Coci Yana Murna Saboda Faɗuwar Maƙiyansa
Coci na ruhaniya yana murna saboda faɗuwar maƙiyansa masu bautar gumaka da tsanantawa.
96 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa,
“Halleluya!
Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,
2 gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma.
Ya hukunta babbar karuwan nan
wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta.
Ya rama jinin bayinsa a kanta.”
3 Suka sāke tā da murya suka ce,
“Halleluya!
Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.”
4 Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce,
“Amin, Halleluya!”
5 Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa,
“Ku yabi Allahnmu,
dukanku da kuke bayinsa,
ku da kuke tsoronsa,
babba da yaro!”
6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,
“Halleluya!
Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.
7 Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna
mu kuma ɗaukaka shi!
Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi,
amaryarsa kuwa ta shirya kanta.
8 Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta
ta sanya.”
(Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)
9 Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”
10 Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”
Da Alama Ɗan Allah Zai Bayyana Lokacin Da Aka Rushe Mugunta
Bayyanar Ɗan Allah a fili, wadda da alama za ta faru lokacin da aka rushe mugunta gaba ɗaya, kamar yadda ya bayyana ga kakannin dā, da kuma ga manzanni bayan tashinsa daga matattu; da farkon sabon tsarin zamanin Allah, da nasarar ikilisiya ta ruhaniya.
11 Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. 12 Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. 13 Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. 14 Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. 15 Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki. 16 A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce,
Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.
17 Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah, 18 don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.”
19 Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa. 20 Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. 21 Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.
An Ɗaure Shaiɗan na Shekaru Dubu
Bayan dogayen tashe-tashen hankula, yaƙe-yaƙe, da juyin juya hali da suka zo tare da rushewar mugunta, wani dogon lokacin hutawa na shekaru dubu ya fara, wanda aka kwatanta da ɗaure Shaiɗan. Kamar yadda ruhohin mutane da yawa suka tashi tare da Kiristi a tashinsa daga matattu, an ce ruhohin shahidai da na amintaccen coci za su sāke rayuwa tare da Kiristi a lokacin bayyanarsa a fili a wannan lokaci (2000–3000).
1 Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. 2 Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. 3 Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci.
4 Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu. 5 (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko. 6 Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.
Mugunta Ta Sāke Farfaɗowa, Sai Hukunci na Ƙarshe
Zuwa ƙarshen tsarin zamanin shekaru dubu, ruhun mugunta ya fara farfaɗowa, amma tashin dukan matattu da hukuncin ƙarshe na 'yan Adam sun dakatar da ci gabansa.
7 Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, 8 zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. 9 Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su. 10 Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin.
11 Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. 12 Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. 13 Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. 14 Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. 15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.
Babu Sauran Mutuwa, Mugunta, da Baƙin Ciki
Bayanin farin ciki na har abada da zai zo, lokacin da mutuwa, mugunta, da baƙin ciki ba za su ƙara kasancewa a cikin 'yan Adam ba.
1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”
Kiristi Yana Gayyatar Kowa Ya Shiga Wannan Farin Ciki
Kiristi yana bayyana tabbaci da gaskiyar wannan kwatanci, yana kuma gayyatar dukan mutane su shiga wannan farin ciki.
5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”
6 Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. 7 Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. 8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”