An Annabta Zuwan Kiristi

Annabci game da zuwan Kiristi da kuma maido da Yahudawa.

710 zuwa 699 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 42–43

1 “Ga bawana, wanda na ɗaukaka,

zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi;

Zan sa Ruhuna a cikinsa

zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.

2 Ba zai yi ihu ko ya tā da murya,

ko ya daga muryarsa a tituna ba.

3 Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba,

ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba.

Cikin aminci zai kawo adalci;

4 ba zai kāsa ko ya karai ba

sai ya kafa adalci a duniya.

Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”

5 Ga abin da Allah Ubangiji ya ce,

shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su,

wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta,

wanda ya ba wa mutanenta numfashi,

da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.

6 “Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci;

zan riƙe hannunka.

Zan kiyaye ka in kuma sa ka

zama alkawari ga mutane

haske kuma ga Al’ummai,

7 don ka buɗe idanun makafi

ka ’yantar da kamammu daga kurkuku

kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.

8 “Ni ne Ubangiji; sunana ke nan!

Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka.

9 Duba, abubuwan da sun tabbata,

sababbin abubuwa kuwa nake furtawa;

kafin ma su soma faruwa

na sanar da su gare ku.”

10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,

ku yi yabonsa daga iyakar duniya,

ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,

ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.

11 Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu;

bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki.

Bari mutanen Sela su rera don farin ciki;

bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.

12 Bari su ɗaukaka Ubangiji

su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.

13 Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi,

kamar jarumi zai yi himma;

da ihu zai tā da kirarin yaƙi

zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa.

14 “Na daɗe ina shiru,

na yi shiru na kuma ƙame kaina.

Amma yanzu, kamar mace mai naƙuda,

na yi ƙara, ina nishi ina kuma haki.

15 Zan lalatar da duwatsu da tuddai

in busar da dukan itatuwansu;

zan mai da koguna su zama tsibirai

in kuma busar da tafkuna.

16 Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba,

a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su;

zan mai da duhu ya zama haske a gabansu

in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul.

Abubuwan da zan yi ke nan;

ba zan yashe su ba.

17 Amma waɗanda suka dogara ga gumaka,

waɗanda suke ce wa siffofi, ‘Ku ne allolinmu,’

za a mai da su baya da kunya.

18 “Ka ji, kai kurma;

duba, kai makaho, ka kuma gani!

19 Wane ne makaho in ba bawana ba,

da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba?

Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni,

makaho kamar bawan Ubangiji?

20 Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba;

kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.”

21 Yakan gamsar da Ubangiji

saboda adalcinsa

ya sa dokarsa ta zama mai girma da kuma mai ɗaukaka.

22 Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima,

an yi wa dukansu tarko a cikin rammuka

ko kuma an ɓoye su cikin kurkuku.

Sun zama ganima,

babu wani da zai kuɓutar da su;

an mai da su ganima,

ba wanda zai ce, “Mayar da su.”

23 Wane ne a cikinku zai saurari wannan

ko ya kasa kunne sosai a cikin kwanaki masu zuwa?

24 Wa ya ba da Yaƙub don yă zama ganima

Isra’ila kuma ga masu kwasar ganima?

Ba Ubangiji ba ne,

wanda kuka yi wa zunubi?

Gama ba su bi hanyoyinsa ba;

ba su yi biyayya da dokarsa ba.

25 Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa,

yaƙi mai tsanani.

Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba;

ya cinye su, amma ba su koyi kome ba.

43:1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,

shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,

shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,

“Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;

na kira ka da suna; kai nawa ne.

2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,

zan kasance tare da ku;

sa’ad da kuka bi ta koguna,

ba za su kwashe ku ba.

Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,

ba za tă ƙone ku ba;

harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.

3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,

Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;

na bayar da Masar don fansa,

Kush da Seba a maimakonku.

4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,

saboda kuma ina ƙaunarku,

zan ba da mutane a maimakonku,

al’umma kuma domin ranku.

5 Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;

zan kawo yaranku daga gabas

in kuma tattara ku daga yamma.

6 Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’

Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’

Kawo ’ya’yana maza daga nesa

’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,

7 kowa da ake kira da sunana,

wanda aka halitta saboda ɗaukakata,

wanda na siffanta na kuma yi.”

8 Jagoranci waɗanda suke da idanu amma suke makafi,

waɗanda suke da kunnuwa amma suke kurame.

9 Dukan al’ummai su taru

mutane kuma su tattaru.

Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan

ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru?

Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai,

don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.”

10 “Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji,

“bawana kuma wanda na zaɓa,

saboda ka sani ka kuma gaskata ni

ka kuma fahimci cewa ni ne shi.

Kafin ni babu allahn da aka siffanta,

ba kuwa za a yi wani a bayana ba.

11 Ni kaɗai, ni ne Ubangiji,

kuma in ban da ni babu wani mai ceto.

12 Na bayyana na ceci na kuma furta,

Ni ne, ba wani baƙon allah a cikinku.

Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “cewa ni ne Allah.

13 I, kuma tun fil azal ni ne shi.

Babu wani da zai amshi daga hannuna.

Sa’ad da na aikata, wa zai iya sauyawa?”

14 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila,

“Saboda ku zan aika Babilon

in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira,

a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su.

15 Ni ne Ubangiji, Mai Tsarkin nan,

Mahaliccin Isra’ila, Sarkinku.”

16 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

shi da ya yi hanya ta cikin teku,

hanya ta cikin manyan ruwaye,

17 wanda ya ja kekunan yaƙi da dawakai,

mayaƙa da kuma ƙarin mayaƙa tare

ya kwantar da su a can, ba kuwa za su ƙara tashi ba,

ya kashe hayaƙi daga lagwani,

18 “Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru;

kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce.

19 Duba, ina yi abu sabo!

Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba?

Ina yin hanya a cikin hamada

rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.

20 Namun jeji suna girmama ni,

diloli da mujiyoyi ma haka,

domin na tanada musu ruwa a hamada

da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa,

don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna,

21 mutanen da na yi saboda kaina

don su furta yabona.

22 “Duk da haka ba ku kira bisa sunana ba, ya Yaƙub,

ba ku gajiyar da kanku saboda ni ba, ya Isra’ila.

23 Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba,

balle ku girmama ni da hadayunku.

Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba

balle in gajiyar da ku da bukatar turare.

24 Ba ku saya wani turaren kalamus domina ba

ko ku gamshe ni da kitsen hadayunku.

Amma kun nawaita ni da zunubanku

kuka kuma gajiyar da ni da laifofinku.

25 “Ni kaɗai ne na shafe

laifofinku, saboda sunana,

ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba.

26 Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce,

bari mu yi muhawwara wannan batu tare;

ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.

27 Mahaifinku na farko ya yi zunubi;

masu magana a madadinku suka yi mini tayarwa.

28 Saboda haka zan kunyata manyan baƙi na haikalinku,

zan tura Yaƙub ga hallaka

Isra’ila kuwa yă zama abin dariya.