Ƙaho na Biyar: Muhammadu da Saracenawa
An bayyana tasowa, bunƙasa, da kifarwa ta ƙarshe na riddodi biyu masu tafiya tare, manyan maƙiyan salama, ilimi, da farin cikin ’yan Adam guda biyu, wato mulkin fafaroma da Musulunci, ta wurin ƙahonin kaito biyu na farko, da kuma ƙahon kaito na uku har zuwa kwano na shida, wanda aka zubo a ƙarƙashin na uku. An busa ƙaho na biyar, ko ƙahon kaito na farko. Faɗuwar tauraro, wato gurɓacewar ikkilisiyar gabas, ta kawo riddar Muhammadu da Saracenawa, waɗanda suka ci Kiristocin da suke cikin ɓata da yaƙi na shekaru 150 (606 zuwa 762).
96 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. 2 Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. 3 Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya. 4 Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani. 5 Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum. 6 Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu.
7 Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane. 8 Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki. 9 Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi. 10 Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar. 11 Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon.
Ƙaho na Shida: Masarautun Sultan Huɗu Sun Kai Hari
Bayan dogon lokaci an busa ƙaho na shida. Masarautun sultan huɗu na ƙarfin mulkin Musulmi, waɗanda manyan biranensu su ne Bagadaza, Damaskus, Aleppo, da Ikoniyum, sun fara barin ƙasashensu kusa da Yuferites suna kai wa Kiristoci hari, suka sami nasararsu ta farko a 1281. Sun lalata daular Hellenawa, aikin da aka shirya su dominsa (1453). Sun ƙwace ƙarin ƙasa na ƙarshe a 1672.
12 Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa.
13 Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah. 14 Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.” 15 Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam. 16 Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu.
17 Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa. 18 Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu. 19 Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni.
20 Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba. 21 Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
Wani Littafin Naɗi Dabam don Daular Yamma
Bayan annabcin ya faɗi tarihin daular gabas tun da wuri, ya ci gaba zuwa tarihin daular yamma a wannan lokaci ɗaya na shekaru 1260. Wani mala’ika dabam ya ba Yohanna wannan ɓangaren annabcin a matsayin littafin naɗi dabam, don a bambanta shi da abubuwan da ƙahonin kaito biyu suka annabta.
1 Sai na ga wani babban mala’ika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta. 2 Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa, 3 ya kuma yi ihu da ƙarfi kamar rurin zaki. Da ya yi ihun, sai muryoyin tsawan nan bakwai suka yi magana. 4 Sa’ad da tsawan nan bakwai kuwa suka yi magana, ina dab da rubutawa; amma na ji wata murya daga sama ta ce, “Rufe abin da tsawan nan bakwai suka faɗa kada ka rubuta.”
5 Sai mala’ikan da na gani na tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama. 6 Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri! 7 Amma a ranakun da mala’ika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”
8 Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.”
9 Sai na je wajen mala’ikan na ce masa yă ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yă yi tsami, amma ‘a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.’ ” 10 Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun mala’ikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma sa’ad da na cinye, cikina ya yi tsami. 11 Sa’an nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, al’ummai, harsuna da kuma sarakuna.”
Shaidu Biyu cikin Tufafin Buhun Makoki
An raba ƙaramin littafin naɗi, wanda ya ƙunshi tarihin annabci na cocin yamma, zuwa sassa biyar. Sashe na farko yana nuna bambanci tsakanin Kiristoci na suna kawai da Kiristoci na ruhaniya, da kuma raini, sakaci da aka yi ko'ina, da ƙiyayya ga Nassi da masu fassara shi da gaskiya, ta wurin kwatancin shaidu biyu suna annabci sanye da tufafin makoki. Yana annabta cewa waɗannan shaidu za su yi annabci kusan shekaru 1260, har lokacin da shaidarsu cikin tufafin makoki za ta kusan ƙarewa, sa'an nan za a kashe su, su tashi daga matattu, su kuma yi nasara a kan waɗanda suka yi farin ciki da mutuwarsu. Wannan zai faru kafin a busa ƙaho na bakwai. Wannan sashe na Ru'ya ta Yohanna yana da wuyar fahimta ƙwarai: wataƙila gabatarwa ce ta gaba ɗaya ga abubuwan da ƙaramin littafin naɗi ya ƙunsa (606–1866).
1 Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can. 2 Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Al’ummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42. 3 Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.” 4 Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. 5 Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu. 6 Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so.
7 To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. 8 Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu. 9 Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su. 10 Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya.
11 Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su. 12 Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo.
13 A wannan sa’a aka yi wata babbar girgizar ƙasa kashi ɗaya bisa goma kuma na birnin ya rushe. Aka kashe mutane dubu bakwai a girgizar ƙasar, waɗanda suka tsira kuwa suka ji tsoro suka ɗaukaka Allah na sama.
14 Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba.