Sashe na 11: Mulkin Yotam

Masarautar Yahuda

758 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Sarakuna 15:32

32 A shekara ta biyu ta mulkin Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila, Yotam ɗan Uzziya sarkin Yahuda ya fara mulki.

2 Tarihi 27:1–2

1 Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. 2 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda mahaifinsa Uzziya ya yi, sai dai bai kutsa cikin haikalin Ubangiji kamar mahaifinsa ba. Mutane kuwa, suka ci gaba da aikata ayyukan lalaci.

2 Sarakuna 15:35

35 Duk da haka, bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙona turare a can. Yotam ya sāke gina Ƙofar Bisa ta haikalin Ubangiji.

Mika 1–2

1 Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.

2 Ku ji, ya ku mutane duka,

ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki,

bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku,

daga haikalinsa mai tsarki.

3 Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa;

zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.

4 Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa,

kamar kaki a gaban wuta,

kwaruruka kuma za su ɓace,

kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.

5 Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub,

da kuma zunuban gidan Isra’ila ne.

Mene ne laifin Yaƙub?

Shin, ba Samariya ba ce?

Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda?

Shin, ba Urushalima ba ce?

6 “Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji,

wurin noman inabi.

Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari

in kuma bar harsashin gininta a bayyane.

7 Za a ragargaje dukan allolinta;

za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta;

zan lalatar da dukan gumakanta.

Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su,

ga karuwanci kuma za su koma.”

8 Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka;

zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara.

Zan yi kuka kamar dila,

in yi baƙin ciki kamar mujiya.

9 Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne;

ya bazu har Yahuda.

Ya ma kai bakin ƙofar mutanena,

har ma Urushalima da kanta.

10 Kada a faɗe shi a Gat;

kada ma a yi kuka.

A maimako haka, a yi birgima a cikin ƙura

a Bet-Leyafra.

11 Ku wuce tsirara da kuma kunya,

ku mazaunan Shafir.

Bet-Ezel tana makoki

domin babu wani daga Za’anan

da ya fito don yă taimaka.

12 Mazaunan Marot

sun ƙosa su ga alheri,

amma Ubangiji ya sauko da azaba,

har zuwa ƙofar Urushalima.

13 Ku da kuke zama a Lakish,

ku ɗaura wa dawakai kekunan yaƙi.

Gama ku kuka fara yin zunubi

a Sihiyona,

gama an sami laifofin Isra’ila

a cikinku.

14 Saboda haka za ku ba da kyautan bankwana

ga Moreshet Gat.

Garin Akzib zai zama abin yaudara

ga sarakunan Isra’ila.

15 Ku mazaunan Maresha

Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi.

Sarakunan Isra’ila

za su gudu zuwa Adullam.

16 Ku aske kanku ƙwal don makoki,

ku yi wa kanku ƙwalƙwal kamar ungulu.

Gama za a ja ’ya’yan da kuke farin ciki

a kai su bauta.

2:1 Taku ta ƙare, ku da kuke shirya makirci,

ku da kuke ƙulle-ƙullen mugunta a kan gadonku!

Da gari ya waye sai ku fita ku aikata mugunta

domin ikon aikatawa yana hannunku.

2 Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su,

ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace.

Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa,

har ku ƙwace masa gādonsa.

3 Saboda haka, Ubangiji ya ce,

“Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i,

yadda ba za ku iya ceton kanku ba.

Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba,

gama zai zama lokacin bala’i ne.

4 A wannan rana mutane za su yi muku ba’a

za su yi muku gwalo da wannan waƙar makoki,

‘An lalatar da mu sarai;

an rarraba mallakar mutanena.

Ya ɗauke shi daga gare ni!

Ya miƙa filayenmu ga maciyan amanarmu.’ ”

5 Saboda haka ba za ku kasance da wani a taron jama’ar Ubangiji

da zai raba ƙasar ta wurin jefa ƙuri’a ba.

6 “Kada ku yi annabci” in ji annabawansu.

“Kada ku yi annabci game da waɗannan abubuwa;

abin kunya ba zai same mu ba.”

7 Daidai ne a ce, ya gidan Yaƙub,

“Ruhun Ubangiji yana fushi ne?

Yana yin irin waɗannan abubuwa?”

“Ashe, maganata ba tă amfane

wanda ayyukansa suke daidai ba?

8 Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi

kamar magabci.

Kun tuɓe riga mai tsada

daga waɗanda suke wucewa ba tare da kun damu ba,

sai ka ce mutanen da suke komowa daga yaƙi.

9 Kun kori matan mutanena

daga gidajensu masu daɗi.

Kuka kawar da albarkata har abada

daga wurin ’ya’yansu.

10 Ku tafi, ku ba ni wuri!

Gama wannan ba wurin hutunku ba ne,

gama ya ƙazantu,

ya zama kangon da ya wuce gyara.

11 In maƙaryaci da mazambaci ya zo ya ce,

‘Zan yi muku annabci ku sami wadataccen ruwan inabi da barasa,’

zai dai zama annabin da ya dace da wannan mutane ne!

12 “Tabbatacce zan tattara ku duka, ya gidan Yaƙub;

zan tattara ku raguwar Isra’ila.

Zan kawo su wuri ɗaya kamar

tumaki a cikin garke,

kamar garke a wajen kiwonsa;

wurin zai cika da mutane.

13 Wanda ya fasa ƙofa ya buɗe, shi zai haura yă yi musu jagora,

za su fashe bangon su fita.

Sarkinsu zai wuce gabansu,

Ubangiji kuma zai kasance a gaba.”

2 Tarihi 27:3–9

3 Yotam ya sāke ginin Ƙofar Bisa na haikalin Ubangiji, ya kuma yi aiki sosai a katanga a tudun Ofel. 4 Ya gina garuruwa a tuddan Yahuda, ya giggina katanga da gine-gine masu tsawo a wuraren da suke a kurmi.

5 Yotam ya yi yaƙi da sarkin Ammonawa ya kuma ci su. A wannan shekara Ammonawa suka biya shi haraji talenti ɗari na azurfa, garwan alkama dubu goma da kuma garwa dubu goma na sha’ir. Ammonawa suka kawo masa wannan kuma a shekara ta biyu da ta uku.

6 Yotam ya ƙaru a iko saboda ya daidaita al’amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.

7 Sauran ayyuka a mulkin Yotam, haɗe da dukan yaƙe-yaƙensa da waɗansu abubuwan da ya yi, suna a rubuce a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. 8 Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. 9 Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

2 Sarakuna 15:37

37 (A kwanakin nan Ubangiji ya fara aikan Rezin sarkin Aram da Feka ɗan Remaliya, su yi gāba da Yahuda.)

2 Sarakuna 15:33–34

33 Ya zama sarki yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. 34 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa Uzziya ya yi.

2 Sarakuna 15:36

36 Game da sauran ayyukan mulkin Yotam da aikin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

2 Sarakuna 15:38

38 Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda, birnin mahaifinsa. Ahaz ɗansa kuma ya gāje shi.

Masarautar Isra’ila

Mulkin Feka

2 Sarakuna 15:27–29

27 A shekara ta hamsin da biyu ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Feka ɗan Remaliya ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya yi mulki shekara ashirin. 28 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai kauce wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta yi ba.

29 A zamanin Feka sarkin Isra’ila, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo ya kama Iyon, Abel-Bet-Ma’aka, Yanowa da Kedesh da kuma Hazor. Ya kame Gileyad da Galili, haɗe da dukan ƙasar Naftali, ya kuma kwashi mutanen zuwa Assuriya.