Mutuwar Yerobowam na Biyu
784 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
28 Game da sauran ayyukan mulkin Yerobowam, da dukan abin da ya yi, da yaƙe-yaƙen da ya yi, haɗe da sāke ƙwato wa Isra’ila Damaskus da Hamat waɗanda suke a hannun Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
10 Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba. 11 Gama ga abin da Amos yake cewa,
“ ‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi,
kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta,
nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
12 Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can. 13 Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.”
14 Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul. 15 Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’ 16 Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce,
“ ‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila,
kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’
17 “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce,
“ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni,
kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata.
Za a auna ƙasarka a kuma raba ta,
kai kuma za ka mutu a ƙasar arna.
Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta,
nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
8:1 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji ya nuna mini kwandon nunannun ’ya’yan itace. 2 Ya yi tambaya ya ce, “Me ka gani Amos?”
Sai na amsa na ce, “Kwandon nunannun ’ya’yan itace.”
Sai Ubangiji ya ce mini, “Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba.
3 “A ranan nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Waƙoƙin a haikali za su koma makoki. Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!”
4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata
kuka kori matalautan ƙasar.
5 Kuna cewa,
“Yaushe Sabon Wata zai wuce
don mu sayar da hatsi,
Asabbaci ta wuce,
don mu sayar da alkama?”
Mu yi awo da ma’aunin zalunci
mu ƙara kuɗin kaya
mu kuma cutar da mai saya,
6 mu sayi matalauta da azurfa
masu bukata kuma da takalmi,
mu sayar da alkamar haɗe da yayi.
7 Ubangiji ya rantse da Girman Yaƙub, “Ba zan taɓa mantawa da duk wani abin da suka yi ba.
8 “Shin, ƙasar ba za tă yi rawan jiki saboda wannan ba,
kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba?
Ƙasar duka za tă hau ta sauka kamar Nilu;
za a dama ta sa’an nan ta nutse
kamar kogin Masar.
9 “A wannan rana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka,
“Zan sa rana ta fāɗi da tsakar rana
in kuma duhunta duniya da rana tsaka.
10 Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki
kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka.
Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki
za ku kuma aske kawunanku.
Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi
kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci.
11 “Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka,
“sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar,
ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba,
sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.
12 Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku
suna yawo daga arewa zuwa kudu,
suna neman maganar Ubangiji,
amma ba za su samu ba.
13 “A wannan rana
“kyawawan ’yan mata da kuma samari masu ji da ƙarfi
za su suma don ƙishirwa.
14 Waɗanda suka yi rantsuwa da abin kunya na Samariya,
ko kuma su ce, ‘Muddin allahnku yana a raye, ya Dan,’
ko kuwa, ‘Muddin allahn Beyersheba yana a raye,’
za su fāɗi,
ba kuwa za su ƙara tashi ba.”
9:1 Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce,
“Bugi kan ginshiƙan
don madogaran ƙofa su girgiza.
Saukar da su a kan dukan mutane;
waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi.
Ba mutum guda da zai tsere,
babu wani da zai tsira.
2 Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari,
daga can hannuna zai fitar da su.
Ko da sun hau can sama
daga can zan sauko da su.
3 Ko da sun ɓuya a bisa Karmel,
a can zan farauce su in cafko.
Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku,
a can zan umarci maciji yă sare su.
4 Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta,
a can zan umarci takobi yă kashe su.
“Zan sa musu ido
don mugunta ba don alheri ba.”
5 Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,
shi da yakan taɓa ƙasa sai ta narke,
kuma dukan mazauna cikinta suna makoki,
ƙasar gaba ɗaya takan hau ta kuma sauka kamar Nilu,
sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar,
6 shi da ya gina kyakkyawar fadarsa a cikin sammai
ya kuma kafa harsashenta a duniya,
shi da yakan kira ruwan teku
yă kuma kwarara su a bisa duniya,
Ubangiji ne sunansa.
7 “Ku ba Isra’ilawa ba ne,
daidai gare ni kamar yadda Kushawa suke?”
In ji Ubangiji.
“Ban fito da Isra’ila daga Masar ba,
Filistiyawa kuma daga Kaftor
Arameyawa kuma daga Kir ba?
8 “Tabbatacce idanun Ubangiji Mai Iko Duka
suna a kan mulkin nan mai zunubi.
Zan hallaka shi
daga fuskar duniya,
duk da haka ba zan hallaka
gidan Yaƙub ƙaƙaf ba,”
in ji Ubangiji.
9 “Gama zan ba da umarni,
zan kuma tankaɗe gidan Isra’ila
a cikin dukan ƙasashe
kamar yadda ake tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi
kuma ko ƙwaya ɗaya ba za tă fāɗi a ƙasa ba.
10 Dukan masu zunubi a cikin mutanena
za su mutu ta wurin takobi,
wato, su masu cewa,
‘Masifa ba za tă fāɗo ko ta same mu ba.’
11 “A wannan rana zan maido
da tentin Dawuda da ya fāɗi.
Zan gyaggyara wuraren da suka yayyage,
in kuma maido da kufansa
in gina shi kamar yadda yake a dā,
12 domin su mallaki raguwar Edom
da duk al’ummai da suke amsa sunana,”
in ji Ubangiji shi wanda zai yi waɗannan abubuwa.
13 “Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji,
“sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi
mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi.
Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu
yă kuma kwararo daga tuddai.
14 Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta mutanena Isra’ila.
“Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu.
Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu;
za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu.
15 Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu,
ba kuwa za a ƙara tumɓuke su
daga ƙasar da na ba su ba,”
in ji Ubangiji Allahnku.
29 Yerobowam ya huta da kakanninsa, sarakunan Isra’ila. Zakariya ɗansa kuwa ya gāje shi.