An Ƙwace Urushalima An Kama Zedekiya; An ’Yantar da Irmiya
588 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
5 An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.
6 A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.
3 Sa’an nan dukan fadawan sarkin Babilon suka shiga suka zazzauna a Ƙofar Tsakiya. Wato, Nergal-Sharezer na Samgar-Nebo, Sarsekim wani babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da dukan sauran fadawan sarkin Babilon.
7 Sai aka huda katangan birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Babiloniyawa suke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba. 8 Amma sojojin Babiloniyawa suka runtumi sarki Zedekiya, suka ci masa a filayen Yeriko. Dukan sojoji suka yashe shi.
9 Da aka kama Zedekiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babilon a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babilon ya yanke masa shari’a. 10 Sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuda a Ribla. 11 Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babilon inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.
11 To, fa, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ba da wannan umarnai game da Irmiya ta wurin Nebuzaradan shugaban matsaran sarki cewa, 12 “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.” 13 Saboda haka Nebuzaradan shugaban matsara, Nebushazban babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da sauran hafsoshin sarkin Babilon 14 suka aika aka kawo Irmiya daga filin matsar. Suka miƙa shi ga Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, don yă kai shi gidansa. Saboda haka ya zauna a can a cikin mutanensa.
24 Shugaban matsara kuma ya ɗauki Serahiya babban firist, da Zefaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar, ya tafi da su. 25 Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai ’yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su. 26 Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babilon a Ribla, 27 Sarkin Babilon kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat.
Haka aka tafi da mutanen Yahuda bautar talala, daga ƙasarta.
An Ƙone Haikalin da Ke Urushalima
12 A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima. 13 Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima. 14 Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima.
17 Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon. 18 Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali. 19 Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.
20 Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna. 21 Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki. 22 A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman. 23 Akwai siffofin rumman tasa’in da shida da ake gani a gefen. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne.
15 Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon. 16 Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.
10 Amma Nebuzaradan shugaban matsaran ya bar waɗansu matalauta a ƙasar Yahuda, su da ba su da kome; a lokacin kuwa ya ba su gonakin inabi da kuma filaye.
Zabura ta Asaf.
1 Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka;
sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki,
sun bar Urushalima kufai.
2 Sun ba da gawawwakin bayinka
kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama,
nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.
3 Sun zubar da jini kamar ruwa
ko’ina a Urushalima,
kuma babu wani da zai binne matattu.
4 Mun zama abin reni ga maƙwabta,
abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
5 Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne?
Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta?
6 Ka zuba fushinka a kan al’umman
da ba su yarda da kai ba,
a kan mulkokin
da ba sa kira bisa sunanka;
7 gama sun cinye Yaƙub
suka lalatar da ƙasar zamansa.
8 Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu;
bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu,
gama mun fid da zuciya sarai.
9 Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,
saboda ɗaukakar sunanka;
ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu
saboda sunanka.
10 Don me al’ummai za su ce,
“Ina Allahnsu yake?”
A idanunmu, ka sanar wa al’ummai
cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar.
11 Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka;
ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.
12 Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai
zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.
13 Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka,
za mu yabe ka har abada;
daga tsara zuwa tsara
za mu yi ta ba da labarin yabonka.