Taron Jama’a na Biyu
1015 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Sa’an nan Sarki Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ɗana Solomon, wanda Allah ya zaɓa, matashi ne, kuma bai gogu ba. Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne. 2 Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim. 3 Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali, 4 talenti dubu uku na zinariya (zinariyar Ofir) da tacecciyar azurfa dubu bakwai; don adon bangon gine-ginen, 5 don aikin zinariya da kuma aikin azurfa, don kuma dukan aikin da gwanaye za su yi. Yanzu fa wa yake da niyya yă miƙa kansa a yau don Ubangiji?”
6 Sai shugabannin iyalai, shugabannin kabilan Isra’ila, manyan hafsoshin mayaƙa dubu-dubu da manyan hafsoshi mayaƙa ɗari-ɗari, da shugabannin lura da ayyukan sarki suka yi bayarwa da yardar rai. 7 Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah. 8 Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji. 9 Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai.
10 Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa,
“Yabo gare ka, ya Ubangiji,
Allah na mahaifinmu Isra’ila,
har abada abadin.
11 Girma da iko
da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji,
gama kome a sama da ƙasa naka ne.
Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji;
an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
12 Wadata da girma daga gare ka suke;
kai ne mai mulkin dukan abubuwa.
A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke
don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.
13 Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka,
muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.
14 “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne. 15 Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya. 16 Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne. 17 Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka. 18 Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya. 19 Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.”
Ta Solomon.
1 Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah,
ɗan sarki da adalcinka.
2 Zai shari’anta mutanenka da adalci,
marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.
3 Duwatsu za su kawo wadata ga mutane,
tuddai kuma su ba da amfani na adalci.
4 Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane
yă kuma cece ’ya’yan masu bukata;
zai murƙushe masu danniya.
5 Zai jimre muddin rana tana nan,
muddin akwai wata, har dukan zamanai.
6 Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka,
kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
7 A kwanakinsa adalai za su haɓaka
wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.
8 Zai yi mulki daga teku zuwa teku
kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.
9 Kabilun hamada za su rusuna a gabansa
abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
10 Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa
za su ba da gandu gare shi;
sarakunan Sheba da Seba
za su ba shi kyautai.
11 Dukan sarakuna za su rusuna masa
kuma dukan al’ummai za su bauta masa.
12 Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka,
marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
13 Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata
yă ceci masu bukata daga mutuwa.
14 Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici,
gama jininsu yake a gabansa.
15 Bari yă yi doguwar rayuwa!
Bari a ba shi zinariya daga Sheba.
Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa
su kuma albarkace shi dukan yini.
16 Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar;
bari yă cika bisan tuddai.
Bari ’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon;
bari yă bazu kamar ciyayi a gona.
17 Bari sunansa yă dawwama har abada;
bari yă ci gaba muddin rana tana nan.
Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa,
za su kuma ce da shi mai albarka.
18 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila,
wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.
19 Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada;
bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa.
Amin kuma Amin.
20 Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.
20 Sa’an nan Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ku yabi Ubangiji Allahnku.” Saboda haka suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu; suka rusuna suka kuma fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji da kuma sarki.
21 Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila. 22 Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana.
Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist. 23 Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya. 24 Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan ’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya.
25 Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu.