Bitrus Ya Rubuta wa Kiristoci Yahudawa da na Al’ummai

Bitrus ya rubuta wasiƙarsa ta farko ga Yahudawa waɗanda, a lokacin tsanantawa, suka nemi mafaka a ƙasashen arna da aka ambata a farkonta, da kuma waɗanda suka tuba daga cikin Al’ummai. Ya rubuta domin ya ƙarfafa su su jure wahala da farin ciki saboda addininsu, ya kuma jaddada musu bukatar yin rayuwa mai tsarki marar zargi, domin su kunyata ƙiren ƙaryar abokan gābansu.

65 ko 66 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bitrus Ya Gai da Kiristoci Yahudawa da na Al’ummai

Gaisuwa da albarkar Bitrus ga Yahudawa da Al’ummai waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah, wanda annabawa suka bayyana, don su zama masu biyayya ga bishara ta wurin aikin Ruhu Mai Tsarki. Ta haka suke da rabo cikin dukan albarkun da suke fitowa daga jinin Kiristi na kafara.

1 Bitrus 1:1–2

1 Bitrus, manzon Yesu Kiristi,

Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya, 2 waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa.

Alheri da salama su zama naku a yalwace.

Bitrus Ya Yabi Allah Saboda Sabuwar Haihuwarsu

Bitrus yana yabon Allah saboda haihuwa ta ruhaniya ta Yahudawa da Al’ummai zuwa ga begen rai bayan mutuwa ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, domin su sami rabo cikin gādon da ba ya lalacewa. Cikin begen wannan ceto ya kamata su yi farin ciki ƙwarai, ko da yake suna baƙin ciki saboda wahaloli iri-iri. Ana bukatar waɗannan don a gwada bangaskiyarsu, wadda gwajinta ya fi na zinariya daraja, tun da yake yana samo musu madawwamiyar ɗaukaka da yabo a zuwan Yesu Kiristi. Suna farin ciki ƙwarai a cikinsa a matsayin Mai Ceto, ko da yake ba sa ganinsa, da sanin cewa za su karɓi ladar bangaskiyarsu daga gare shi, wato ceton rayukansu. Annabawa sun yi annabcin wannan ceto, suna bincike da kyau don su san lokaci da kuma mutanen da Ruhun Allah yake nufi, sa’ad da ya yi shaida tun da wuri game da wahalolin Kiristi da ɗaukaka da albarkun da za su biyo bayansu. Ruhu Mai Tsarki ya kuma bayyana wa annabawa cewa ba kansu suke yi wa hidima ba, sai dai mutanen wani zamani mai zuwa, cikin abubuwan da manzanni suke sanar wa duniya yanzu, waɗanda wannan Ruhu Mai Tsarki ɗin ya ba su iko saboda wannan manufa. Waɗannan asirai mala’iku, da kuma mutane, “suna marmari su duba” (Fitowa 25:20).

1 Bitrus 1:3–12

3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 4 da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, 5 ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci. 6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.

10 Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse, 11 suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi. 12 Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.

Ku Yi Rayuwa Cikin Tsoro Mai Tsarki, An Fanshe Ku da Jinin Kiristi

Saboda albarkun da wahalolin Kiristi suka samo, Bitrus yana kiransu su ƙarfafa zuciya cikin dukan gwaje-gwajensu, begen rai madawwami da aka yi musu alkawarinsa a ranar da za a bayyana Kiristi yana riƙe da su har ƙarshen rayuwarsu. Ya kamata su guji sha’awace-sha’awacen da suka aikata kafin su tuba, su kuma yi koyi da tsarkin Allah, wanda ya kira su su zama ’ya’yansa, kamar yadda Musa ya rubuta (Firistoci 19:2; 1 Bitrus 5:10; 2:21; 3:9). Tun da yake za a yi wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa, ba tare da nuna bambanci ba, ana roƙonsu su yi zaman lokacin baƙuncinsu a duniya cikin tsoro na girmamawa. Balle ma, tun da yake an cece su daga camfe-camfe, al’adu ko gurɓatattun ayyukan ibada da suka gāda daga kakanninsu ta wurin jinin Kiristi, kamar na hadayar zunubi marar lahani. An naɗa Kiristi cikin nufin Allah kafin kafuwar duniya, aka kuma nuna inuwarsa ta wurin hadayar Doka, amma aka bayyana shi a zamani na ƙarshe, wato zamanin bishara, ga Al’ummai ma. Ta wurin bangaskiya ga jinƙan Allah da aka nuna cikin wannan hadayar Kiristi, suna gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu ya kuma ɗaukaka shi zuwa ɗaukakar sama, domin, da bangaskiyarsu ta kafu cikin cikar alkawuran Allah, begensu na madawwamiyar ɗaukaka ta wurin Kiristi ya kasance ga Allah.

1 Bitrus 1:13–21

13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; 16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”

17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18 Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19 sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.

An Sāke Haifar Ku, Ku Ƙaunaci Juna

Bitrus ya ƙarfafa waɗanda aka tsarkake zukatansu daga sha’awoyin jiki ta wurin gaskatawa da Kiristi Yesu su ƙaunaci juna, ba da ayyuka da kalmomin ƙarya ba, sai dai da zuciya mai tsabta wadda ba ta da sha’awoyin jiki, a matsayin ’yan’uwa da aka sāke haifa. Ba a sāke haifar su ta wurin zuriyarsu daga iyayen mutane ba, sai dai daga tushe na allahntaka da na sama, wato koyarwar Allah mai rai, wadda take dawwama har abada.

1 Bitrus 1:22–25

22 Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya. 23 Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. 24 Gama,

“Dukan mutane kamar ciyawa suke,

darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;

ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,

25 amma maganar Ubangiji tana nan har abada.”

Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

Duwatsu Masu Rai a Haikalin Allah na Ruhaniya

Bitrus yana roƙonsu su watsar da dukan mugayen halaye na tsohon halinsu, kuma, kamar jarirai da aka sāke haifa ta wurin alherin Allah, su yi marmarin madara marar gauraye ta bishara, domin sabon halinsu ya sami abinci har ya kai ga girma, tun da yake sun riga sun ɗanɗana nagarta da fifikon Ubangiji a cikin haihuwarsu ta biyu, ta ruhaniya (Zabura 34:8). Da suke zuwa gare shi ta wurin bangaskiya kamar ga dutsen tushe mai rai, ana gina su a kansa suna kuma da rabo cikin rayuwarsa, har su zama haikali na ruhaniya da ƙungiyar firistoci (Fitowa 19:6; Ru’uya ta Yohanna 1:6), waɗanda aka naɗa don su miƙa hadayun addu’a da yabo ta wurin Kiristi. Haka Ishaya ya furta (Ishaya 28:16) cewa a Sihiyona za a kafa “zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja,” a matsayin tushen sabon haikalin Allah, wanda zai haɗa ɓangarorin gini biyu, Yahudawa da Al’ummai, cikin ikkilisiya ɗaya (Afisawa 2:21). Waɗanda suka gaskata suna cikin wannan gini. Amma game da marasa biyayya an rubuta (Zabura 118:22) cewa wannan dutsen tushe da aka ƙi “ya zama dutsen kusurwar gini” na sabon haikalin Allah, da kuma “dutsen tuntuɓe” ga waɗanda ba su gaskata da Kiristi ba, wanda za su fāɗi a kansa su farfashe, kamar yadda Ishaya ya yi annabci (Ishaya 8:14–15). Bitrus ya kwatanta manyan gatan Kirista da lakabobin da aka taɓa ba wa ikkilisiyar Yahudawa, ga dukan waɗanda aka shigar da su cikin alkawari da Allah.

1 Bitrus 2:1–10

1 Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna. 2 Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, 3 yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji.

4 Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse, da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi 5 ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi. 6 Gama a cikin Nassi an ce,

“Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona,

zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja,

wanda kuma ya dogara gare shi

ba zai taɓa kunyata ba.”

7 A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba,

“Dutsen da magina suka ƙi

ya zama dutsen kusurwar gini,

8 kuma,

“Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe

kuma fā ne da yake sa su fāɗi.”

Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.

9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki. 10 Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.

A Matsayin Baƙi, Ku Miƙa Kai ga Kowace Gwamnatin ’Yan Adam

Da yake nuni ga Isra’ilawa na dā (Ibraniyawa 11:13), Bitrus ya kira su, a matsayin baƙi da matafiya waɗanda ba su da gādo a duniya (kamar yadda suke a zahiri a Asiya, Fontus da sauran ƙasashe), su nemi ƙasa ta sama, su kuma guji sha’awoyin jiki, waɗanda suke bautar da rai ko kuma halaka shi. Su yi rayuwa yadda ayyukansu masu kyau za su ƙaryata ƙiren ƙaryar abokan gābansu. Su miƙa kai ga kowace irin gwamnatin ’yan Adam saboda Ubangiji, domin su rufe bakin jahilcin wawaye waɗanda suke da’awar cewa addininsu ya sa ba sa son yin biyayya ga sarakuna da mahukunta. A matsayin zaɓaɓɓun mutanen Allah, Yahudawa sun yi fahariyar cewa su mutane ne masu ’yanci, waɗanda dokokinsu suke mulka. Da wannan a zuciyarsa, Bitrus ya kira su su bari dokokin addininsu su mulke su a zuciya, amma kada su yi amfani da ’yancinsu a matsayin abin rufe tawaye, kamar yadda Yahudawa suka yi, sai dai su yi rayuwa a matsayin bayin Allah.

1 Bitrus 2:11–17

11 Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku. 12 Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.

13 Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, 14 ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai. 15 Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci. 16 Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. 17 Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.

Masu Hidima Su Sha Wahala Kamar Yadda Kiristi Ya Sha Wahala

Bitrus ya ƙarfafa bayin gida da masu hidima su yi biyayya ga iyayengijinsu cikin miƙa kai da girmamawa, har ma ga masu tsauri da rashin adalci, kada su sa biyayyarsu ta dogara da halin waɗanda suke yi wa hidima. Su sha wahala saboda yin alheri, suna bin misalin Kiristi, wanda ya sha wahala dominsu domin su bi sawunsa. Babu zunubi a cikinsa (Ishaya 53:6). Ya ɗauki hukuncin da zunubi ya cancanta, domin ya ’yantar da mutum daga ikonsa.

1 Bitrus 2:18–25

18 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma. 19 Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. 20 Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah. 21 Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi.

22 “Bai taɓa yin laifi ba sam,

ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.”

23 Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci. 24 Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa. 25 Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku.