Nauyin da ke Kan Mata da Mazajensu Kiristoci

Bitrus ya ci gaba da jaddada musu manyan nauye-nauyen dangantakar iyali. Ya gaya wa matan Kirista su yi biyayya ga mazajensu, ko da mazajensu arna ne, domin ta wurin halayensu masu tsarki su jawo su ga ƙaunar bishara da aikata ta. Don su sami ƙaunar mazajensu, kada su taƙaita adonsu ga kamannin waje, sai dai su fi ƙawata ran da yake ɓoye a ciki, suna bin misalin Saratu, wadda ta amince da kasancewarta ƙarƙashin Ibrahim ta wurin kiransa ubangiji. Su 'ya'yanta mata ne muddin suna aikata abin da ya dace da halinsu na Kirista. An umarci mazajen Kirista su bi da matansu yadda ya dace da waɗanda aka koya wa nauye-nauyen addinin Kirista.

65 ko 66 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Bitrus 3:1–7

1 Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2 sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3 Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4 Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. 5 Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, 6 kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.

7 Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.

Ku Saka wa Mugunta da Albarka

A ƙarshe, Bitrus ya ƙarfafa kowa, masu aure da marasa aure, su kasance da haɗin kai na Kirista, tausayi da ƙauna, suna saka wa mugunta da zagi da albarka. Kullum su yi abin da lamirinsu yake nuna musu, domin kyawawan halayensu cikin Kiristi su kunyata waɗanda suke zarginsu da aikata mugunta a kan ƙarya. Idan nufin Allah ya sa su sha wahala, ya fi kyau su sha wahala saboda aikata alheri maimakon saboda aikata mugunta.

1 Bitrus 3:8–17

8 A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u. 9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka. 10 Gama,

“Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,

yă kuma ga kwanaki masu kyau

dole yă ƙame harshensa daga mugunta

leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;

dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,

amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”

13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.

Wahalolin Kiristi, Jirgin Nuhu da Baftisma

A wani ɗan kaucewa daga batun, domin kada su ɗauki wahalolinsu a matsayin alamar rashin jin daɗin Allah da su, Bitrus ya ƙarfafa su ta wurin duba wahalolin Kiristi. Ko da yake Kiristi mai cikakken adalci ne, ya sha wahala saboda zunuban waɗansu, domin ya kawo mutum wurin Allah. An kashe shi cikin yanayinsa na ɗan adam, amma an sake rayar da shi ta wurin Ruhun Allah. Ta wurin wannan Ruhu, wanda ya ba Nuhu ikon ruhaniya, ya yi wa'azi ga ruhohin da a yanzu aka kulle, ko aka tsare, kamar a kurkuku ƙarƙashin shari'ar adalcin Allah, don su karɓi hukuncin da ya dace da zunubansu. Allah ya yi haƙuri yana jira shekara 120 don ya ga ko za su tuba su sami ceto, sa'ad da ake gina jirgin (Farawa 6:3). Sa'an nan iyalin Nuhu, waɗanda suka ba da gaskiya, suka sami ceto ta wurin ruwa. Wannan alama ce ta ceton iyalin Kiristi, cikin jirgin ikkilisiya, ta wurin ruwan baftisma, wanda ta wurinsa ake kawo su cikin sabon yanayin rayuwa kuma a cece su daga kabari ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu. Ya shiga sama, kuma an sa mala'iku da kowane rukuni na halittu, a sama da ƙasa, a ƙarƙashinsa, domin ya ba dukan waɗanda suka gaskata da shi ceto.

1 Bitrus 3:18–22

18 Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu, 19 ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi 20 waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa, 21 ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 22 wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.

Matattu ga Zunubi, Masu Rayuwa don Nufin Allah

Tun da Kiristi ya sha mutuwa mai raɗaɗi cikin jiki saboda ɗan adam, Bitrus ya kira su su ma su gicciye halin jiki, domin waɗanda suka kashe halin jiki sun daina zunubi, ko kuma sun mutu ga zunubi. Suna yin sauran rayuwarsu ba bisa ga sha’awoyin halin jiki ba, sai dai bisa ga nufin Allah. Gama sun ɓata lokaci fiye da kima a rayuwarsu ta dā cikin abubuwan banƙyama da munanan ayyuka na kunya waɗanda masu bautar gumaka suka tsunduma a ciki. Yanzu masu bautar gumaka suna mamaki, suna kuma yi musu ƙiren ƙarya domin ba sa haɗa kai da su cikin wannan wuce gona da iri na lalata, suna mantawa cewa dole ne su ba da lissafi ga wanda zai yi wa masu adalci da miyagu shari’a. Saboda wannan ne aka yi wa masu bautar gumaka bishara, waɗanda suke matattu cikin laifofi da zunubai, domin waɗanda suka ba da gaskiya, ko da mutanen da halin jiki yake mulka sun yi musu shari’a ko suka hukunta su, su rayu bisa ga nufin Allah cikin ruhu.

1 Bitrus 4:1–6

1 Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. 2 Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. 3 Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. 4 Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku. 5 Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu. 6 Dalilin ke nan da ya sa aka yi wa’azin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu.

Ikon Masu Tsananta Musu Zai Ƙare Ba da Daɗewa Ba

Bitrus ya ta’azantar da su da tabbacin cewa ba da daɗewa ba za a hallaka ikon masu tsananta musu ƙwarai, a hallakar da za ta auka wa mutanen Yahuda da ƙasarsu a matsayin daula. Ya ƙarfafa su, domin su tsira daga wannan, su yi tsaro daga kowace irin ƙazanta kuma su yi addu’a, suna da ƙauna mai zafi, wadda take jure wa kurakuran juna ko ta shafe su. A wannan lokaci na tsanantawa su riƙa karɓar juna a gidajensu, ba tare da la’akari da wahalar da hakan zai jawo ba. Kowa ya yi hidima bisa ga baiwar tanadin Allah da alherinsa da ya karɓa daga wurin Ubangiji. Duk mai magana a kan maganar Allah ya yi magana “kamar wanda yake isar da kalmomin Allah.” Duk mai biyan bukatun matalauta ya yi haka daga abin da Allah ya ba shi, yana ba Allah ɗaukaka ta wurin Yesu Kiristi.

1 Bitrus 4:7–11

7 Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a. 8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa. 9 Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba. 10 Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam. 11 In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.

Ku Yi Farin Cikin Raba Wahalolin Kiristi

Bitrus yana gargaɗin Kiristoci kada su yi mamakin masifu da tsanantawar da suke zuwa a kansu, waɗanda aka nufa don a gwada bangaskiyarsu, sai dai su yi farin ciki, tun da yake ta wurinsu suna da rabo cikin wahalolin Kiristi, domin a ɗaukaka su tare da shi. Masu albarka ne waɗanda ake zagi saboda su Kiristoci ne, gama Ruhun Allah da ya sauka a kan Yesu yana sauka a kansu su ma: masu tsananta musu suna saɓon Kiristi, amma ta wurin wahalolinsu ana girmama shi. Saboda haka yana gargaɗinsu kada su sha wahala saboda wani laifin da suka aikata (yana ambaton laifofin da Yahudawa marasa bangaskiya suka ba da kansu gare su), wanda ba ya kawo ɗaukaka ko lada. Amma duk wanda yake shan wahala saboda shi Kirista ne kada yă ji kunya, ko yaya hukuncin yake da kunya, sai dai yă ɗaukaka Ubangiji, wanda shi ma ya sha wahala saboda shi mai tsarki ne. Lokaci ya yi yanzu na hukuncin Yahudawa a matsayin al’umma, wanda zai fara daga gidan Allah (Yohanna 16:2; Mattiyu 23:35; Ezekiyel 9:6). In ya fara da Yahudawa masu bi tukuna, wace hallaka mai bantsoro ce za ta auko wa waɗanda ba sa biyayya ga bishara? In kuwa Kiristoci sukan tsira daga hukuncin Allah a kan Urushalima da ƙyar ƙwarai, ta yaya marasa tsoron Allah da masu zunubi za su sa zuciya ga kuɓuta? Bitrus ya ce wa Al’ummai da kuma Yahudawa masu shan wahala saboda adalci su danƙa rayukansu ga Allah kamar ga Mahaliccinsu mai aminci, wanda zai lura da su a matsayin halittunsa da ’ya’yansa, ya kuma ba su rai madawwami, in sun ci gaba da aikata nagarta.

1 Bitrus 4:12–19

12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14 In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku. 15 In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi. 16 Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna. 17 Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah? 18 Kuma,

“In da ƙyar masu adalci su kuɓuta,

me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?”

19 Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.

Dattawa Su Yi Kiwo ga Garken Allah

Bitrus ya ƙarfafa dattawa, a matsayinsa na wanda ya ga wahalolin Kiristi da idanunsa (a lambun, a lokacin kama shi da kuma a zauren babban firist), wanda kuma ya gani ya kuma raba ɗaukakar sāke kamanninsa, su ciyar da garken Kiristi da aminci. Su yi aikin bishop-bishop, wato masu kulawa, a waɗannan lokutan tsanantawa, ba domin an matsa musu ba amma da yardar rai, ba don neman abin rayuwa ba amma da tsananin marmarin ƙara ɗaukakar Allah. Kada su nuna iko na danniya a kan garkunan, waɗanda suke gādon Allah, amma su zama misalan tawali'u da kowace irin ɗabi'ar alheri ta Kirista a gare su. Kuma idan Babban Makiyayi ya bayyana, wanda garkunan suke nasa, waɗanda suka yi aikinsu za su karɓi rawanin ɗaukaka daga wurinsa.

1 Bitrus 5:1–4

1 Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana. 2 Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima; 3 ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken. 4 Sa’ad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa.

Ku Kasance da Tawali'u Kuma Ku Yi Tsayayya da Iblis

Bitrus ya umarci waɗanda suke riƙe da ƙananan muƙamai a ikkilisiya su yi biyayya ga dattawa, sa'an nan ya kira su duka su yi biyayya, suna yi wa juna hidima a matsayin da kowa yake, kuma su yafa tawali'u a matsayin tufafi, tsaro da kāriya. Tun da Allah yana gāba da masu girman kai, ya kamata su ƙasƙantar da kansu su kuma yi biyayya da haƙuri ga yadda yake bi da su cikin kowane haɗari da wahala, suna ɗora dukan damuwarsu ga Allah, wanda yake kula da su (Zabura 55:22). Abin da kaɗai ya kamata su damu da shi shi ne su mallaki sha'awoyinsu, suna da kamun kai kuma kullum suna lura da kansu, domin a wannan lokacin gwaje-gwajensu da masifunsu abokin gābansu na ruhaniya yana yawo, “yana neman wanda zai cinye,” da begen sa su fāɗi daga bangaskiya. Dole ne su yi tsayayya da shi, suna tsaye da ƙarfi cikin bangaskiya ga Ɗan Allah, suna sane cewa rabon almajiran Kiristi ne su sha tsanantawa daga mutane da aljanu. Bitrus ya yi addu'a ga Allah ya ƙarfafa su ya kuma kammala su cikin bangaskiyar Kiristi.

1 Bitrus 5:5–11

5 Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin,

“Allah yana gāba da mai girman kai,

amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”

6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

10 Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. 11 Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin.

Bitrus Ya Aika Wasiƙarsa Ta Hannun Sila

Bitrus ya gaya musu cewa yana aika wannan wasiƙa ta hannun Sila (wanda shi ne Sila da aka ambata a Ayyukan Manzanni 15:40; 16:19), kuma a ganinsa ya rubuta musu a taƙaice, yana shaida musu cewa abin da aka yi musu wa’azi a kai shi ne bisharar Kiristi ta gaskiya. Ya roƙe su su gai da juna a matsayin alamar ƙaunarsu ta Kirista, kuma ya ƙare da albarkarsa ta manzo.

1 Bitrus 5:12–14

12 Da taimakon Sila, wanda na ɗauka a matsayin ɗan’uwa mai aminci, na rubuta muku a taƙaice, ina ƙarfafa ku ina kuma shaida muku cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske. Ku tsaya daram a cikinsa.

13 Ita wadda take a Babilon, zaɓaɓɓiya tare da ku, tana gaishe ku, haka ma ɗana Markus.

14 Ku gai da juna da sumbar ƙauna.

Salama gare ku duka da kuke cikin Kiristi.