Mala’iku Uku Sun Yi Kira ga ’Yan Adam
Kashi na biyar na ƙaramin littafin naɗi ya nuna halin dannewa da ikkilisiyar Allah ta ruhaniya take ciki a tsawon shekaru 1260. Ta wurin kwatancin mala’iku uku masu kira ga ’yan Adam, da alama ya annabta Gyaran Addini ta hannun Luther, da ƙoƙarin Ingila na yanzu wajen wayar da kan ’yan Adam, da kuma hamayya da mulkin fafaroma da za ta fi samun nasara a nan gaba.
96 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. 2 Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. 3 Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya. 4 Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon. 5 Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.
6 Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. 7 Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”
8 Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.”
9 Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, 10 shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. 11 Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.” 12 Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu.
13 Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.”
“I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.
Girbin Hatsi da Inabi na Fushin Allah
Bayan annabin ya faɗi abin da ƙaramin littafin naɗi ya ƙunsa, ya ci gaba zuwa busa ƙahon kaito na uku, lokacin da za a zubo kwanoni bakwai, ko tsawa bakwai su yi ƙara, waɗanda mala’ikan ya hana Yohanna rubutawa (Ru’ya ta Yohanna 10:4) har sai ya bayyana annabce-annabcen ƙaramin littafin naɗi. An bayyana (Ru’ya ta Yohanna 10:7) cewa asirin Allah zai cika a kwanakin muryar mala’ika na bakwai. An faɗi munanan abubuwan da za su zo kafin kafa mulkin Kiristi, a ƙarshen shekaru 1260, ta wurin alamomin girbin inabi da girbin hatsi na fushin Allah. Ana sa ran nasarar ikkilisiyar Allah bayan hukunce-hukuncensa sun cika.
14 Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa. 15 Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.” 16 Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya.
17 Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi. 18 Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.” 19 Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah. 20 Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300.
15:1 Na ga wata babbar alama mai banmamaki a sama, mala’iku bakwai da annobai bakwai na ƙarshe, na ƙarshe, domin da su ne fushin Allah ya cika. 2 Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su 3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,
“Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,
ya Ubangiji Maɗaukaki.
Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,
ya Sarkin zamanai.
4 Wane ne ba zai ji tsoronka,
yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?
Gama kai kaɗai ne mai tsarki.
Dukan al’ummai za su zo
su yi sujada a gabanka,
gama an bayyana ayyukan adalcinka.”
Mala’iku Bakwai Sun Shirya Kwanonin Fushi
Yanzu an busa ƙahon kaito na bakwai. A kashi na farko na wahayin shekaru 1260, an bayyana cewa an busa shi bayan ci gaban ikokin Musulmi ya cika (wanda ya ƙare a ƙarshe a 1698; Ru’ya ta Yohanna 11:15–18), kuma ya kawo ƙarshen tarihin annabci na daular gabas har zuwa lokacin da za a kifar da wannan addini. An nuna mala’iku bakwai suna shirya kwanonin fushin Allah, don hukunta duniya, da ikokin Musulmi, da ikokin fafaroma, da ikokin marasa bangaskiya, kafin zamanin addinin Kirista na dukan duniya ya fara (1698 zuwa 1860).
5 Bayan wannan sai na duba, a cikin sama kuwa sai ga haikali, wato, tabanakul na Shaida, a buɗe. 6 Daga cikin haikalin mala’iku bakwai tare da annobai bakwai suka fito. Suna saye da tufafin lilin masu tsabta masu walƙiya, suna kuma saye da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu. 7 Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa mala’iku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin. 8 Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na mala’iku bakwai.
16:1 Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”
Kwano na Farko: Juyin Juya Halin Faransa
An zubo kwano na farko, kuma girbin fushin Allah ya fara. An annabta wani mummunan bala'i tsakanin ƙarshen yaɗuwar Musulunci da ƙarshen shekaru 1260 da yake gabatowa. A fahimtarmu, zubar da wannan kwano yana annabcin Juyin Juya Halin Faransa, bala'i mafi muni da ya taɓa faɗa wa mabiyan addinin shugaban cocin Roma, wanda tasirinsa har yanzu yake tayar da hankalin dukan duniyar da ta ci gaba. Ƙurjin da aka annabta zai addabi tsarin shugabancin cocin Roma yana iya zama rashin bangaskiya (1789–1791).
2 Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada.
Kwano na Biyu: Teku Ya Zama Jini
An zubo kwano na biyu, kuma teku ya zama jini. Wannan alama tana iya kwatanta yaƙe-yaƙe da kisan kiyashi masu zubar da jini da suka addabi duniya a lokacin (1791–1794).
3 Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu.
Kwano na Uku: Koguna Sun Zama Jini
An zubo kwano na uku, kuma koguna da maɓuɓɓugan ruwa sun zama jini. Waɗannan alamomi suna iya wakiltar gurɓata tushen ilimi da rashin bangaskiya, da kuma halakar da ƙananan ƙasashen Turai a lokacin yaƙe-yaƙen juyin juya hali (1794–1801).
4 Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini. 5 Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce,
“Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai,
kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan;
6 gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka,
ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.”
7 Na kuma ji bagaden ya amsa,
“I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”
Kwano na Huɗu: Wataƙila Daular Napoleon
An zubo kwano na huɗu. An kwatanta duniya tana ƙonewa saboda zafin rana. Da yake rana sananniyar alama ce ta ikon sarauta, watakila ana nufin daular Napoleon (1801–1814).
8 Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta. 9 Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.
Kwano na Biyar: Mabiyan Shugabancin Cocin Roma Suna Cikin Azaba
An zubo kwano na biyar. An kwatanta mabiyan tsarin shugabancin cocin Roma suna cikin ƙunci da azaba. Yanzu muna rayuwa a ƙarƙashin wannan kwano. Wataƙila wannan alama tana nufin ƙiyayyar Roma ta shugaban coci ga ci gaban ilimi mai ƙaruwa wanda ba a iya dakatarwa, wanda yake tona rashin ma'ana da kurakuran addinin shugaban cocin Roma ba tare da ya haifar da gyara da tuba ba.
10 Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba 11 suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.
Kwano na Shida: Daular Turkiyya Tana Raunana
An zubo kwano na shida. A wannan lokaci ƙarshen shekaru 1260 ya kusanto. Alamomin da suke ƙarƙashin wannan kwano suna kwatanta faɗuwar daular Turkiyya da ta ƙara kusantowa, ko da yake har yanzu tana faruwa a hankali, da shirye-shiryen maido da Yahudawa, da farkon babban ƙawancen masu iko masu gāba da Kiristi a kan cocin Kiristi a Falasɗinu, ƙarƙashin tasirin mugayen ƙa'idoji ko addinan ƙarya.
12 Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas. 13 Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan. 14 Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.
15 “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”
16 Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon.