Feka Ya Yi Wa Yahuda Mummunar Ɓarna

741 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Tarihi 28:4–19

4 Ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a masujadan kan tudu, a bisa tuddai da kuma ƙarƙashin kowane itace mai inuwa.

5 Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya miƙa shi ga sarkin Aram. Arameyawa suka ci shi a yaƙi, suka kuma kwashe mutanensa da yawa a matsayin ’yan kurkuku, suka kawo Damaskus.

Ya kuma ba da shi ga sarkin Isra’ila, wanda ya jijji masa a yaƙi. 6 A rana ɗaya Feka ɗan Remaliya ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu ashirin a Yahuda, domin Yahuda sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu. 7 Zikri, wani jarumin Efraim, ya kashe Ma’asehiya ɗan sarki, Azrikam hafsa mai lura da fada, da kuma Elkana, mataimakin sarki. 8 Isra’ilawa suka kame kamammu daga ’yan’uwansu mata, ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata dubu ɗari biyu. Suka kuma kwashe ganima mai yawan gaske, waɗanda suka kwasa zuwa Samariya.

9 Amma wani annabin Ubangiji mai suna Oded yana a can, sai ya fito don yă sadu da mayaƙa sa’ad da suke komowa zuwa Samariya. Ya ce musu, “Domin Ubangiji Allah na kakanninku yana fushi da Yahuda, ya ba da su cikin hannunku. Sai kuka kashe su cikin fushin da ya kai sama. 10 Yanzu kuma kuna niyya ku mai da maza da matan Yahuda da Urushalima bayinku. Amma ku ɗin ba ku da laifin zunubi ga Ubangiji Allahnku ne? 11 To, ku saurare ni! Ku mai da ’yan’uwanku da kuka kama a matsayin ’yan kurkuku, gama fushin Ubangiji yana a kanku.”

12 Sai waɗansu shugabanni a Efraim, Azariya ɗan Yehohanan, Berekiya ɗan Meshillemot, Hezekiya ɗan Shallum da Amasa ɗan Hadlai, suka tasar wa waɗanda suke isowa daga yaƙi. 13 Suka ce, “Dole ku kawo waɗannan ’yan kurkukun a nan, ko kuwa za ku yi laifi a gaban Ubangiji. Kuna niyya ku ƙara ga zunubinmu da kuma laifinmu? Gama laifinmu ya riga ya yi yawa, kuma fushinsa mai tsanani yana a kan Isra’ila.”

14 Saboda haka sojoji suka ba da ’yan kurkukun da ganima a gaban hafsoshi da dukan taron. 15 Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin ’yan’uwansu a Yeriko, wato, Birnin Itatuwan Dabino, sa’an nan suka koma Samariya.

16 A lokacin nan Sarki Ahaz ya aika wurin sarkin Assuriya neman taimako. 17 Mutanen Edom sun sāke zuwa suka yaƙi Yahuda suka kuma kwashe ’yan kurkuku, 18 yayinda Filistiyawa suka kai hari wa garuruwa a gindin tuddai da kuma a Negeb na Yahuda. Suka kame su suka kuma zauna a Bet-Shemesh, Aiyalon da Gederot, haka ma Soko, Timna da Gimzo tare da ƙauyuka kewayensu. 19 Ubangiji ya ƙasƙantar da Yahuda saboda Ahaz sarkin Isra’ila, gama ya hadasa mugunta a Yahuda kuma ya kasance marar aminci ga Ubangiji.

Obadiya 1

1 Wahayin Obadiya.

Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce a kan Edom.

Mun ji saƙo daga wurin Ubangiji cewa,

An aiki jakada zuwa ga al’ummai yă faɗa musu cewa,

“Ku tashi, mu tafi mu yi yaƙi da ita.”

2 “Duba, zan maishe ki ƙarama a cikin al’ummai;

za a rena ki ƙwarai.

3 Fariyar zuciyarki ta yaudare ki,

ke da kike zama can bisa duwatsu

kika kuma yi gidanki a kan ƙwanƙoli,

ke da kike ce wa kanki,

‘Wa zai iya saukar da ni ƙasa?’

4 Ko da yake kina firiya kamar gaggafa

kin kuma yi sheƙarki a can cikin taurari,

daga can zan saukar da ke,”

in ji Ubangiji.

5 “In ɓarayi suka zo miki,

in kuma ’yan fashi suka shigo gidan da dare,

kash, bala’i zai jira ki

ba abin da suke so ne kawai za su sata ba?

In kuma masu tsinka ’ya’yan inabi suka zo miki,

ba sukan bar ’ya’yan inabi kaɗan ba?

6 Amma za a washe Isuwa ƙaƙaf,

a kuma yaye ɓoyayyiyar dukiyarsa!

7 Dukan waɗanda kike tarayya da su, za su kore ki zuwa iyaka;

abokanki kuma za su yaudare ki, su kuma sha ƙarfinki;

waɗanda suke cin abincinki, za su sa miki tarko,

amma ba za ki gane ba.

8 “A wannan rana,” in jin Ubangiji,

“zan hallaka masu hikimar Edom,

zan shafe mutane masu fahima a duwatsun Isuwa.

9 Jarumawanki, ya Teman, za su razana,

za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa.

10 Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub,

za ki sha kunya;

za a hallaka ki har abada.

11 A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido

yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki,

baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa

suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima,

kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.

12 Bai kamata ki rena ɗan’uwanki

a ranar masifarsa ba,

ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda

a ranar hallakarsu,

ko ki yi fariya sosai

a ranar wahalarsu.

13 Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena

a ranar bala’insu ba,

ko ki rena su a cikin masifarsu

a ranar bala’insu,

ko ki ƙwace dukiyarsu

a ranar bala’insu ba.

14 Bai kamata ki tsaya a mararraba

don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba,

ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu

a ranar wahalarsu ba.

15 “Ranar Ubangiji ta yi kusa

don dukan al’ummai.

Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku;

ayyukanku za su koma a kanku.

16 Kamar yadda kuka sha a kan tuduna mai tsarki,

haka dukan al’ummai za su yi ta sha,

za su sha, su kuma sha

su zama sai ka ce ba su taɓa kasancewa ba.

17 Amma a kan Dutsen Sihiyona za a sami ceto;

Dutsen zai zama mai tsarki,

gidan Yaƙub kuma

zai mallaki gādonsa.

18 Gidan Yaƙub zai zama kamar wuta,

gidan Yusuf kuma kamar harshen wuta;

gidan Isuwa zai zama kamar tattaka,

za a kuma sa masa wuta yă ƙone.

Babu wanda zai tsira

daga gidan Isuwa.”

Ni Ubangiji na faɗa.

19 Mutane daga Negeb za su mamaye

duwatsun Isuwa,

mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki

ƙasar Filistiyawa.

Za su mamaye filayen Efraim da Samariya,

Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad.

20 Wannan ƙungiyar Isra’ilawan da aka kwashe zuwa bauta da suke a Kan’ana

za su mallaki ƙasar har zuwa Zarefat;

waɗannan da aka kwashe zuwa bauta daga Urushalima da suke a Sefarad

za su mallaki garuruwan Negeb.

21 Masu kawo ceto za su haura zuwa Dutsen Sihiyona

don su yi mulkin duwatsun Isuwa.

Ubangiji ne zai yi mulki.

Ishaya 1:2–31

2 Ku kasa kunne, ya sammai! Ki saurara, ya duniya!

Gama Ubangiji ya yi magana,

“Na yi renon ’ya’ya, na kuma raya su,

amma sun tayar mini.

3 Saniya ta san maigidanta,

jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa,

amma Isra’ila ba su sani,

mutanena ba su gane ba.”

4 Kash, ya ke al’umma mai zunubi,

mutane cike da laifi,

tarin masu aikata mugunta,

’ya’yan da aka miƙa wa lalaci!

Sun yashe Ubangiji;

sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila

suka juya masa baya.

5 Me ya sa za a ƙara yin muku dūka?

Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa?

An yi wa dukan kanku rauni,

zuciyarku duk tana ciwo.

6 Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku

ba lafiya,

sai miyaku da ƙujewa

da manyan gyambuna,

ba a tsabtacce su ba ko a daure

ko shafa musu magani.

7 Ƙasarku ta zama kufai,

an ƙone biranenku da wuta;

baƙi suna ƙwace gonakinku

a idanunku,

ta zama kango kamar sa’ad da baƙi suka rushe ta.

8 An bar diyar Sihiyona

kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi,

kamar bukka a gonar kabewa,

kamar birnin da aka kewaye da yaƙi.

9 Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki

ya bar mana raguwar masu rai ba,

da mun zama kamar Sodom,

da mun zama kamar Gomorra.

10 Ku saurari maganar Ubangiji,

ku masu mulkin Sodom;

ku kasa kunne ga dokar Allahnmu,

ku mutanen Gomorra!

11 Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku,

mene ne suke a gare ni?”

Ina da isashen hadayun ƙonawa,

na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba;

ba na jin daɗin

jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.

12 Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana,

wa ya nemi wannan daga gare ku,

da kuke kai da kawowa a filayen gidana?

13 Ku daina kawo hadayu marasa amfani!

Turarenku abin ƙyama ne gare ni.

Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini,

ba zan iya jure wa mugun taronku ba.

14 Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku

na ƙi su.

Sun zama mini kaya;

na gaji da ɗaukansu.

15 Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a,

zan ɓoye fuskata daga gare ku;

ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa,

ba zan kasa kunne ba.

Hannuwanku sun cika da jini!

16 Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku.

Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana;

Ku daina aikata mugunta.

17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.

Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.

Ku ba wa marayu hakkinsu,

ku taimaki gwauruwa.

18 Ubangiji ya ce,

“Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,

Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,

za su zama fari kamar ƙanƙara;

ko da sun yi ja kamar mulufi,

za su zama kamar ulu.

19 In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya,

za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;

20 amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa,

za a kashe ku da takobi.”

Ni Ubangiji na faɗa.

21 Dubi yadda amintacciyar birni

ta zama karuwa!

Dā ta cika da yin gaskiya;

dā masu adalci a can suke zama,

amma yanzu sai masu kisankai kaɗai!

22 Azurfarki ta zama jebu,

an gauraye ruwan inabinki mafi kyau da ruwa.

23 Masu mulkinki ’yan tawaye ne,

abokan ɓarayi;

dukansu suna ƙaunar cin hanci

suna bin kyautai.

Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a;

ba sa taimakon gwauruwa.

24 Saboda haka Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,

Mai Iko nan na Isra’ila, ya furta,

“Kai, zan sami hutu daga maƙiyana

in kuma yi ramuwa a kan abokan gābana.

25 Zan juye hannuna a kanki;

zan wanke ke sarai

in fitar da dukan ƙazantarki.

26 Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can,

mashawartanki kamar yadda suke da fari.

Bayan haka za a ce da ke

Birnin Masu Adalci,

Amintacciyar Birni.”

27 Za a fanshi Sihiyona da adalci,

masu tubanta kuma da aikin gaskiya.

28 Amma za a karye ’yan tawaye da masu zunubi,

waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka.

29 “Za ku ji kunya saboda masujadan ƙarƙashin itatuwan oak

da kuka yi farin ciki;

za a kunyata ku saboda lambun

da kuka zaɓa.

30 Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye,

kamar lambu marar ruwa.

31 Mutum mai ƙarfi zai zama kamar rama,

aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta;

duka za su ƙone tare,

ba kuwa wanda zai kashe wutar.”