Ahaz Ya Ƙulla Ƙawance da Tiglat-Fileser

Ahaz ya ƙulla ƙawance da Tiglat-Fileser, sarkin Assuriya.

740 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Sarakuna 16:6–9

6 A wannan lokaci, Rezin sarkin Aram ya sāke ƙwato Elat wa Aram ta wurin korar Yahuda. Sa’an nan mutanen Edom suka mamaye Elat suna kuwa zaune a can har yau.

7 Ahaz ya aika a faɗa wa Tiglat-Fileser sarkin Assuriya cewa, “Ni abokin tarayyarka ne kuma mai dogara da kai. Ka haura ka cece ni daga hannun sarkin Aram da hannun sarkin Isra’ila waɗanda suke kawo mini hari.” 8 Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyar da suke a haikalin Ubangiji da suke kuma a ma’ajin fada ya aika wa sarkin Assuriya kyauta. 9 Sai sarkin Assuriya ya ji roƙonsa. Ya tashi ya fāɗa wa Damaskus da hari ya kuma kame ta. Ya kwashi mazaunanta zuwa Kir, ya kuma kashe Rezin.

Ishaya 28

1 Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim,

ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa,

da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,

ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!

2 Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi.

Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna,

kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa,

zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.

3 Za a tattaka wannan rawani,

girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.

4 Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa,

da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,

zai zama kamar ’ya’yan ɓaure, nunan fari,

da zarar wani ya gani ya kuma tsinka,

zai haɗiye shi.

5 A wannan rana Ubangiji Maɗaukaki

zai zama rawani mai daraja

kyakkyawan rawani

wa mutanensa da suka ragu.

6 Zai zama ruhun adalci

gare shi wanda yake zaune a kujerar shari’a,

wurin samun ƙarfi

ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofi.

7 Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi

suke jiri don sun sha barasa

Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa

sun kuma yi tatur da ruwan inabi;

suna jiri saboda sun sha barasa,

suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi,

suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.

8 Duk amai ya rufe teburori

kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.

9 “Wane ne yake so ya koyar?

Ga wa yake bayyana saƙonsa?

Ga yaran da aka yaye,

ga waɗanda ba a daɗe da yayewa ba ne?

10 Gama haka yake.

Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi,

mulki a kan mulki, mulki a kan mulki;

nan kaɗan, can kaɗan.”

11 To da kyau, da leɓunan baƙi da ku harsunan da ba sani ba

Allah zai yi magana da wannan mutane,

12 waɗanda zai ce,

“Wannan shi ne wurin hutu, bari waɗanda suka gaji su huta”;

da kuma, “Wannan shi ne wurin wartsakewa”

amma sun ƙi su saurara.

13 Saboda haka fa, maganar Ubangiji gare su za tă zama,

Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi,

mulki akan mulki, mulki a kan mulki;

nan kaɗan, can kaɗan,

domin su tafi su kuma fāɗi da baya,

su ji rauni a kuma kama su da tarko, a kai su zaman bauta.

14 Saboda haka ku saurari maganar Ubangiji, ku masu ba’a

ku da kuke mulkin wannan mutane a Urushalima.

15 Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa,

mun kuma yi yarjejjeniya da kabari.

Sa’ad da zafi ya ratsa,

ba zai taɓa mu ba,

gama mun mai da ƙarya mafakarmu

ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.”

16 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,

“Duba, na kafa dutse a Sihiyona,

dutsen da aka gwada,

dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe;

wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.

17 Zan mai da gaskiya igiyar gwaji

adalci kuma ɗan katakon gwajin ginin;

ƙanƙara za tă share mafakarku,

ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku.

18 Za a soke alkawarinku da mutuwa;

yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba.

Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa,

zai hallaka ku.

19 A duk sa’ad da ya zo;

ko da safiya, ko dare ko kuma da rana,

zai yi ta ratsawa yana kwasanku.”

Za ku zama kamar mutumin

da ya zama abin karin magana,

20 wanda ya yi ƙoƙari yă kwanta a gajeren gado,

yă kuma rufa da ɗan siririn bargo.

21 Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim,

zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyon

don yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba,

yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa.

22 Yanzu ku daina ba’arku,

in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi;

Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini

game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.

23 Ku saurara ku kuma ji muryata;

ku kasa kunne ku kuma ji abin da na faɗa.

24 Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne?

Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne?

25 Sa’ad da ya shirya wuri da kyau,

ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba?

Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa

sha’ir a kunyoyinsa,

tamba kuma a filinsa ba?

26 Allahnsa ya umarce shi

ya kuma koya masa hanyar da take daidai.

27 Ba a bugan kanumfari da ƙaton sanda

ko a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya;

akan buga kanumfari da siririn sanda

ɗaɗɗoya kuma da tsumagiya.

28 Dole a niƙa hatsi don a yi burodi;

saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba.

Ya san yadda zai sussuke alkamarsa,

ba tare da ya ɓata tsabarta ba.

29 Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne,

shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.

2 Tarihi 28:20–23

20 Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo wurinsa, sai ya wahalar da sarki Ahaz maimakon taimakonsa. 21 Ahaz ya ɗauki waɗansu abubuwa daga haikalin Ubangiji da kuma daga fadan sarki da kuma daga sarakuna, ya ba da su ga sarkin Assuriya, amma wannan bai taimake shi ba.

22 Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji. 23 Ya miƙa hadayu ga allolin Damaskus, waɗanda suka ci shi a yaƙi; gama ya yi tunani, “Da yake allolin sarakunan Aram sun taimake su, zan miƙa hadayu domin su taimake ni.” Amma suka zama sanadin fāɗuwarsa da kuma fāɗuwar dukan Isra’ila.

2 Sarakuna 16:10–18

10 Sa’an nan sarki Ahaz ya tafi Damaskus don yă sadu da Tiglat-Fileser sarkin Assuriya. Da ya kai can sai ya ga wani bagade a Damaskus, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayanin bagaden. 11 Saboda haka Uriya firist ya gina bagaden bisa ga tsarin da Sarki Ahaz ya aika masa daga Damaskus, ya kuma gama shi kafin Sarki Ahaz yă dawo. 12 Da sarki ya dawo daga Damaskus ya ga bagaden, sai ya tafi kusa da shi ya kuma miƙa hadaya a bisansa. 13 Ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa da ta hatsi, ya zuba hadayarsa ta sha, ya kuma yayyafa jinin hadayunsa ta zumunci a bisa bagaden. 14 Sai ya cire bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi a gaban haikalin wato, tsakanin ƙofar shiga haikalin Ubangiji da sabon bagaden. Ya ajiye shi a gefen arewa na sabon bagaden.

15 Sarkin Ahaz ya umarci Uriya cewa, “A kan babban sabon bagade, ka miƙa hadayar ƙonawa ta safe, da hadayar hatsi ta yamma, da hadayar sarki ta ƙonawa da hadayarsa ta hatsi, da hadaya ta dukan jama’ar ƙasar, tare da hadayan hatsinsu da kuma ta sha. Ka yayyafa jinin hadayun ƙonawa a kan bagade. Amma zan yi amfani da bagaden tagulla don neman bishewa.” 16 Uriya firist kuwa ya yi duk abin da Sarki Ahaz ya umarta.

17 Sarkin Ahaz ya kawar da katakon ya kuma ɗauke tasoshin daga mazauninsu da ake iya matsarwa. Ya ɗauke ƙaton kwano mai suna Teku daga kan bijiman tagullar da ya tallafe su ya ajiye a kan mazaunin dutse. 18 Ya kawar da rumfa Asabbacin da aka gina a haikalin, ya kuma kawar da mashigin sarki na waje da haikalin Ubangiji, duk dai don yă gamshi sarkin Assuriya.

2 Tarihi 28:24–25

24 Ahaz ya tattara kayayyaki daga haikalin Allah ya kwashe su. Ya kulle ƙofofin haikalin Ubangiji ya kakkafa bagadai a kowace kusurwa a titin Urushalima. 25 A kowane gari a Yahuda, ya gina masujadan kan tudu don ƙone hadayu ga waɗansu alloli, ya kuma tsokane Ubangiji Allah na kakanninsa ya yi fushi.

Hosiya 5

1 “Ku ji wannan, ku firistoci!

Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa!

Ku saurara, ya ku gidan sarauta!

Wannan hukunci yana a kanku,

kun zama tarko a Mizfa,

ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor.

2 ’Yan tawaye sun yi zurfi cikin kisan gilla.

Zan hore su duka.

3 Na san Efraim ƙaf;

Isra’ila ba a ɓoye take a gare ni ba.

Efraim, yanzu ka juya ka shiga karuwanci;

Isra’ila ta lalace.

4 “Ayyukansu ba su ba su dama

su koma ga Allahnsu ba.

Halin karuwanci yana cikin zuciyarsu;

ba su yarda da Ubangiji ba.

5 Girmankan Isra’ila yana ba da shaida a kansu;

Isra’ilawa, har ma Efraim, sun yi tuntuɓe a cikin zunubinsu;

Yahuda ma ya yi tuntuɓe tare da su.

6 Sa’ad da suka tafi tare da garkunan shanu, tumaki da awakinsu

don su nemi Ubangiji,

ba za su same shi ba;

ya janye kansa daga gare su.

7 Su marasa aminci ne ga Ubangiji;

suna haihuwar shegu.

Yanzu bukukkuwar Sabon Watansu

za su cinye su da gonakinsu.

8 “Amon kakaki a Gibeya,

ƙaho a Rama.

Ku yi kirarin yaƙi a Bet-Awen;

ku ja gaba, ya Benyamin.

9 Efraim za tă zama kango

a ranar hukunci.

A cikin kabilan Isra’ila

na yi shelar abin da yake tabbatacce.

10 Shugabannin Yahuda suna kamar waɗanda

suke matsar da duwatsun shaidar da aka sa a kan iyaka ne.

Zan zubo musu da fushina a kansu

kamar rigyawar ruwa.

11 An danne Efraim,

an murƙushe ta a shari’a

ta ƙudura ga bin gumaka.

12 Na zama kamar asu ga Efraim,

kamar ruɓa ga mutanen Yahuda.

13 “Sa’ad da Efraim ya ga ciwonsa,

Yahuda kuwa miyakunta,

sai Efraim ya juya ga Assuriya,

ya aika wurin babban sarki don neman taimako.

Amma bai iya warkar da kai ba,

bai iya warkar da miyakunka ba.

14 Gama zan zama kamar zaki ga Efraim,

kamar babban zaki ga Yahuda.

Zan yage su kucu-kucu in tafi;

zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su.

15 Sa’an nan zan koma wurina

sai sun yarda da laifinsu.

Za su kuma nemi fuskata;

cikin azabansu za su nace da nemana.”