An Ƙone Haikalin da Ke Urushalima (continued)

588 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 94

1 Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa,

Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka.

2 Ka tashi, ya Alƙalin duniya;

ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su.

3 Har yaushe mugaye, ya Ubangiji

har yaushe mugaye za su yi ta murna?

4 Suna ta yin maganganun fariya;

dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya.

5 Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji;

suna danne gādonka.

6 Suna kashe gwauraye da kuma baƙi;

suna kisan marayu.

7 Suna ce, “Ubangiji ba ya gani;

Allah na Yaƙub bai kula ba.”

8 Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane;

ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?

9 Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne?

Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?

10 Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne?

Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?

11 Ubangiji ya san tunanin mutum;

ya san cewa tunaninsu banza ne.

12 Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji,

mutumin da ka koyar daga dokarka;

13 kana ba shi sauƙi a lokacin wahala,

sai har an haƙa rami wa mugaye.

14 Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba;

ba zai taɓa yashe gādonsa ba.

15 Za a sāke kafa hukunci a kan adalci,

kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi.

16 Wane ne zai yi gāba da mugaye domina?

Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina?

17 Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba,

da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.

18 Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”

ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,

ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.

20 Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai,

wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?

21 Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci

suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa.

22 Amma Ubangiji ya zama kagarata,

Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.

23 Zai sāka musu saboda zunubansu

yă kuma hallaka su saboda muguntarsu;

Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.

2 Sarakuna 24:17–20

17 Sarkin Babilon ya sa Mattaniya, ɗan’uwan mahaifin Yehohiyacin, ya zama sarki a madadinsa, ya canja masa suna zuwa Zedekiya.

18 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna. 19 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi. 20 Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa.

To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.

Irmiya 52:4

4 A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, Sarkin Yahuda, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina katanga kewaye da ita.

Irmiya 39:2

2 A rana ta tara ga watan huɗu a shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya, sai aka huda katanga.

Irmiya 39:4–9

4 Sa’ad da Zedekiya sarkin Yahuda da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu; suka bar birnin da dare ta hanyar lambun sarki, ta ƙofar da take tsakanin katanga biyu, suka nufi waje Araba.

5 Amma sojojin Babiloniyawa suka bi su, suka ci wa Zedekiya a filayen Yeriko. Suka kama shi suka kai shi wurin Nebukadnezzar a Ribla a ƙasar Hamat, inda aka yanke masa hukunci. 6 A can Ribla sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idanunsa aka kuma kashe dukan manyan mutanen Yahuda. 7 Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya ya kuma buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babilon.

8 Sai Babiloniyawa suka cinna wa fadar da kuma gidajen mutane wuta suka farfasa katangar Urushalima. 9 Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya kwashi mutanen da suka rage a birnin zuwa zaman bauta a Babilon, tare da waɗanda suka riga suka tafi wurinsa, da kuma sauran mutanen.

2 Sarakuna 25:3–21

3 A rana ta tara ta watan huɗu, lokacin da yunwa ta yi tsanani a birnin, babu kuma abinci domin mutane su ci. 4 Sai aka huda katanga sa’an nan dukan sojoji suka tsere da dare a ƙofa tsakanin katanga biyu da suke kusa da lambun sarki, ko da yake Babiloniyawa sun kewaye birnin. Suka tsere suka nufi Araba. 5 Amma sojojin Babiloniyawa suka bi sarki, suka cin masa a filayen Yeriko. Dukan sojojinsa kuwa suka rabu da shi suka watse.

6 Aka kama shi, aka kai shi gaban sarkin Babilon a Ribla, inda aka yanke masa hukunci. 7 Suka kashe ’ya’yan Zedekiya a gabansa, sa’an nan aka ƙwaƙule idanunsa. Suka daure shi da sarƙar tagulla, suka kai shi Babilon.

8 A rana ta bakwai na watan biyar, wadda ta zama shekara ta goma sha tara ta mulkin Sarki Nebukadnezzar na Babilon, Nebuzaradan, babban hafsan matsaran sarki, kuma bafadan sarkin Babilon, ya zo Urushalima 9 Ya cinna wa haikalin Ubangiji wuta, da fadan sarki, da kuma dukan gidajen Urushalima. Ya kuma ƙone duk wani gini mai muhimmanci. 10 Dukan mayaƙan Babilon a ƙarƙashin umarnin babban hafsan matsaran sarki, suka rushe katangar Urushalima. 11 Nebuzaradan babban hafsan matsaran, ya kwashi waɗanda suka rage a cikin birnin, tare da sauran jama’a, da waɗanda suka miƙa kansu ga sarkin Babilon, ya kai su bauta. 12 Amma hafsan ya bar waɗansu daga cikin mafiya talauci na ƙasar don su yi aiki a lambunan inabi da kuma gonaki.

13 Babiloniyawan kuma suka sassare ginshiƙan tagulla, da wuraren zama da za a iya matsar da su, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla da yake a haikalin Ubangiji, suka kwashe tagullan zuwa Babilon. 14 Suka ɗauke tukwane, da manyan cokula, da acibalbal, da kwanoni, da dai dukan kayan da aka yi da tagulla don hidima a haikalin Ubangiji. 15 Babban hafsan matsaran sarkin ya kwashe har da kwanoni na kwashe garwashin wuta da sauran kwanoni, dukansu kuwa ƙeran zinariya ko azurfa tsatsa ne.

16 Tagullar ginshiƙai biyun nan, da ta ƙaton kwanon da ake ce da shi Teku, da ta dukan amalanke masu riƙe ruwa waɗanda Sarki Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji, sun fi gaba a auna su. 17 Tsawon kowane ginshiƙi, ƙafa ashirin da bakwai ne. Hulunan tagullan da suke ƙwalƙwalin kowane ginshiƙi kuma yana da tsawon ƙafa huɗu da rabi. Kuma aka yi masa ado da saƙa da ’ya’yan itace kewaye da shi. Bayan ginshiƙin ma haka yake.

18 Babban hafsan ya kwashi Serahiya babban firist, da Zefaniya na biye da shi a girma, da matsara ƙofofi uku. 19 Daga cikin waɗanda suka rage a birnin, ya ɗauki hafsa mai kula da dakaru, da kuma mashawartan sarki guda biyar. Ya kuma tafi da magatakarda wanda yake babban jami’in soja mai ɗaukan dukan jama’an ƙasar, tare da mutanensa guda sittin waɗanda aka samu a birnin. 20 Nebuzaradan, babban hafsan, ya kwashe su duka ya kawo su wurin sarkin Babilon a Ribla. 21 A can Ribla, a ƙasar Hamat, sarkin Babilon ya sa aka kashe su. Haka Yahuda ta tafi bauta daga ƙasarta.