Isra’ila Ba Tare da Sarki Ba Bayan Mutuwar Yerobowam na Biyu
776 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,
gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo
a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.
“Babu aminci, babu ƙauna,
babu yarda da Allah a cikin ƙasar.
2 Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa,
yin sata da zina;
sun wuce gona da iri,
kisankai a kan kisankai.
3 Saboda wannan ƙasar tana makoki,
kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace;
namun jeji da tsuntsayen sararin sama
da kuma kifin teku suna mutuwa.
4 “Amma kada wani mutum yă kawo tuhuma,
kada wani mutum yă zargi wani,
gama mutanenka suna kama da waɗanda
suke kawo tuhume-tuhume a kan firist ne.
5 Kuna tuntuɓe dare da rana,
annabawa ma suna tuntuɓe tare da ku.
Saboda haka zan hallaka mahaifiyarku,
6 mutanena suna hallaka saboda jahilci.
“Domin kun ƙi neman sani,
ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina;
domin kun ƙyale dokar Allahnku,
ni ma zan ƙyale ’ya’yanku.
7 Yawan ƙaruwar firistoci,
haka suke yawan zunubi a kaina;
sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya.
8 Suna ciyar da kansu a kan zunuban mutanena
suna kuma haɗamar muguntarsu.
9 Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke.
Zan hukunta dukansu saboda al’amuransu
in kuma sāka musu saboda ayyukansu.
10 “Za su ci amma ba za su ƙoshi ba;
za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba,
gama sun rabu da Ubangiji
don su ba da kansu 11 ga karuwanci,
ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,
waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.
12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace
suka kuwa sami amsa daga sanda.
Halin karuwanci yakan ɓad da su;
sun yi rashin aminci ga Allahnsu.
13 Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu
suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai,
a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri,
inda inuwa take da daɗi.
Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci
surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
14 “Ba zan hukunta ’ya’yanku mata
sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba,
balle surukanku mata,
sa’ad da suka yi zina,
gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai
suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada,
mutane marasa ganewa za su lalace!
15 “Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila,
kada Yahuda ya yi laifi.
“Kada ku tafi Gilgal;
kada ku haura zuwa Bet-Awen.
Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’
16 Isra’ilawa masu taurinkai ne,
kamar karsana mai taurinkai.
Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu
kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?
17 Efraim ya haɗa kai da gumaka;
ku ƙyale shi kurum!
18 Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare,
sai suka ci gaba da karuwancinsu;
masu mulkinsu suna ƙaunar abin kunya.
19 Guguwa za tă share su,
hadayunsu kuma za su jawo musu abin kunya.
Mulkin Zakariya 773 kafin haihuwar Almasihu
8 A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Zakariya ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki wata shida. 9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi. Bai bar aikata zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi ba.
10 Sai Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla wa Zakariya maƙarƙashiya. Ya tasam masa a gaban jama’a, ya kashe shi, ya kuma gāje shi. 11 Game da sauran ayyukan mulkin Zakariya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. 12 Ta haka maganar Ubangiji da ya yi wa Yehu ta cika, wadda ya ce, “Zuriyarka za tă zauna a kursiyin Isra’ila har tsara ta huɗu.”
Mulkin Shallum 772 kafin haihuwar Almasihu
13 Shallum ɗan Yabesh ya zama sarki a shekara ta talatin da tara ta mulkin Uzziya sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki na wata ɗaya a Samariya. 14 Sa’an nan Menahem ɗan Gadi ya gangara daga Tirza ya haura zuwa Samariya. Ya tasam wa Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya kuma gāje shi.
15 Game da sauran ayyukan mulkin Shallum, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
Mulkin Menahem
16 A lokacin nan sai Menahem ya taso daga Tirza, ya kai wa Tifsa hari da kowa wanda yake a birnin da kewayenta, don sun ƙi su buɗe ƙofofinsu. Ya kori Tifsa daga aiki, ya kuma tsattsaga cikin dukan mata masu juna biyu.
17 A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Menahem ɗan Gadi ya zama sarkin Isra’ila, ya yi mulki a Samariya shekara goma. 18 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A duk tsawon mulkinsa, bai rabu da zunuban da Yerobowam ɗan Nebat ya sa Isra’ila suka aikata ba.
19 Sai Ful sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar hari, Menahem kuwa ya ba shi talenti dubu na azurfa don yă sami goyon bayansa, yă kuma ƙarfafa kahuwa mulkin. 20 Menahem ya tara kuɗin ne ta hanyar haraji a Isra’ila inda ya sa kowane attajiri ya ba da shekel hamsin don a ba sarkin Assuriya. Sa’an nan sarkin Assuriya ya janye, bai ƙara kasance a ƙasar ba.
21 Game da sauran ayyukan mulkin Menahem, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. 22 Menahem ya huta tare da kakanninsa. Fekahiya ɗansa kuma ya gāje shi.
Mulkin Fekahiya 768 kafin haihuwar Almasihu
23 A shekara ta hamsin ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Fekahiya ɗan Menahem ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekara biyu. 24 Fekahiya ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat wanda ya sa Isra’ila ya aikata ba. 25 Ɗaya daga cikin manyan fadawansa, Feka ɗan Remaliya, ya ƙulla masa maƙarƙashiya. Ɗauke da mutanen Gileyad hamsin, ya kashe Fekahiya tare da Argob da kuma Ariye a fadan sarki a Samariya. Ta haka Feka ya kashe Fekahiya ya kuma gāje shi.
26 Game da sauran ayyukan mulkin Fekahiya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.