Hatimi na Farko: Bishara Ta Yi Nasara

An buɗe hatimi na farko. Wahayin da ya biyo baya ya sanar da nasarar bishara a kan Yahudawa da Al’ummai gaba ɗaya.

96 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ru’uya ta Yohanna 6:1–2

1 Na kalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!” 2 Na duba, can kuwa a gabana ga wani farin doki! Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi rawani, ya yi sukuwa ya fito kamar mai nasara da ya kutsa don nasara.

Hatimi na Biyu: An Warwatsa Yahudawa

An buɗe hatimi na biyu. Ya sanar da munanan tsanantawa da kuma warwatsa Yahudawa gaba ɗaya a ƙarƙashin mulkin Trajan da Hadrian (102–138).

Ru’uya ta Yohanna 6:3–4

3 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!” 4 Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi.

Hatimi na Uku: Salama da Wadata

An buɗe hatimi na uku. Ya sanar da salama da wadata a zamanin mulkin iyalin Septimius Severus (193–235).

Ru’uya ta Yohanna 6:5–6

5 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa. 6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!”

Hatimi na Huɗu: Yaƙi, Yunwa, da Annoba

An buɗe hatimi na huɗu. Ya sanar da munanan yaƙe-yaƙe, yunwa, tsanantawa, da annobobi da suka yaɗu a zamanin mulkin Maximinus, Decius, da Valerian (255–271).

Ru’uya ta Yohanna 6:7–8

7 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!” 8 Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya.

Hatimi na Biyar: Tsanantawa ta Ƙarshe daga Maguzawa

An buɗe hatimi na biyar. Ya sanar da tsanantawa ta ƙarshe da maguzawa suka yi wa addinin Kirista, da kuma tsoron Kiristoci (286–301).

Ru’uya ta Yohanna 6:9–11

9 Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. 10 Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” 11 Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.

Hatimi na Shida: An Kifar da Maguzanci

An buɗe hatimi na shida. Ya nuna tashe-tashen hankulan Daular Romawa a lokacin da aka kifar da maguzanci gaba ɗaya, da kuma kafuwar ikkilisiyar Kirista cikin nasara a madadinsa. Wannan ɓangaren wahayin kuma yana nuni ga farin ciki na har abada na shahidan farko, da yabon da suke yi wa Allah da Ɗan Rago (323).

Ru’uya ta Yohanna 6:12–7:17

12 Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, 13 taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi. 14 Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa.

15 Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. 16 Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! 17 Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”

7:1 Bayan wannan, na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace. 2 Sai na ga wani mala’ika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa mala’ikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku ya ce, 3 “Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.” 4 Sai na ji yawan waɗanda aka sa musu hatimi. Su 144,000 daga dukan kabilan Isra’ila.

5 Daga kabilar Yahuda mutum 12,000 ne aka sa musu hatimin,

daga kabilar Ruben mutum 12,000,

daga kabilar Gad mutum 12,000,

6 daga kabilar Asher mutum 12,000,

daga kabilar Naftali mutum 12,000,

daga kabilar Manasse mutum 12,000,

7 daga kabilar Simeyon mutum 12,000,

daga kabilar Lawi mutum 12,000,

daga kabilar Issakar mutum 12,000,

8 daga kabilar Zebulun mutum 12,000,

daga kabilar Yusuf mutum 12,000,

daga kabilar Benyamin mutum 12,000.

9 Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. 10 Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,

“Ceto na Allahnmu ne,

wanda yake zaune a bisan kursiyi,

da kuma na Ɗan Ragon.”

11 Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12 suna cewa,

“Amin!

Yabo da ɗaukaka,

da hikima da godiya da girma

da iko da ƙarfi

sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.

Amin!”

13 Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?”

14 Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.”

Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. 15 Saboda haka,

“suna a gaban kursiyin Allah

suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa;

kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu.

16 ‘Ba za su sāke jin yunwa ba;

ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba.

Rana ba za tă buga su ba,’

ko kuma kowane irin zafin ƙuna.

17 Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu;

‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’

‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”

Hatimi na Bakwai: Mala’iku Bakwai da Ƙahoni

An buɗe hatimi na bakwai. Mala’iku bakwai masu ƙahoni bakwai sun bayyana a sama. An sanar da addu’o’in godiya na Kiristocin da yanzu suke hutawa, da karɓar addu’o’insu da Allah ya yi, tare da halakar da ’yan barbari za su yi wa daular nan gaba.

Ru’uya ta Yohanna 8:1–5

1 Sa’ad da ya buɗe hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kusan rabin sa’a. 2 Sai na ga mala’iku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai.

3 Wani mala’ika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yă miƙa tare da addu’o’in dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin. 4 Hayaƙin turaren tare da addu’o’in tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun mala’ikan. 5 Sai mala’ikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa.

Ƙaho na Farko: Al’ummomin Arewa Sun Mamaye

Wani sabon zamani na kifar da ikon Romawa, wanda har zuwa wannan lokaci ya danne mutumin zunubi, ya fara da busa ƙahoni bakwai. An busa ƙaho na farko. Abubuwan al’ajabi da suka biyo baya suna nuni ga mamayar Daular Romawa da al’ummomin barbari na Arewa za su yi (323–412).

Ru’uya ta Yohanna 8:6–7

6 Sai mala’iku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su.

7 Mala’ika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.

Ƙaho na Biyu: Vandalawa Sun Yi Nasara

An busa ƙaho na biyu. Vandalawa da Alanawa a ƙarƙashin Genseric sun lalata ikon siyasa na Daular Romawa ta Yamma (395–455).

Ru’uya ta Yohanna 8:8–9

8 Mala’ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai ga wani abu kamar babban dutse mai cin wuta, aka jefa cikin teku. Kashi ɗaya bisa uku na teku ya zama jini, 9 kashi ɗaya bisa uku na halittu masu rai da suke cikin tekun suka mutu, kashi ɗaya bisa uku kuma na jiragen ruwa kuma suka hallaka.

Ƙaho na Uku: An Sa Ruwa Ya Yi Ɗaci

An busa ƙaho na uku. A nan ana iya yin nuni ga tuɓe Augustulus, sarkin Romawa na ƙarshe a Yamma; ko riddar shugabannin ikkilisiya masu kwaɗayin mulki ko gurɓacewarsu; ko yaɗuwar ra’ayoyin Augustine, waɗanda fiye da sauran ra’ayoyi suka sa ruwan rai ya yi ɗaci, suka kuma lalata haɗin kan Kiristoci (455–476).

Ru’uya ta Yohanna 8:10–11

10 Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa 11 sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.

Ƙaho na Huɗu: Ragowar Ikon Roma Ya Ƙare

An busa ƙaho na huɗu. Ya annabta yaƙe-yaƙe a Italiya tsakanin waɗanda suka ci Roma da yaƙi, da janar-janar na Justinian, da Gothawa, da kuma kafuwar gwamnatin gwamna na Ravenna, wadda ta shafe dukan ragowar ikon Roma, har zuwa shekara ta 606.

Ru’uya ta Yohanna 8:12

12 Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare.

An Shirya Hanya don Manyan Riddodi Biyu

Yanzu wani zamani mai muhimmanci a tarihin ’yan Adam ya fara. Gurɓacewar da ta yaɗu tsakanin Kiristoci da raunin siyasar daular sun shirya hanya don manyan riddodi biyu, waɗanda za su ɗauki shekaru 1260 kuma su tashi tare a daulolin gabas da yamma (606).

Ru’uya ta Yohanna 8:13

13 Yayinda nake kallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce, “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala’ikun nan uku suke shirin busawa!”