Zabura Daga Mulkin Dawuda, Kwanakinsu Ba Su Tabbata Ba (continued)

Zaburan da Dawuda ya rubuta bayan ya zama sarki, waɗanda ba a tabbatar da ranakun rubuta su da yanayin da aka rubuta su ba.

1015 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 120–122

Waƙar haurawa.

1 Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata,

ya kuwa amsa mini.

2 Ka cece ni, ya Ubangiji,

daga leɓuna masu ƙarya

da kuma daga harsuna masu yaudara.

3 Me zai yi maka,

me kuma ya fi,

ya kai harshe mai yaudara?

4 Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi,

tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.

5 Kaitona da nake zama a Meshek,

da nake zama a ciki tentunan Kedar!

6 Da daɗewa na zauna

a cikin waɗanda suke ƙin salama.

7 Ni mutum ne mai salama;

amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

Waƙar haurawa.

121:1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,

ta ina ne taimakona zai zo?

2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,

wanda ya kafa sama da ƙasa.

3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,

shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila

ba ya gyangyaɗi ko barci.

5 Ubangiji yana tsaronka,

Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;

6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba

balle wata da dare.

7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,

zai tsare ranka;

8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka

yanzu da har abada kuma.

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

122:1 Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni,

“Bari mu tafi gidan Ubangiji.”

2 Ƙafafunmu suna tsaye

a ƙofofinki, ya Urushalima.

3 An gina Urushalima kamar birnin

da aka yi a harhaɗe wuri guda.

4 A can ne kabilu suke haurawa,

kabilan Ubangiji,

don su yabi sunan Ubangiji

bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.

5 A can kursiyoyin shari’a yake tsaye,

kursiyoyin gidan Dawuda.

6 Ku yi addu’a don salamar Urushalima,

“Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

7 Bari salama ta kasance a katangarki

zaman lafiya kuma a fadodinki.”

8 Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina,

zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”

9 Saboda gidan Ubangiji Allahnmu,

zan nemi wadatarki.

Zabura 124

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1 Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba,

bari Isra’ila yă ce,

2 da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba

sa’ad da aka auka mana,

3 sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu,

ai, da sun haɗiye mu da rai;

4 da rigyawa ta kwashe mu,

da ambaliya ta rufe mu.

5 Da ruwa mai hauka

ya share mu ƙaf.

6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,

wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.

7 Mun tsira kamar tsuntsu

daga tarkon mai farauta;

an tsinke tarko,

muka kuwa tsira.

8 Taimakonmu yana a sunan Ubangiji,

Wanda ya yi sama da ƙasa.

Zabura 131

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1 Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji,

idanuna ba sa fariya;

ban dami kaina da manyan al’amura ba

ko abubuwan da suka sha ƙarfina.

2 Amma na haƙura na kuma kwantar da raina;

kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa,

kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.

3 Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji

yanzu da har abada kuma.

Zabura 133

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1 Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma

sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!

2 Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai,

yana gangarawa a gemu,

yana gangarawa a gemun Haruna,

har zuwa wuyan rigunansa.

3 Yana kamar raɓar Hermon

da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona.

Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa,

har ma rai na har abada.