Irmiya Ya Yi Makokin Rushewar Ƙasarsa

588 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Makoki 1–2

1 Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki,

birnin da a dā yake cike da mutane!

Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa,

wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe!

Ita da take sarauniya a cikin larduna

yanzu ta zama baiwa.

2 Tana yin kuka mai zafi da dare,

hawaye na gangara a kan kumatunta.

A cikin masoyanta duka

babu wanda ya yi mata ta’aziyya.

Duk abokanta sun yashe ta;

sun zama abokan gābanta.

3 Bayan wahala da baƙin ciki,

Yahuda ta tafi bauta.

Ta zauna a cikin ƙasashe,

ba tă samu wurin hutawa ba.

Duk masu fafararta sun same ta

sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.

4 Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki,

gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya.

Ba kowa a hanyoyin shiganta.

Firistocinta suna gurnani,

’yan matana kuma suna wahala,

kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.

5 Maƙiyanta sun zama shugabanninta;

Abokan gābanta suna da kwanciyar rai.

Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai

domin yawan zunubanta.

’Ya’yanta sun tafi bauta,

a ƙarƙashin maƙiyanta.

6 Diyar Sihiyona ba ta

da sauran daraja.

’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi

waɗanda suka rasa wurin kiwo;

cikin rashin ƙarfi suka guje

wa masu fafararsu.

7 A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo

Urushalima ta tuna da dukan dukiyar

da take da ita a kwanakin dā can.

Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta,

ba wanda ya taimake ta.

Maƙiyanta suka dube ta

suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.

8 Urushalima ta yi zunubi ƙwarai

saboda haka ta zama marar tsarki.

Dukan masu martaba ta sun raina ta,

gama sun ga tsiraicinta;

ita ma da kanta tana nishi da ƙyar

ta kuma juya baya.

9 Ƙazantarta ta manne wa rigunanta;

ba tă kula da nan gaba ba,

fāɗuwarta kuwa babban abu ne;

babu wanda zai yi mata ta’aziyya.

“Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata,

gama maƙiyi ya yi nasara.”

10 Maƙiya ya kwashe

dukiyarta duka;

ta ga mutanen da ba su san Allah ba

sun shiga wuri mai tsarkinta

waɗanda ka hana su

shiga taron jama’arka.

11 Dukan mutanenta suna nishi

da ƙyar suna neman burodi;

sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci

don kada su mutu da yunwa.

“Ubangiji, ka duba ka gani,

gama an yashe ni.”

12 “Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa?

Ku duba ku gani.

Ko akwai wata wahala kamar

irin wadda nake sha,

wadda Ubangiji ya auko mini

a cikin zafin fushinsa?

13 “Daga sama ya aiko da wuta,

ya aiko ta cikin ƙasusuwana.

Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna

ya juyo da ni.

Ya bar ni ni kaɗai,

sumamme dukan yini.

14 “Ya ɗaura zunubaina a wuyana;

aka naɗe su a hannuwansa.

Aka rataye su a wuyana

Ubangiji ya kwashe ƙarfina.

Ya bashe ni

ga waɗanda suka fi ni ƙarfi.

15 “Ubangiji ya ƙi

duk mayaƙan da suke tare da ni;

ya sa wata runduna ta tayar mini

ta kuma tattake samarina.

Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda

kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa.

16 “Dalilin da ya sa nake kuka ke nan

idanuna kuma suna ta zubar da hawaye.

Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya,

ba wanda zai sabunta ruhuna.

’Ya’yana sun zama fakirai

domin maƙiyina ya yi nasara.”

17 Sihiyona ta miƙa hannunta,

amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya.

Ubangiji ya umarta cewa

maƙwabtansa za su zama maƙiyansa;

Urushalima ta zama

abar ƙyama a cikinsu.

18 “Ubangiji mai adalci ne,

duk da haka na yi tawaye da umarninsa.

Ku saurara, jama’a duka;

ku dubi wahalar da nake sha.

Samarina da ’yan matana

duka sun tafi bauta.

19 “Na kira abokaina

amma sun yashe ni.

Firistocina da dattawana

sun hallaka a cikin birnin

yayinda suke neman abinci

don kada su mutu da yunwa.

20 “Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki!

Ina shan azaba a raina,

ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata,

domin na yi tawaye sosai.

A waje takobi na kisa;

a ciki kuma akwai mutuwa.

21 “Mutane suna ji ina nishi da ƙyar,

amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya.

Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki;

suna farin ciki da abin da ka yi.

Ka kawo ranan nan da ka sanar

domin su ma su zama kamar ni.

22 “Bari ka ga muguntarsu duka;

ka yi musu

yadda ka yi mini

domin dukan zunubansu.

Nishina da yawa

kuma zuciyata ta gaji.”

2:1 Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyona

da gizagizan fushi!

Ya jefar da darajar Isra’ila

daga sama zuwa ƙasa;

bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba

a ranar fushinsa.

2 Ubangiji ya hallakar

da wurin zaman Yaƙub ba tausayi;

A cikin fushinsa kuma zai rurrushe

kagaran Diyar Yahuda.

Ya ƙasƙantar da mulki

da masu mulki.

3 A cikin zafin fushi ya fasa

kowane ƙaho na Isra’ila.

Ya janye hannun damansa

sa’ad da maƙiyi ya zo.

Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙone

duk abin da yake kusa da ita.

4 Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa;

hannun damansa na shirye.

Kamar maƙiyi,

ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani;

ya zuba fushinsa kamar wuta

a kan tenti na Diyar Sihiyona.

5 Ubangiji kamar maƙiyi ne;

ya hallaka Isra’ila.

Ya hallaka wurarenta duka

ya kuma hallaka kagaranta.

Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki

wa Diyar Yahuda.

6 Ya rushe haikalinsa kamar lambu;

ya hallaka wurin yi masa sujada.

Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta

da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci;

a cikin zafin fushinsa

ya watsar da sarki da firist.

7 Ubangiji ya ƙi bagadensa

ya kuma yi wofi da haikalinsa.

Ya ba maƙiyinta fadodinta;

suka yi sowa a cikin gidan Ubangiji

kamar a ranar da ake yin biki.

8 Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangon

da yake kewaye da Diyar Sihiyona.

Ya auna da igiyar awo

bai fasa hallaka ta ba.

Ya sa katanga da katanga

duk suka lalace.

9 Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa;

ya kakkarya ƙarafanta.

Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta

duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe,

babu sauran doka,

annabawa kuma ba su samun

wahayi daga wurin Ubangiji.

10 Dattawan Diyar Sihiyona

sun zauna shiru a ƙasa;

suka kuma sa rigar buhu.

’Yan matan Urushalima suka

sunkuyar da kawunansu ƙasa.

11 Idanuna sun dushe don yawan kuka,

raina na cike da baƙin ciki;

zuciyata ta karaya

domin mutanena sun hallaka,

domin yara da jarirai suna suma

a kan hanyoyi a cikin birni.

12 Suna ce wa uwayensu,

“Ina burodi da ruwan inabi?”

Yayinda suke suma kamar mutanen

da aka ji masu ciwo a cikin birni,

sa’ad da suke mutuwa

a hannuwan uwayensu.

13 Me zan ce miki?

Da me zan kwatanta ki,

ke Diyar Urushalima?

Da me zan misalta ki,

yadda zan iya yi miki ta’aziyya,

Ke Budurwa Diyar Sihiyona?

Ciwonki yana da zurfi kamar teku.

Wane ne zai iya warkar da ke?

14 Wahayin annabawanki

ƙarya ne kuma marasa amfani;

ba su tona zunubanki ba

yadda za su iya ceto ki daga bauta ba.

Sun yi miki annabcin ƙarya

marar amfani.

15 Duk masu wucewa

suna yi miki tafi na reni;

suna yi wa Diyar Urushalima

tsaki suna kaɗa kai suna cewa,

“Wannan ne birnin da aka ce

kyakkyawa ne,

mai farantawa dukan duniya rai?”

16 Maƙiyanki duka suna ta surutu

game da ke;

suna tsaki suna cizon haƙora

suna cewa, “Mun hallaka ta.

Wannan ce ranar da muke jira;

yau mun gan ta.”

17 Ubangiji ya yi abin da ya shirya;

ya cika maganarsa,

wadda ya umarta tun daɗewa.

Ya jefar da ke ba tausayi,

ya bari maƙiya sun yi nasara da ke,

ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.

18 Zuciyar mutane

ta yi kuka ga Ubangiji.

Ya bangon Diyar Urushalima,

bar hawayenki su zuba kamar rafi

dare da rana;

kada ki huta,

kada idanunki su huta.

19 Ki tashi, ki yi kuka cikin dare,

dare na yi sai ki fara kuka;

kina buɗewa Ubangiji zuciyarki.

Ki ɗaga hannuwanki gare shi

domin rayukan ’ya’yanki,

waɗanda suka suma don yunwa

a kan kowane titi.

20 “Ka duba, ka gani ya Ubangiji.

Wane ne ka taɓa yi wa haka?

Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu,

’ya’yan da suka yi reno?

Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa

a cikin haikalin Ubangiji?

21 “Matasa da tsofaffi duk

suna kwanciya a cikin ƙurar tituna;

an karkashe matasa

da ’yan matana da takobi.

Ka kashe su a ranar fushinka;

ka kashe su ba tausayi.

22 “Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki,

haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe.

A ranar fushin Ubangiji

ba mai tserewa ba wanda zai tsira;

maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu,

na kuma lura da su.”