Ƙaho na Bakwai: Ikkilisiya Ta Yi Murna
An busa ƙaho na bakwai. Ikkilisiya ta dukan duniya ta yi murna da nasarar shaidun da ake sa ran samu a ƙarshen shekaru 1260.
96 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
15 Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce,
“Mulkin duniya ya zama
mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa,
zai kuwa yi mulki har abada abadin.”
16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, 17 suna cewa,
“Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,
domin ka karɓi ikonka mai girma
ka kuma fara mulki.
18 Al’ummai suka yi fushi;
fushinka kuwa ya zo.
Lokaci ya yi don a shari’anta matattu,
da kuma don sākawa wa bayinka annabawa
da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka,
ƙarami da babba,
don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.”
Dodon Ya Tsananta wa Ikkilisiya
Kashi na biyu na ƙaramin littafin naɗi. Ta wurin hoton mace mai haihuwar ɗa namiji cikin azaba, da korarta zuwa jeji da dodon mai kawuna bakwai da ƙahoni goma ya yi, an annabta tsanantawa ga ikkilisiyar Kiristi, wadda take haifar da Kiristoci na gaskiya masu aminci, ta hannun mugun ruhun da ya fara kawo mugunta cikin wannan duniya. Wannan gwagwarmaya ma ta ɗauki shekaru 1260, daga 606 zuwa 1866.
19 Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma.
12:1 Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta. 2 Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa. 3 Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa. 4 Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi. 5 Ta haifi ɗa, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al’ummai da sandar ƙarfe. Aka fyauce ɗanta zuwa wurin Allah da kuma kursiyinsa. 6 Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260.
7 Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani. 8 Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama. 9 Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.
10 Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa,
“Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu,
da kuma ikon Kiristinsa.
Gama mai zargin ’yan’uwanmu,
wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana,
an jefar da shi ƙasa.
11 Sun ci nasara a kansa
ta wurin jinin Ɗan Ragon
da ta wurin kalmar shaidarsu;
ba su ƙaunaci rayukansu sosai
har da za su ja da baya daga mutuwa.
12 Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai,
da ku da kuke zaune a cikinsu!
Amma kaiton duniya da kuma teku,
gama Iblis ya sauko gare ku!
Ya cika da fushi,
domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.”
13 Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji. 14 Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba. 15 Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya. 16 Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa. 17 Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.
Wakilin Mugun Ruhu Shi Ne Ikon Roma
Kashi na uku na ƙaramin littafin naɗi, wanda ya bayyana wakilin mugun ruhun da ya tsananta wa ikkilisiyar Allah ta gaskiya na shekaru 1260, ta wurin alamomin da suka dace da ikon Roma kaɗai.
1 Macijin kuwa ya tsaya a bakin teku. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo. 2 Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma. 3 Ɗaya daga cikin kawunan dabbar ya yi kamar yana da raunin da zai iya kashe shi, amma raunin nan da zai iya kashe shi ya riga ya warke. Dukan duniya ta yi mamaki ta kuma bi dabbar. 4 Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?”
5 Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girman kai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arba’in da biyu. 6 Ta buɗe bakinta don tă yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama. 7 Aka ba ta iko tă yaƙi tsarkaka tă kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jama’a, harshe da kuma al’umma. 8 Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada, dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba.
9 Duk mai kunne ji, bari yă ji.
10 Duk wanda aka ƙaddara ga bauta,
ga bauta zai tafi.
Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi,
da takobin za a kashe shi.
Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka.
Mulkin Ruhaniya na Ikkilisiyar Roma
Kashi na huɗu na ƙaramin littafin naɗi, wanda ya nuna mulkin ruhaniya na Ikkilisiyar Roma, wanda gwamnatocin duniya na Turai suka goyi baya kuma suka amince da shi a tsawon shekaru 1260.
11 Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji. 12 Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta. 13 Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu banmamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane. 14 Saboda alamun nan da aka ba ta iko tă yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu. 15 Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada. 16 Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, 17 don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta.
18 Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666.