Kwano na Bakwai: Yaƙin Armageddon

An zubo kwano na bakwai. Yanzu shekaru 1260 sun wuce. Girbin inabin fushin Allah, wanda annabawan dā suka daɗe suna annabtawa, yanzu ya fara, tare da manyan tashe-tashen hankula da dogayen yaƙe-yaƙe a faɗin duniya. Yanzu an kai ga yanke hukuncin doguwar gwagwarmayar da ke tsakanin nagarta da mugunta. Addinan ƙarya na tsarin mulkin Paparoma da rashin bangaskiya sun haɗa kai a kan ragowar ikilisiya, da Yahudawa da suke taruwa domin a maido da su kamar yadda aka daɗe ana yi musu alkawari, da kuma babbar ƙasar da take da ƙarfin teku, wadda da alama ita ce Ingila (Ishaya 17:18), har yaƙin Armageddon ya faru a Falasɗinu. Watakila wannan kwano ya ƙunshi shekaru masu yawa.

96 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ru’uya ta Yohanna 16:17–21

17 Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!” 18 Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce. 19 Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa. 20 Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba. 21 Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.

Tsarin Shugabancin Cocin Roma Kafin Faɗuwarsa

Bayan sanarwar waɗannan manyan al'amura a dunƙule, an nuna wa annabin tarihin tsarin mulkin Paparoma da yanayinsa kafin a rushe shi gaba ɗaya.

Ru’uya ta Yohanna 17

1 Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. 2 Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.”

3 Sa’an nan mala’ikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma. 4 Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. 5 Sunan da aka rubuta a goshinta asiri ne,

Babilon mai girma

mahaifiyar karuwai

da kuma na abubuwa masu banƙyama na duniya.

6 Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu.

Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai. 7 Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka asirin macen nan da dabbar da take hawa, wadda take da kawuna bakwai da ƙahoni goma. 8 Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo.

9 “Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai. 10 Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma sa’ad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci. 11 Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta.

12 “Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na sa’a guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar. 13 Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu. 14 Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.”

15 Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna. 16 Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta. 17 Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika. 18 Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.”

Faɗuwar Tsarin Shugabancin Cocin Roma da Rashin Addini

An bayyana faɗuwar tsarin shugabancin cocin Roma da rashin addini dalla-dalla.

Ru’uya ta Yohanna 18

1 Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa. 2 Ya yi kira da babbar murya ya ce,

“Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi.

Ta zama gidan aljanu

da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu,

wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama.

3 Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin

haukan zinace zinacenta.

Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita,

attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”

4 Sai na ji wata murya daga sama ta ce,

“Ku fita daga cikinta, mutanena,

don kada zunubanta su shafe ku,

don kada wata annobarta ta same ku;

5 gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama.

Allah kuma ya tuna da laifofinta.

6 Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku;

ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi.

Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata.

7 Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki

kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta.

A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce,

‘Ina zama kamar sarauniya;

ni ba gwauruwa ba ce,

kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’

8 Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata,

mutuwa, makoki da kuma yunwa.

Wuta zai cinye ta,

gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta.

9 “Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita. 10 Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa,

“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma.

Ya ke Babilon, birni mai iko!

Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’

11 “Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu 12 kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; 13 kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.

14 “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’ 15 Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki 16 su ce,

“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma,

saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja,

mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai!

17 Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’

“Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. 18 Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’ 19 Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa,

“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma,

inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku

suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa!

Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’

20 “Ki yi murna a kanta, ya sama!

Ku yi murna, ku tsarkaka!

Ku yi murna, ku manzanni da annabawa!

Allah ya hukunta shi

saboda abin da ya yi muku.”

21 Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce,

“Da wannan irin giggitawa

za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa,

ba za a ƙara ganin ta ba.

22 Ba za a ƙara jin

ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho

a cikinki ba.

Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’a

a cikinki kuma ba.

Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa

a cikinki kuma ba.

23 Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa

a cikinki ba.

Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya

a cikinki ba.

Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya.

Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce.

24 A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka,

da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”