game da kurakuran malaman ƙarya ta wurin tunatar da su hukuncin Allah a kan waɗanda suka yi ridda. Ya ƙarfafa su cikin tsanantawa ta wurin nuna musu kuɓutar farin ciki ta waɗanda suka dogara ga Allah, da kuma ƙarshen wannan duniya da na tsarin addinin Yahuda.

66 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bitrus Ya Sake Gaishe da Kiristocin Yahuda da na Ba’al’ummai

Gaisuwa da albarkar Bitrus. Yesu Kiristi ya naɗa shi manzo ga Yahudawa da Al’ummai, kuma ya ba manzannin ikon Allah ta wurin baiwar Ruhu Mai Tsarki iri-iri, domin su kawo mutane ga rayuwa ta ibada. Ana samun wannan ta wurin sanin Kiristi Yesu (Yohanna 17:3), wanda ya kira su zuwa ɗaukakar zama manzanninsa, ya cika su da ƙarfi da ƙarfin hali don wannan aiki, ya kuma ba su amanar dukan alkawuran bishara masu ɗaukaka, domin mutum ya sāke samun rabo cikin halin tsarki da rashin mutuwa, bayan ya kuɓuta daga lalacewar da sha’awa ta jawo a duniya. Su ƙara wa bangaskiyarsu ƙarfin hali na gaskiya da tsayuwar zuciya a lokacin da ake tsananta musu, tare da ƙara sanin koyarwar Kiristi; su ƙara wa sani kame kai cikin dukan jin daɗin duniya, da haƙuri cikin wahaloli, da ibada ga Allah; su ƙara wa ibada ƙaunar ’yan’uwansu Kiristoci, su kuma ƙara wa ƙaunar ’yan’uwa ƙaunar dukan mutane, ba tare da ware maƙiyansu ba. Idan waɗannan abubuwa suka yalwata a cikinsu, ba za su zama marasa aiki ko marasa amfani wajen ayyukan alheri ba. Amma duk wanda ba shi da ayyukan alheri da halayen Kirista masu bayyana a aikace, ya makantar da kansa da gangan, yana rufe idanunsa daga haske, yana kuma zaɓar ya manta da alkawarin da ya yi a baftisma na tsarkake kansa daga zunubansa na dā. Da yake mutane da yawa suna haka, an ƙarfafa su su ƙara himma sosai wajen tabbatar da kiransu da zaɓensu ta wurin bishara su zama ’ya’yan Allah da na ikilisiyarsa, ta yin ayyukan alheri ta wurin bangaskiya. Idan suna aikata waɗannan abubuwa, Allah zai riƙe su da alherinsa, ya kuma ba su shiga mulkinsa na har abada cikin daraja da nasara.

2 Bitrus 1:1–11

1 Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi,

Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu.

2 Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu.

3 Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa. 4 Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.

5 Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; 6 ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; 7 ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. 8 Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9 Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā.

10 Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba, 11 za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.

Bitrus Ya Ga Girman Kiristi da Idanunsa

Da yake aikata kyawawan halayen Kirista ta wurin bangaskiya ita ce kaɗai hanyar shiga mulkin Kiristi, Bitrus ya bayyana cewa yana ganin ya dace da aikinsa na manzo, muddin yana cikin jiki, ya riƙa tunatar da su waɗannan gaskiyoyi da suka riga suka kahu a cikinsu, ya kuma zuga su su aikata su. Da yake ya san mutuwarsa ta kusa (Yohanna 21:18–19), yana ƙoƙarin taimaka musu ta wurin rubuta musu, domin su riƙa tuna waɗannan abubuwa koyaushe bayan ya bar jiki. Gama sa’ad da suka sanar da su iko da bayyanar Yesu Kiristi, ba su yaɗa “tatsuniyoyin da aka ƙago da wayo” ba, irin labaran arna na allolinsu suna bayyana a duniya cikin surar mutum. Bitrus da kansa, tare da Yaƙub da Yohanna, ya ga girmansa a kan dutse mai tsarki, lokacin da Allah, daga ɗaukakarsa mai girma, ya bayyana cewa shi Ɗansa ne. Wannan murya da sāke kamanninsa sun tabbatar da annabce-annabcen Tsohon Alkawari game da Kiristi. Su mai da hankali gare su kamar hasken da ya jagoranci ’yan Adam cikin yanayinsu na jahilcin ruhaniya, har zuwa lokacin da ranar bishara za ta waye, tauraron safiya na adalci kuma zai haskaka a rayukansu. Su sani cewa babu annabcin da yake fitowa daga motsin ran mutum ko ƙagarsa. Gama a dā ba nufin mutum ne ya kawo annabci cikin tunanin waɗanda suka faɗe shi ba, amma tsarkakan mutanen Allah ne suka bayyana manufofin nufinsa yayin da Ruhu Mai Tsarki yake bishe su, wato yake hure su.

2 Bitrus 1:12–21

12 Saboda haka kullum zan tuna muku da waɗannan, ko da yake kun sansu kun kuma kahu ƙwarai cikin gaskiyar da kuke da ita yanzu. 13 A ganina ya dace in tunashe ku muddin ina raye cikin tentin wannan jiki, 14 domin na sani na kusa in ajiye shi a gefe, yadda Ubangijinmu Yesu Kiristi ya nuna mini a sarari. 15 Zan kuwa yi iyakacin ƙoƙari in ga cewa bayan rabuwata kullum za ku iya tuna da waɗannan abubuwa.

16 Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido. 17 Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba sa’ad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.” 18 Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama sa’ad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki.

19 Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku. 20 Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. 21 Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

Malaman Ƙarya da Tabbataccen Hukuncin Allah

Bitrus ya annabta cewa kamar yadda akwai annabawan ƙarya a cikin Yahudawa, waɗanda suka ɓatar da mutane da yawa, suna musun Allah wanda ya fanshe su daga bauta a Masar, haka kuma za a sami malaman ƙarya a cikin ikilisiyar Kirista. Za su shigo da karkatattun koyarwarsu masu halakarwa a ɓoye, suna musun Ubangijinmu wanda ya saye su da jininsa daga bautar zunubi da mutuwa (Fitowa 15:16; Maimaitawar Shari’a 32:6), suna kuma jawo wa kansu halaka. Mutane da yawa za su bi su, ta wurin muguwar rayuwarsu kuma za su sa a saɓi bishara, suna kasuwanci da rayukan mutane. Hukuncinsu, wanda aka ayyana a kan zunubi tun daga farko, ba ya jinkiri, amma zai riske su ba da daɗewa ba. Gama Allah bai bar mala’ikun da suka yi zunubi ba tare da hukunci ba, amma ya jefa su jahannama, yana tsare su har zuwa ranar shari’a a wurin azaba da duhu wanda ba za su iya tserewa daga gare shi ba. Bai bar duniyar dā ba tare da hukunci ba, haka ma biranen Sodom da Gomorra, amma ya mai da su misalin hukuncin da za a kawo wa marasa ibada a ranar ƙarshe. Ta wurin ceton Nuhu da Lot cikin mu’ujiza, Bitrus ya tabbatar da cewa lalle Allah zai ceci waɗanda suka dogara gare shi kuma suke bayinsa masu aminci daga gwaji da haɗari, kamar yadda lalle zai halaka malaman ƙarya da masu rashin biyayya da halaka ta har abada.

2 Bitrus 2:1–9

1 Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. 2 Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. 3 Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.

4 Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci; 5 in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai; 6 in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah; 7 in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka; 8 (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci) 9 in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a.

Malaman Ƙarya a Hanyar Bala’am

Bitrus ya bayyana halayen malaman ƙarya. Kamar dabbobi marasa hankali, suna bin ɗabi’ar dabbar da ke cikinsu, waɗanda aka yi don a kama a halaka domin suna halakarwa, suna saɓon abin da ba su fahimta ba, kuma za su hallaka cikin lalatattun koyarwarsu da ayyukansu. Suna nuna munanan halayensu a fili. Suna aikata lalata a bukukuwan ƙaunarsu. Suna yaudarar rayukan waɗanda ba su kahu cikin bangaskiya ba da ra’ayin cewa an kafa Jibin Ubangijinmu ne don a bunƙasa ƙaunar jiki, kuma sun ƙware a kowace irin dabarar lalata mutane da zamba. Suna bin hanyar Bala’am, wanda (Ƙidaya 31:16; Ru’ya ta Yohanna 2:14) ya yi saɓanin saninsa da lamirinsa domin ya sami ladar mugunta da aka yi masa alkawari.

2 Bitrus 2:10–16

10 Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki.

Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama; 11 duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji. 12 Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka.

13 Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku. 14 Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri! 15 Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta. 16 Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin.

Maɓuɓɓugan da Ba Su da Ruwa, Bayin Lalacewa

Bitrus ya kwatanta malaman ƙarya da maɓuɓɓugan da ba su da ruwa, da kuma gizagizan da suke nuna alamar ruwan sama amma su ƙare da hadari su jawo halaka maimakon su biya begen mutane. Ta wurin halatta kowace irin lalata da holewa, suna jawo waɗanda suka ware kansu daga arna su zama almajiransu. Suna yi musu alkawarin ’yancin biyan sha’awoyinsu ba tare da wani hani ba, alhali halinsu yana nuna cewa su bayin lalacewa ne. Gama duk wanda sha’awoyinsa suka rinjaya, ya zama bawansu. Ga waɗanda sanin bishara ya juyo da su daga bautar gumaka da lalata da holewar duniyar arna, suka kuma sāke shiga tarkonsu, ƙazantar da za su shiga a ƙarshe za ta fi ta farko kawo mutuwa, domin sun yi zunubi ga hasken ruhaniya da gata mafi girma da aka ba su.

2 Bitrus 2:17–22

17 Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu. 18 Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure. 19 Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi. 20 In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko. 21 Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su. 22 A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”

Malaman Ƙarya Masu Musun Zuwan Kiristi

Bitrus ya nuna cewa manufarsa ta rubuta wasiƙunsa biyu ita ce ya tunatar da su annabce-annabcen annabawan dā (Zabura 1:1; Daniyel 12:2), da koyarwa da umarnan manzanni da aka kafa a kansu. Ya san cewa annabawa sun annabta bayyanar malaman ƙarya waɗanda za su musanta cewa Kiristi zai zo ya yi wa duniya shari’a (Irmiya 17:15; Ezekiyel 12:22–27; Yahuda 1:14–15; Daniyel 12:2). Da gangan suke ƙin sanin cewa sama, wato sararin iska, da ƙasa sun samu ne daga ruwa ta wurin maganar Allah, kuma da wannan ruwa aka riga aka halaka duniya saboda muguntar mutum. Ƙasar yanzu da sararin iskarta, waɗanda suke wanzuwa ta wannan hanya ɗaya, su ma suna iya fuskantar irin wannan halaka saboda dalili ɗaya. Amma an adana su ana kiyaye su daga ambaliyar ruwa, domin ambaliyar wuta ta cinye su a ranar sakayya da shari’a.

2 Bitrus 3:1–7

1 Abokaina ƙaunatattu, wannan ita ce wasiƙata ta biyu gare ku. Na rubuta su biyun su zama abin tuni don su faɗakar da ku ga tunani mai kyau. 2 Ina so ku tuna da kalmomin da annabawa masu tsarki na dā suka faɗa da kuma umarnin da Ubangijinmu da Mai Cetonmu ya bayar ta wurin manzanninku.

3 Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu. 4 Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.” 5 Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma. 6 Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci. 7 Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.

Ranar Ubangijinmu Za Ta Zo Kamar Ɓarawo

Bitrus ya gargaɗi ’yan’uwa Kiristoci kada masu izgili su ruɗe su, waɗanda suka ɗauka daga jinkirin Allah cewa ko dai ba shi da ikon cika alkawuransa, ko kuma ba shi da niyyar cika su. Su tuna cewa babu wani tsawon lokaci, kome tsawonsa, da za a kwatanta da kasancewar Allah har abada, kuma babu wani lokaci da zai iya canja manufofinsa (Zabura 90:4). Ba dalilin da waɗannan malamai suka bayar ne ya sa zuwan Ubangijinmu yake jinkiri ba, amma saboda haƙurinsa ne da kuma rashin son kowa ya hallaka. Duk da jinkirin ranar Ubangijinmu, tabbas za ta zo farat ɗaya, ta faɗa wa mutane kamar ɓarawo da dare (Mattiyu 24:43). Sa’an nan dukan sararin iska tare da tururinsa za su shuɗe da wuta, da ƙara mai girma da fashe-fashe, abubuwan da aka yi su da su kuma za su kama da wuta su rabu, dukan tsarin duniyar zahiri kuma, tare da dukan ayyukan halitta da na fasaha da ke cikinta, za a ƙone su ƙurmus. Da yake dukan abubuwan duniya za su narke, suna da dalilai mafi ƙarfi na yin rayuwa mai tsarki da ibada ga Allah, suna marmarin zuwan ranar Allah maimakon su ji tsoronta, ranar da wannan tsarin duniya zai narke. Gama bisa ga alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim da zuriyarsa ta ruhaniya (Romawa 4:13–16; Ishaya 65:17–23; 66:22), su sa rai ga “sabuwar sama da sabuwar ƙasa” (Ru’ya ta Yohanna 21:27; 22:14–15), madawwamiyar mazaunar ruhohi masu albarka.

2 Bitrus 3:8–13

8 Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. 9 Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.

10 Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu.

11 Da yake za a hallaka dukan abubuwa ta haka, waɗanne irin mutane ne ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi rayuwar tsarki da ta tsoron Allah, 12 yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi. 13 Amma bisa ga alkawarinsa muna zuba ido ga sabuwar sama da kuma sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zama.

A Same Ku da Tsarki Sa’ad da Kiristi Ya Zo

Da yake an yi wa dukan Kiristoci alkawarin gādon Kan’ana na har abada, wato sabbin sammai da sabuwar duniya (Luka 20:35), Bitrus yana ƙarfafa su su yi matuƙar ƙoƙari domin Kiristi, Alƙalin masu rai da matattu, ya same su masu tsarki, marasa laifi, masu amfani a rayuwarsu, kuma masu salama da shi. Su ɗauki jinkirin zuwansa a matsayin tabbacin nufinsa na cewa dukan mutane su sami ceto, kamar yadda Bulus, ta wurin hurewar Allah, ya rubuta musu (Afisawa 2:3, 4, 5; Kolossiyawa 1:21; 1 Tessalonikawa 3:13; 4:14–18; 2 Tessalonikawa 1:7–10; Titus 2:13). Bulus ya kuma rubuta game da tashin matattu (1 Korintiyawa 15:22; Filibbiyawa 3:20–21), ƙonewar duniya (2 Tessalonikawa 1:8), ƙasar sama inda masu adalci suke zama (1 Tessalonikawa 4:17; Ibraniyawa 4:9; 12:14, 18, 24) da kuma hukuncin dukan mutane (Romawa 14:10). Wasu daga cikin waɗannan abubuwa suna da wuyar fahimta ga ɗan Adam, kuma marasa ilimi da waɗanda ba su kahu a bangaskiya ba suna karkatar da su, kamar yadda suke yi wa sauran sassan Nassin, suna lalata ɗabi’un mutane, suna jawo wa kansu halaka. Amma su, tun da manzanni da annabawa sun riga sun yi musu gargaɗi game da waɗannan koyarwar ƙarya, su yi hankali da su, suna ƙaruwa kowace rana cikin sanin koyarwar Yesu Kiristi, suna kuma ba shi ɗaukaka yanzu har zuwa ranar madawwami.

2 Bitrus 3:14–18

14 Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kuna zuba ido ga wannan, sai ku yi matuƙar ƙoƙari don a same ku ba tabo, sai dai zaman salama da shi. 15 Ku yi zaman sanin cewa haƙurin Ubangijinmu yana nufin ceto ne, kamar yadda ƙaunataccen ɗan’uwanmu Bulus ma ya rubuta muku da hikimar da Allah ya ba shi. 16 Haka yake rubutu cikin dukan wasiƙunsa, yana magana a cikinsu a kan waɗannan al’amura. Wasiƙunsa sun ƙunshi waɗansu abubuwa masu wuyar fahimta, waɗanda jahilai da kuma waɗanda ba tsayayyu ba ne suke murɗe ma’anarsu, kamar yadda suke yi da sauran Nassosi, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.

17 Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kun riga kun san wannan, sai ku zauna a faɗake don kada a ɗauke hankalinku ta wurin kuskuren marasa bin dokan nan har ku fāɗi daga matsayinku. 18 Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.

A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin.