Sashe na 12: Mulkin Ahaz
Masarautar Yahuda
Halin Ahaz
742 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 A shekara ta goma sha bakwai ta mulkin Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda ya fara mulki. 2 Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba. 3 Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila har ya miƙa ɗansa hadaya a wuta, yana bin hanyoyin banƙyama na al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. 4 Ya miƙa hadaya, ya kuma ƙona turare a masujadan tudu, da kan tuddai, da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace.
Rezin da Feka Sun Mamaye Yahuda
5 Sai Rezin sarkin Aram, da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su kai wa Urushalima hari, suka kuma kewaye Ahaz, amma ba su iya shan ƙarfinsa ba.
1 Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.
2 Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.
3 Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki. 4 Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba. 5 Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa, 6 “Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.” 7 Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“ ‘Ba zai faru ba,
ba zai auku ba,
8 gama kan Aram shi ne Damaskus,
kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin.
Cikin shekaru sittin da biyar
za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.
9 Kan Efraim shi ne Samariya,
kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya.
In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba,
ba za ku dawwama ba.’ ”
10 Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce, 11 “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.”
12 Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”
13 Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure? 14 Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel. 15 In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa. 16 Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango. 17 Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”
18 A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya. 19 Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa.
20 A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku. 21 A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai. 22 Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma. 23 A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can. 24 Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar. 25 Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu.
8:1 Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz. 2 Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.”
3 Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz. 4 Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”
5 Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,
6 “Domin wannan jama’a ta ƙi
natsattsen ruwan rafin Shilowa
suka yi ta farin ciki a kan Rezin
ɗan Remaliya,
7 saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu
rigyawar ruwan Kogi,
wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa.
Zai cika dukan gaɓoɓinsa,
yă kuma malala har zuwa bakin kogi.
8 Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta,
yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa.
Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka,
Ya Immanuwel!”
9 Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro!
Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe.
Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro!
10 Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba;
ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba,
gama Allah yana tare da mu.
11 Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce,
12 “Kada ka kira wani abu makirci
game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci;
kada ji tsoron abin da suke tsoro,
kada kuma ka firgita game da shi.
13 Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki,
shi ne wanda za ka ji tsoro,
shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa,
14 zai kuwa kasance a wuri mai tsarki;
amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama
dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe
dutse kuma da zai sa su fāɗi.
Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama
tarko da raga.
15 Yawancinsu za su yi tuntuɓe;
za su fāɗi a kuwa ragargaza su,
za a sa musu tarko a kuma kama su.”
16 Ɗaura shaidar nan ta gargadi
ka kuma yimƙe umarnin Allah a cikin almajiraina.
17 Zan saurari Ubangiji,
wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yaƙub.
Zan dogara gare shi.
18 Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona.
19 Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai? 20 Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani. 21 Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu. 22 Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.