Ahaz Ya Ƙulla Ƙawance da Tiglat-Fileser (continued)
Ahaz ya ƙulla ƙawance da Tiglat-Fileser, sarkin Assuriya.
740 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 “Ku zo, mu koma ga Ubangiji.
Ya yayyage mu kucu-kucu
amma zai warkar da mu;
ya ji mana ciwo
amma zai daure mana miyakunmu.
2 Bayan kwana biyu zai rayar da mu,
a rana ta uku zai tashe mu,
don mu rayu a gabansa.
3 Bari mu yarda da Ubangiji;
bari mu nace gaba don mu yarda da shi.
Muddin rana tana fitowa,
zai bayyana;
zai zo mana kamar ruwan bazara,
kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”
4 “Me zan yi da kai Efraim?
Me zan yi da kai Yahuda?
Ƙaunarku tana kamar hazon safiya,
kamar raɓar safiya da takan ɓace.
5 Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana,
na kashe ku da kalmomin bakina;
hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.
6 Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,
ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.
7 Kamar Adamu, sun tā da alkawari,
sun yi mini rashin aminci a can.
8 Gileyad birni ce ta mugayen mutane,
da tabon alamun jini.
9 Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum,
haka ƙungiyoyin firistoci suke;
suna kisa a hanya zuwa Shekem,
suna aikata laifofi bankunya.
10 Na ga wani abu mai bantsoro
a gidan Isra’ila.
A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci
Isra’ila kuma ta ƙazantu.
11 “Ku kuma, ya mutanen Yahuda,
na shirya muku ranar girbi.
“A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena,
Ahaz Ya Mutu; An Annabta Ƙarfin Hezekiya 726 kafin haihuwar Almasihu
Mutuwar Ahaz, da annabci game da ƙarfin Hezekiya.
26 Sauran ayyukan mulkinsa da dukan hanyoyinsa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila. 27 Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Urushalima, amma ba a sa shi a makabartan sarakunan Isra’ila ba. Sai Hezekiya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
28 Wannan abin da Allah ya yi magana ya zo ne a shekarar da Sarki Ahaz ya mutu.
29 Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa,
cewa sandar da ta buge ku ta karye;
daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso,
’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.
30 Mafi talauci na matalauta zai sami wurin kiwo,
mabukata kuma za su kwana lafiya.
Amma zan hallakar da saiwarka da matsananciyar yunwa;
za tă kashe naka da suka rage da rai.
31 Ki yi ihu, ya ke ƙofa! Yi kururuwa, ya ke birni!
Ku razana, dukanku Filistiyawa!
Ƙunshin hayaƙi yana tasowa daga arewa,
kuma babu matsorata a cikin sojojinsa.
32 Wace amsa ce za a bayar
wa jakadun wannan al’umma?
“Ubangiji ya kafa Sihiyona,
kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”
1 Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Ba kamar Dawuda kakansa ba, bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ba. 2 Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila ya kuma yi zubin gumaka domin a bauta wa Ba’al. 3 Ya ƙone hadayu a Kwarin Ben Hinnom, ya kuma miƙa ’ya’yansa maza a cikin wuta, yana bin hanyoyi banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.
19 Game da sauran ayyukan mulkin Ahaz, abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 20 Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi da su a Birnin Dawuda. Hezekiya ɗansa kuma ya gāje shi.
Masarautar Isra’ila 739 kafin haihuwar Almasihu
Mulkin Feka da Hosheya
30 Sa’an nan Hosheya ɗan Ela ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya. Ya fāɗa masa ya kuma kashe shi, sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki a shekara ta shirin ta mulkin Yotam ɗan Uzziya.
31 Game da sauran ayyukan mulkin Feka da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
1 A shekara ta goma sha biyu ta mulkin Ahaz sarkin Yahuda, Hosheya ɗan Ela ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki na shekara tara. 2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar na sarakunan Isra’ilan da suka riga shi ba.