An Annabta Zaman Bauta da Halakar Babilon

Annabci game da zaman bauta a Babilon da kuma halakar Babilon.

710 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 46–47

1 Bel ya rusuna, Nebo ya durƙusa ƙasa;

ana ɗaukan gumakansu a kan dabbobi ne.

Siffofin da ake yawo da su nawaya ne,

kayan nauyi masu gajiyarwa.

2 Sun durƙusa suka kuma rusuna tare;

ba su iya kuɓutar da nauyin kaya

su kansu sukan tafi bauta.

3 “Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub,

dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila,

ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku,

na kuma riƙe ku tun haihuwarku.

4 Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura

ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.

Na yi ku zan kuma riƙe ku;

zan lura da ku

in kuma kuɓutar da ku.

5 “Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni?

Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni?

6 Waɗansu sukan zubar da zinariya daga jaka

su kuma auna azurfa a ma’auni;

sukan yi haya maƙerin zinariya don yă ƙera allah,

su kuma rusuna su yi masa sujada.

7 Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi;

sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya.

Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba.

Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa;

ba zai iya cetonsa daga wahala ba.

8 “Ku tuna da wannan, ku sa shi a zuciya,

ku riƙe shi a zuciya, ku ’yan tawaye.

9 Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā;

ni ne Allah, kuma babu wani;

ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.

10 Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko,

daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba.

Na ce nufina zai tabbata,

kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.

11 Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta;

daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina.

Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru;

abin da na shirya, shi zan aikata.

12 Ku kasa kunne, ku masu taurinkai,

ku da kuke nesa da adalci.

13 Ina kawo adalcina kusa,

ba shi da nisa;

kuma cetona ba zai jinkirta ba.

Zan yi wa Sihiyona ceto, darajata ga Isra’ila.

47:1 “Ki gangara, ki zauna a ƙura,

Budurwa Diyar Babilon;

ki zauna a ƙasa ba tare da rawani ba,

Diyar Babiloniyawa.

Ba za a ƙara kira ke marar ƙarfi ’yar gata ba.

2 Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari;

ki kware lulluɓinki.

Ki ɗaga fatarinki ki bar ƙafafunki tsirara,

ki kuma yi ta ratsa cikin rafuffuka.

3 Tsirararki zai bayyana

za a kuma buɗe kunyarki.

Zan ɗauki fansa;

ba zan bar wani ba.”

4 Mai Fansarmu, Ubangiji Maɗaukaki shi ne sunansa,

shi ne Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

5 “Zauna shiru, tafi cikin duhu,

Diyar Babiloniya;

ba za a ƙara kira ke

sarauniyar masarautai.

6 Na yi fushi da mutanena

na ƙazantar da gādona;

na ba su ga hannunki,

ba ki kuwa nuna musu jinƙai ba.

Har ma da tsofaffi

kin jibga musu kaya masu nauyi sosai.

7 Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada,

madawwamiyar sarauniya!’

Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa

ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba.

8 “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi,

mai zama da rai kwance

kina kuma ce wa kanki,

‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.

Ba zan taɓa zama gwauruwa

ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’

9 Duk waɗannan za su sha kanki

cikin farat ɗaya, a rana guda,

rashin ’ya’ya da gwauranci.

Za su zo a kanki da cikakken minzani,

duk da yawan masu dubanki

da kuma dukan sihirinki.

10 Kin dogara a muguntarki

kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’

Hikimarki da saninki sun ɓad da ke

sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’

11 Bala’i zai fāɗo a kanki,

kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba.

Masifa za tă fāɗo a kanki

da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba;

lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba

za tă auko miki nan da nan.

12 “Ki dai ci gaba, da sihirinki

da kuma makarunki masu yawa,

waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya.

Mai yiwuwa ki yi nasara,

mai yiwuwa ki jawo fargaba.

13 Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai!

Bari masananki na taurari su zo gaba,

waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata,

bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.

14 Tabbas suna kama da bunnu;

wuta za tă cinye su ƙaf.

Ba za su ma iya ceton kansu

daga ikon wutar ba.

Ba wutar da wani zai ji ɗumi;

ba wutar da za a zauna kusa da ita.

15 Abin da za su iya yi miki ke nan kawai,

waɗannan da kika yi ta fama da su

kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya.

Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa;

babu ko ɗayan da zai cece ki.