An Tsawata wa Bautar Gumaka

710 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 48

1 “Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub,

waɗanda ake kira da sunan Isra’ila

suka kuma fito daga zuriyar Yahuda,

ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji

kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila,

amma ba da gaskiya ko adalci ba,

2 ku da kuke kiran kanku ’yan ƙasar birni mai tsarki

kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila,

Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,

3 na nanata abubuwan da suka riga suka faru tuntuni,

bakina ya yi shelar su na kuma sanar da su;

sai nan da nan na aikata, suka kuma faru.

4 Gama na san yadda kuke da taurinkai;

jijiyoyin wuyanku ƙarafa ne,

goshinku tagulla ne.

5 Saboda haka na faɗa waɗannan abubuwa tuntuni;

kafin su faru na yi shelarsu gare ku

saboda kada ku ce,

‘Gumakana ne suka yi su;

siffar itacena da allahn zinariyana ne ya ƙaddara su.’

6 Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka.

Ba za ku yarda da su ba?

“Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa,

na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.

7 Yanzu an halicce su, ba da daɗewa ba;

ba ku riga kun ji game da su kafin yau ba.

Saboda haka ba za ku ce,

‘I, na san da su ba.’

8 Ba ku ji ko balle ku gane ba;

tun da kunnenku bai buɗu ba.

Tabbatacce na san yadda kun zama masu tayarwa;

an kira ku ’yan tawaye daga haihuwa.

9 Saboda girman sunana na jinkirta fushina;

saboda girman yabona na janye shi daga gare ku,

don dai kada a yanke ku.

10 Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba;

na gwada ku cikin wutar wahala.

11 Saboda girmana, saboda girmana, na yi haka.

Yaya zan ƙyale a ƙazantar da kaina?

Ba zan raba ɗaukakata da wani ba.

12 “Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub,

Isra’ila, wanda na kira cewa,

Ni ne shi;

ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe.

13 Hannuna ne ya kafa harsashen duniya,

hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai;

sa’ad da na kira su,

duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya.

14 “Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara,

Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa?

Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna

zai aikata nufinsa a kan Babilon;

hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.

15 Ni kaina, na faɗa;

I, na kira shi.

Zan kawo shi,

zai kuma yi nasara a cikin aikinsa.

16 “Ku zo kusa da ni ku kuma saurari wannan.

“Daga farkon shela ban yi magana a ɓoye ba;

a lokacin da ya faru, ina nan a wurin.”

Yanzu kuwa Ubangiji Mai Iko Duka ya aiko ni,

da Ruhunsa.

17 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce,

“Ni ne Ubangiji Allahnku,

wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau,

wanda ya muku hanyar da za ku bi.

18 Da a ce kawai za ku mai da hankali ga umarnaina,

da salamarku ta zama kamar kogi,

adalcinku kamar raƙuman teku.

19 Da zuriyarku ta zama kamar yashi,

’ya’yanku kamar tsabar hatsin da ba a iya ƙidayawa;

da ba za a taɓa yanke sunansu

balle a hallaka su daga gabana ba.”

20 Ku bar Babilon,

ku gudu daga Babiloniyawa!

Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki

ku kuma furta shi.

Ku aika shi zuwa iyakokin duniya;

ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”

21 Ba su ji ƙishi ba sa’ad da ya bishe su a cikin hamada;

ya sa ruwa ya malalo dominsu daga dutse;

ya tsage dutse

ruwa kuwa ya kwararo.

22 “Babu salama ga mugaye” in ji Ubangiji.

Almasihu Yana Magana da Mutanensa

Ishaya 49

1 Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai;

ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa.

Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni;

tun daga haihuwata ya ambaci sunana.

2 Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi,

cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni;

ya sa na zama kamar kibiya mai tsini

ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa.

3 Ya ce mini, “Kai bawana ne,

Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.”

4 Amma na ce, “Na yi aiki a banza;

na kashe duk ƙarfina a banza da wofi.

Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji,

ladana kuma tana a wurin Allahna.”

5 Yanzu fa Ubangiji ya ce

ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa

don in dawo da Yaƙub gare shi

in kuma tattara Isra’ila gare shi,

gama an girmama ni a gaban Ubangiji

Allahna kuma ne ƙarfina

6 ya ce,

“Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana

don ka maido da kabilar Yaƙub

ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye.

Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai,

don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”

7 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila

gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki,

ga bawan masu mulki.

“Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye,

sarakuna za su gani su kuma rusuna,

saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci,

Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”

8 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“A lokacin tagomashina zan amsa muku,

kuma a ranar ceto zan taimake ku;

zan kiyaye ku zan kuma sa

ku zama alkawari ga mutane,

don ku maido da ƙasa

ku kuma sāke raba gādon kufai,

9 don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’

ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku ’yantu!’

“Za su yi kiwo kusa da hanyoyi

su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu.

10 Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba,

ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba.

Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su

ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa.

11 Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi,

a kuma gyara manyan hanyoyina.

12 Duba, za su zo daga nesa

waɗansu daga arewa, waɗansu daga yamma,

waɗansu daga yankin Aswan.”

13 Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai;

ki yi farin ciki, ya ke duniya;

ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu!

Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa

zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.

14 Amma Sihiyona ta ce, “Ubangiji ya yashe ni,

Ubangiji ya manta da ni.”

15 “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta

ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?

Mai yiwuwa ta manta,

amma ba zan taɓa manta da ke ba!

16 Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;

katangarki kullum suna a gabana.

17 ’Ya’yanki maza su komo da gaggawa,

waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su bar ki.

18 Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye;

dukan ’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki.

Muddin ina raye,” in ji Ubangiji,

“Za ki yafa su duka kamar kayan ado;

za ki yi ado da su, kamar amarya.

19 “Ko da yake an lalatar da ke aka kuma mai da ke kufai

ƙasarki kuma ta zama kango,

yanzu za ki kāsa sosai saboda yawan mutanenki,

kuma waɗanda suka cinye ki za su kasance can da nisa.

20 ’Ya’yan da aka haifa a lokacin baƙin cikinki

za su ce a kunnenki,

‘Wannan wuri ya yi mana kaɗan ƙwarai;

ki ƙara mana wurin zama.’

21 Sa’an nan za ki ce a zuciyarki,

‘Wa ya haifa waɗannan?

Na yi baƙin ciki na kuma zama wadda ba ta haihuwa;

an yi mini daurin talala aka kuma ƙi ni.

Wane ne ya yi renon waɗannan?

An bar ni ni kaɗai,

amma waɗannan, ina suka fito?’ ”

22 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,

“Duba, zan yi alama wa Al’ummai,

zan ɗaga tutana wa mutane;

za su kawo ’ya’yanki maza a hannuwansu

su riƙe ’ya’yanki mata a kafaɗunsu.

23 Sarakuna za su zama kamar iyayen reno,

sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye.

Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa;

za su lashe ƙura a ƙafafunki.

Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji;

waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.”

24 Za a iya ƙwace ganima daga jarumawa,

ko a kuɓutar da kamammu daga hannun marasa tsoro?

25 Amma ga abin da Ubangiji yana cewa,

“I, za a ƙwace kamammu daga jarumawa,

a kuma karɓe ganima daga hannun marasa tsoro;

zan gwabza da waɗanda suke gwabzawa da ke,

zan kuwa ceci ’ya’yanki.

26 Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu;

za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi.

Sa’an nan dukan mutane za su sani

cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki,

Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.”