Rezin da Feka Sun Mamaye Yahuda (continued)

742 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 9:1–10:4

1 Duk da haka, babu sauran baƙin ciki ga waɗanda suke shan azaba. Dā ya ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zebulun da ƙasar Naftali, amma nan gaba zai girmama Galili na Al’ummai, ta hanyar teku wadda take ta Urdun.

2 Mutanen da suke tafiya cikin duhu

sun ga babban haske;

a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa

haske ya haskaka.

3 Ka fadada al’umma

ka kuma ƙara farin cikinsu;

suna farin ciki a gabanka

yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi,

kamar yadda mutane sukan yi farin ciki

sa’ad da suke raba ganima.

4 Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi,

kuka ji tsoro

nauyin da ya nawaita musu,

sandar da yake a kafaɗunsu,

sandar masu zaluncinsu.

5 Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi

da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini

zai kasance an ƙone shi

zai kuma zama abin hura wuta.

6 Gama a gare mu an haifa mana yaro,

a gare mu an ba da ɗa,

gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa.

Za a ce da shi

Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki

Uban Madawwami, Sarkin Salama.

7 Game da girmar gwamnatinsa da salama

babu iyaka.

Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa,

zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,

tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.

Ubangiji Maɗaukaki ne

ya yi niyyar aikata wannan duka.

8 Ubangiji ya aika da saƙon gāba da Yaƙub;

zai auka wa Isra’ila.

9 Dukan mutane za su san shi,

Efraim da mazaunan Samariya,

waɗanda suke magana da fariya

suna kuma ɗaga kai,

10 “Tubalai sun zube a ƙasa,

amma za mu sāke gina su da dutse;

an sassare itatuwan ɓaure,

amma za mu maya su da al’ul.”

11 Amma Ubangiji ya ƙarfafa maƙiyan Rezin gāba da su

ya kuma ingiza abokan gāba.

12 Arameyawa daga gabas da Filistiyawa daga yamma

sun cinye Isra’ila da buɗaɗɗen baki.

Duk da haka, fushinsa bai huce ba,

hannunsa har yanzu yana a miƙe.

13 Amma mutanen ba su juyo wurin wanda ya buge su ba,

balle su nemi Ubangiji Maɗaukaki.

14 Saboda haka Ubangiji zai yanke Isra’ila kai da wutsiya,

da reshen dabino da iwa a rana guda;

15 dattawa da manyan mutane su ne kai,

annabawa waɗanda suke koyar da ƙarairayi su ne wutsiya.

16 Waɗanda suke jagorar wannan mutane suna ɓad da su,

su ne waɗanda ake jagora aka sa suka kauce.

17 Saboda haka Ubangiji ba zai ji daɗin matasa ba,

ba kuwa zai ji tausayin marayu da gwauraye ba,

gama kowa marar sanin Allah ne da kuma mugu,

kowane baki yana faɗin mugayen maganganu.

Duk da haka, fushinsa bai huce ba,

hannunsa har yanzu yana a miƙe.

18 Tabbatacce mugunta tana ƙuna kamar wuta;

tana cin ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya,

ta sa wuta a jeji mai itatuwa masu yawa,

don yă yi murtuke hayaƙi har zuwa sama.

19 Ta wurin fushin Ubangiji Maɗaukaki

ƙasar za tă ci wuta

mutane kuma za su zama abin hura wutar,

babu wanda zai ji tausayin ɗan’uwansa.

20 A dama za su ci,

amma su ci gaba da jin yunwa;

a hagu za su ci,

amma ba za su ƙoshi ba.

Kowa zai mai da naman ’ya’yansa abinci.

21 Manasse zai mai da Efraim abinci, Efraim kuma yă cinye Manasse;

tare za su yi gāba da Yahuda.

Duk da haka, fushinsa bai huce ba,

hannunsa har yanzu yana a miƙe.

10:1 Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya,

waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya,

2 don su hana matalauta hakkinsu

su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena,

suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu

suna kuma yi wa marayu ƙwace.

3 Me za ku yi a ranan nan ta hukunci,

sa’ad da masifa ta zo daga nesa?

Ga wa za ku tafi don neman taimako?

Ina za ku bar dukiyarku?

4 Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammu

ko mutuwa cikin waɗanda aka kashe.

Duk da haka, fushinsa bai huce ba,

hannunsa har yanzu yana a miƙe.

Ishaya Ya Annabta Hallakar Damaskus da Ƙabilu Goma

Ishaya 17

1 Abin da Allah ya faɗa game da Damaskus.

“Duba, Damaskus ba za tă ƙara zama birni ba

amma za tă zama tsibin juji.

2 Za a watse a bar biranen Arower

a bar wa tumaki da shanu, waɗanda za su kwanta,

ba tare da wani wanda zai tsorata su ba.

3 Birni mai katanga za tă ɓace daga Efraim,

ikon sarauta kuma daga Damaskus;

raguwar Aram za tă zama

kamar darajar Isra’ila,”

in ji Ubangiji Maɗaukaki.

4 “A wannan rana ɗaukakar Yaƙub za tă ƙare;

kitsen jikinsa zai lalace.

5 Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye

ya kuma girbe hatsin da hannunsa

kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi

a Kwarin Refayim.

6 Duk da haka waɗansu kala za su ragu,

sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun,

aka bar ’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan,

ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai ’ya’ya,”

in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.

7 A wannan rana mutane za su nemi Mahaliccinsu

su kuma juye idanunsu ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

8 Ba za su dubi bagade ba,

waɗanda suke aikin hannuwansu,

ba za su kuma kula da ginshiƙan Ashera ba

da kuma bagadan turaren da yatsotsinsu suka yi.

9 A wannan rana biranensu masu ƙarfi, waɗanda suka bari saboda Isra’ilawa, za su zama kamar wuraren da aka ƙyale suka zama kufai a jeji. Za su kuma zama kango.

10 Kun manta da Allah Mai Cetonku;

ba ku tuna da Dutse, kagararku ba.

Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau

kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,

11 ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma,

da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure,

duk da haka girbin ba zai zama kome ba

a ranar cuta da zafin da ba ta da magani.

12 Kash, ga hayaniyar al’ummai masu yawa

suna hayaniya kamar rurin teku!

Kash, ga fushin mutane

suna ruri kamar rugugi kamar manyan ruwaye!

13 Ko da yake mutane suna ruri kamar sukuwar raƙuman ruwa,

sa’ad da ya tsawata musu za su gudu can da nisa,

aka kore su kamar yayinda iska ya hura a kan tuddai,

kamar tattake kuma a cikin guguwa.

14 Da yamma, sai razana ba tsammani!

Kafin safiya, duk sun ɓace!

Wannan ne rabon waɗanda suka washe mu,

rabon waɗanda suka yi mana ƙwace.