Wautar Bautar Gumaka da Juyowar Al’ummai ga Allah

710 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 44–45

1 “Amma yanzu ka saurara, ya Yaƙub, bawana,

Isra’ila, wanda zaɓa.

2 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

shi wanda ya yi ka, wanda ya siffanta ka a cikin mahaifa,

wanda kuma zai taimake ka.

Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub, bawana,

Yeshurun, wanda na zaɓa.

3 Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa,

rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa;

zan ba da Ruhuna ga ’ya’yanka,

albarkata kuma ga zuriyarka.

4 Za su tsiro kamar ciyawa a wuriyar ruwa,

kamar kurmi kusa da rafuffuka masu gudu.

5 Wani zai ce, ‘Ni na Ubangiji ne’;

wani kuma zai kira kansa da sunan Yaƙub;

har yanzu wani zai rubuta a hannunsa, ‘Na Ubangiji,’

ya kuma ɗauki sunan Isra’ila.

6 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,

Sarki da kuma Mai Fansar Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki.

Ni ne farko ni ne kuma ƙarshe;

in ban da ni babu wani Allah.

7 Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji.

Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana

mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā,

mene ne kuma bai riga ya faru ba,

I, bari yă faɗa abin da zai zo.

8 Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro.

Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba?

Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni?

A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.”

9 Duk masu yin gumaka ba kome ba ne,

da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne.

Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne;

jahilai ne, marasa kunya.

10 Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki,

waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?

11 Shi da irinsa za su sha kunya;

masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum.

Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu;

za su firgita su kuma sha mummunan kunya.

12 Maƙeri yakan ɗauki kayan aiki

ya yi aiki da shi a cikin garwashi;

ya ƙera gunki da guduma,

ya gyara shi da hannuwansa masu ƙarfi.

Yakan ji yunwa ya kuma rasa ƙarfi;

yakan sha ruwa ya kuma ji gajiya.

13 Kafinta yakan gwada katako

yă kuma zāna siffar da alli;

yă goge shi da kayan aiki

yă kuma zāna shi da alƙalami.

Yă siffanta shi a kamannin mutum,

mutum cikin dukan darajarsa,

don yă ajiye shi a cikin masujada.

14 Yakan ka da itacen saifires, ko kuwa ya ɗauki saifires ko oak.

Yă bar shi yă yi girma a cikin itatuwan kurmi,

ko yă shuka itacen fir, ruwan sama kuma yă sa yă yi girma.

15 Abin hura wutar mutum ne;

yakan ɗebi waɗansu yă hura wuta don yă ji ɗumi,

ya hura wuta yă gasa burodi.

Amma yakan ƙera zinariya yă kuma yi masa sujada;

yakan yi gunki sa’an nan yă rusuna masa.

16 Rabin katakon yakan ƙone a wuta;

a kansa yakan dafa abincinsa,

yă gasa namansa yă kuma ci sai ya ƙoshi.

Yakan ji ɗumi yă kuma ce,

“Aha! Na ji ɗumi; na gan wutar.”

17 Da sauran itacen yakan yi allah, gunkinsa;

yă rusuna masa yă kuma yi sujada.

Yakan yi masa addu’a yă ce,

“Ka cece ni; kai ne allahna.”

18 Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba;

an rufe idanunsu don kada su gani,

tunaninsu kuma a rufe don kada su fahimta.

19 Ba wanda yakan dakata ya yi tunani,

ba wanda yake da sani ko fahimi ya ce,

“Da rabinsa na yi amfani da shi don hura wuta;

na ma gasa burodi a kan garwashinsa,

na gasa nama na kuma ci.

Ya kamata in yi abin ƙyama daga abin da ya rage?

Ya kamata in rusuna wa guntun katako?”

20 Yana cin toka, zuciyar da ta ruɗe tana ɓad da shi;

ba zai iya cece kansa ba, ko ya ce,

“Wannan abin da yake hannun dama na ba ƙarya ba ne?”

21 “Tuna da waɗannan abubuwa, ya Yaƙub,

gama kai bawana ne, ya Isra’ila.

Na yi ka, kai bawana ne;

Ya Isra’ila, ba zan manta da kai ba.

22 Na shafe laifofinka kamar girgije,

zunubanka kamar hazon safe.

Ka komo wurina,

gama na kuɓutar da kai.”

23 Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan;

ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi.

Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu,

ku jeji da dukan itatuwanku,

gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub,

ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.

24 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,

Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa.

“Ni ne Ubangiji,

wanda ya yi dukan abubuwa,

wanda ya shimfiɗa sammai

ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,

25 wanda ya sassāke alamun annabawan ƙarya

ya masu duba suka zama wawaye,

wanda ya tumɓuke koyon masu hikima

ya mai da shi banza,

26 wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa

ya kuma cika annabce-annabcen ’yan aikansa,

“wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’

game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’

27 wanda ya ce wa zurfin ruwaye, ‘Ku bushe,

zan kuma busar da rafuffukanku,’

28 wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina

zan kuma cika dukan abin da na gan dama;

zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,”

game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’

45:1 “Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa,

ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi

don yă ci al’ummai a gabansa

ya kuma tuɓe makaman sarakuna,

don yă buɗe ƙofofi a gabansa

don kada a kulle ƙofofi.

2 Zan sha gabanka

in baje duwatsu;

zan farfashe ƙofofin tagulla

in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.

3 Zan ba ka dukiyar duhu,

arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare,

saboda ka san cewa ni ne Ubangiji,

Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.

4 Saboda sunan Yaƙub bawana,

Isra’ila zaɓaɓɓena,

na kira ka da suna

na ba ka matsayin bangirma,

ko da yake ba ka san ni ba.

5 Ni ne Ubangiji, kuma babu wani;

in ban da ni babu wani Allah.

Zan ƙarfafa ka,

ko da yake ba ka san ni ba,

6 saboda daga fitowar rana

har zuwa fāɗuwarta

mutane za su san cewa babu wani in ban da ni.

Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.

7 Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu,

ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i;

ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.

8 “Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama;

bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci.

Bari ƙasa ta buɗe,

bari ceto ya tsiro,

bari adalci ya yi girma tare da shi;

ni, Ubangijine, na sa ya faru.

9 “Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka,

da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa.

Yumɓu ya iya ce wa magini,

‘Me kake yi?’

Aikinka na iya cewa,

‘Ba shi da hannuwa’?

10 Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa,

‘Me ka manta?’

Ko kuwa ga mahaifiyarsa,

‘Me kin haifa?’

11 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,

Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa.

Game da abubuwan da ke zuwa,

kun tambaye ni game da ’ya’yana,

ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?

12 Ai, ni ne wanda ya yi duniya

na kuma halicci mutum a kanta.

Hannuwana ne sun miƙe sammai;

na umarci rundunar sararin sama.

13 Zan tā da Sairus cikin adalcina.

Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe.

Zai sāke gina birnina

ya kuma ’yantar da mutanena masu bautar talala,

amma ba don wata haya ko lada ba,

in ji Ubangiji Maɗaukaki.”

14 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Kayayyakin Masar da hajar Kush,

da waɗannan dogayen Sabenawa,

za su ƙetaro zuwa wurinku

za su kuma zama naku;

za su bi bayanku,

suna zuwa cikin sarƙoƙi.

Za su rusuna a gabanku

su roƙe ku, suna cewa,

‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani;

babu wani allah.’ ”

15 Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka,

Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila.

16 Dukan masu yin gumaka za su sha kunya;

za su fita da kunya gaba ɗaya.

17 Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila

da madawwamin ceto;

ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba,

har abada.

18 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa,

shi da ya halicci sammai,

shi ne Allah;

shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya,

ya kafa ta;

bai halicce ta don ta zama ba kome ba,

amma ya yi ta don a zauna a ciki,

ya ce,

“Ni ne Ubangiji,

kuma babu wani.

19 Ban yi magana asirce ba,

daga wani wuri a ƙasar duhu ba;

ban faɗa wa zuriyar Yaƙub,

‘Ku neme ni a banza ba.’

Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi;

na furta abin da yake daidai.

20 “Ku tattaru ku zo;

ku taru, ku masu gudun hijira daga al’ummai.

Masu jahilci ne waɗanda suke ɗaukan gumakan katakai suna yawo,

waɗanda suke addu’a ga allolin da ba za su cece su ba.

21 Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi,

bari su yi shawara tare.

Wa ya faɗa wannan tuntuni,

wa ya yi shelar sa a kwanakin dā?

Ba ni ba ne, Ubangiji?

Kuma babu Allah in ban da ni,

Allah mai adalci da kuma Mai Ceto;

babu wani sai ni.

22 “Ku juyo gare ni ku sami ceto,

dukanku iyakokin duniya;

gama ni ne Allah,

kuma babu wani.

23 Da kaina na rantse,

bakina ya furta cikin dukan mutunci

kalmar da ba za a janye ba.

A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa;

ta wurina kowane harshe zai rantse.

24 Za su yi zance game da ni su ce, ‘A cikin Ubangiji kaɗai

akwai adalci da kuma ƙarfafawa.’ ”

Duk wanda ya yi fushi da shi

zai zo wurinsa ya kuma sha kunya.

25 Amma a cikin Ubangiji dukan zuriyar Isra’ila

za su sami adalci za su kuwa yi yabo.