An Ƙone Haikalin da Ke Urushalima (continued)

588 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 74

Maskil na Asaf.

1 Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah?

Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka?

2 Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa,

kabilar gādonka, wadda ka fansa,

Dutsen Sihiyona, inda ka zauna.

3 Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai,

dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki.

4 Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu;

suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu.

5 Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura

don yanka itatuwa a kurmi.

6 Sun ragargaje dukan sassaƙar katako

da gatura da kuma gudumarsu.

7 Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus;

suka ƙazantar da mazaunin Sunanka.

8 Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!”

Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar.

9 Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba;

ba sauran annabawan da suka ragu,

kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba.

10 Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah?

Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne?

11 Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama?

Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su!

12 Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa;

ka kawo ceto a kan duniya.

13 Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka;

ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye.

14 Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa

ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada.

15 Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka;

ka busar da koguna masu ruwa.

16 Yini naka ne, dare kuma naka ne;

ka kafa rana da wata.

17 Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya;

ka yi rani da damina.

18 Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji,

yadda wawaye suka ɓata sunanka.

19 Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji;

kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba.

20 Ka kula da alkawarinka,

domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar.

21 Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya;

bari matalauta da mabukata su yabe sunanka.

22 Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka;

ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini.

23 Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka,

ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi.

Zabura 83

Waƙa ce. Zabura ta Asaf.

1 Ya Allah, kada ka yi shiru;

kada ka tsaya cik,

ya Allah, kada ka daina motsi.

2 Dubi yadda abokan gābanka suke fariya,

dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.

3 Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka;

suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so.

4 Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma,

don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.”

5 Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare;

suka haɗa kai gāba da kai,

6 tentunan Edom da na mutanen Ishmayel,

na Mowab da kuma na Hagirawa,

7 Gebal, Ammon da Amalek,

Filistiya, tare da mutanen Taya.

8 Har Assuriya ma ta haɗa kai da su

don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot. Sela

9 Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan,

yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon,

10 waɗanda suka hallaka a En Dor

suka zama kamar juji a ƙasa.

11 Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib,

dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,

12 waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki

wuraren kiwon Allah.”

13 Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna,

kamar yayin da iska take hurawa,

14 kamar yadda wuta ke cin kurmi

ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu,

15 haka za ka kore su da iska mai ƙarfi

ka kuma firgita su da guguwarka.

16 Ka rushe fuskokinsu da kunya

don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.

17 Bari su kasance cikin kunya da taƙaici;

bari su hallaka cikin wulaƙanci.

18 Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji,

cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya.