Umarnin Dawuda ga Solomon
1015 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce, 2 “Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji, 3 ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi. 4 Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’
5 “Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa. 6 Ka yi da shi gwargwadon hikimarka, amma kada ka bari yă gangara kabari da furfura cikin salama.
7 “Amma ka yi alheri ga ’ya’yan Barzillai mutumin Gileyad, ka sa su kasance a cikin waɗanda suke ci a teburinka. Sun goyi bayana sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka Absalom.
8 “Ka tuna, akwai kuma Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim, wanda ya yi ta yin mini muguwar la’ana a ranar da na tafi Mahanayim. Sa’ad da ya gangara ya same ni a Urdun, na rantse masa da sunan Ubangiji na ce, ‘Ba zan kashe ka da takobi ba.’ 9 Amma yanzu, kada ka ɗauke shi marar laifi. Kai mutum ne mai hikima; za ka san abin da za ka yi da shi. Ka kawo furfuransa zuwa kabari da jini.”
Kalmomin Ƙarshe na Dawuda
1 Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe.
“Abubuwan da Dawuda ɗan Yesse ya yi magana a kai,
abubuwan da mutumin da Mafi Ɗaukaka ya girmama.
Mutumin da Allah na Yaƙub ya zaɓa yă zama sarki,
wanda kuma yake mawaƙi waƙoƙin Isra’ila.
2 “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina;
maganarsa tana a harshena.
3 Allah na Isra’ila ya yi magana,
Dutsen Isra’ila ya ce mini,
‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci,
sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,
4 yana kama da hasken safiya
a safiya marar girgije,
kamar haske bayan ruwan sama
da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’
5 “Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba?
Ashe, Allah bai yi madawwamiyar yarjejjeniya da ni
shiryayye da ɗaurarre a kowane sashi ba?
Ba zai kawo ga cikar cetona
yă kuma biya duk bukatuna ba?
6 Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan
da ba a tattara da hannu.
7 Duk wanda ya taɓa ƙaya
yakan yi amfani da wani ƙarfe ne ko sandar māshi;
akan ƙone su inda suke a zube.”
Mutuwar Dawuda
26 Dawuda ɗan Yesse ya zama sarki a bisa dukan Isra’ila. 27 Ya yi mulki a bisa Isra’ila shekaru arba’in, shekaru bakwai a Hebron da kuma shekaru talatin da uku a Urushalima. 28 Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki.
29 Game da ayyukan mulkin Sarki Dawuda, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin Sama’ila mai duba, tarihin annabi Natan da kuma tarihin Gad mai duba, 30 tare da yadda mulkinsa da ikonsa da yanayin da suka kewaye shi da Isra’ila da kuma dukan masarautai na dukan sauran ƙasashe.
10 Sa’an nan Dawuda ya huta tare da kakanninsa. Sai aka binne shi a Birnin Dawuda. 11 Ya yi sarauta shekaru arba’in a bisa Isra’ila. Wato, shekaru bakwai a Hebron da kuma talatin da uku a Urushalima.