An Annabta Ƙin Karɓar Kiristi

Annabci game da ƙin karɓar Kiristi da kuma ɗaukakar ikkilisiyarsa ta ƙarshe.

710 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 50:1–52:12

1 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Ina takardar shaida na saki mahaifiyarka daga aure

wadda na kora?

Ko kuwa ga wanda mutumin da nake bin bashi ne

na sayar da kai?

Saboda zunubanka aka sayar da kai;

saboda laifofinka ne ya sa aka kori mahaifiyarka.

2 Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa?

Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa?

Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka?

Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne?

Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku,

na mai da koguna hamada;

kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa

suka kuma mutu saboda ƙishi.

3 Na suturar da sararin sama da duhu

na kuma mai da tsummoki abin rufuwarsa.”

4 Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni,

don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye.

Ya farkar da ni da safe,

ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.

5 Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana,

kuma ban yi tayarwa ba;

ban ja da baya ba.

6 Na ba da bayana ga masu dūkana,

kumatuna ga masu jan gemuna;

ban ɓoye fuskata

daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba.

7 Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni,

ba zan sha kunya ba.

Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara,

na kuma sani ba zan sha kunya ba.

8 Gama shi da zai tabbatar da ni, marar laifi ne yana kusa.

Wane ne zai kawo ƙararraki game da ni?

Bari mu je ɗakin shari’a tare!

Wane ne mai zargina?

Bari yă kalubalance ni!

9 Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni.

Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi?

Duk za su koɗe kamar riga;

asu za su cinye su.

10 Wane ne a cikinku yake tsoron Ubangiji

yana kuma yin biyayya ga maganar bawansa?

Bari wanda yake tafiya cikin duhu,

wanda ba shi da haske,

ya dogara a sunan Ubangiji ya kuma dogara ga Allahnsa.

11 Amma yanzu fa, dukanku waɗanda kuke ƙuna wuta

kuna kuma tanada wa kanku fitilu masu ci,

ku je ku yi tafiya a cikin hasken wutarku

da na fitilun da kuka ƙuna.

Abin da za ku karɓa ke nan daga hannuna.

Za ku kwanta a cikin azaba.

51:1 “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuna neman adalci

kuke kuma neman Ubangiji.

Dubi dutse daga inda aka yanke ku

da kuma mahaƙar duwatsu inda aka fafe ku;

2 dubi Ibrahim, mahaifinku,

da Saratu, wadda ta haife ku.

Sa’ad da na kira shi kaɗai ne,

na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa.

3 Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona

zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta;

zai sa hamadanta ta zama kamar Eden,

ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji.

Za a sami farin ciki da murna a cikinta,

godiya da ƙarar rerawa.

4 “Ku kasa kunne gare ni, mutanena;

ku ji ni, al’ummata.

Doka za tă fito daga gare ni;

shari’ata za tă zama haske ga al’ummai.

5 Adalcina na zuwa da sauri,

cetona yana a kan hanya,

hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai.

Tsibirai za su dube ni

su kuma jira da sa zuciya don hannuna.

6 Ku daga idanunku zuwa sammai

ku dubi duniya a ƙasa;

sammai za su ɓace kamar hayaƙi,

duniya za tă shuɗe kamar riga

mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje.

Amma cetona zai dawwama har abada,

adalcina ba zai taɓa kāsa ba.

7 “Ku ji ni, ku da kuka san abin da yake daidai,

ku mutanen da kuke da dokata a zukatanku.

Kada ku ji tsoron ba’ar da mutane suke yi

ko ku firgita saboda zargin da suke yi.

8 Gama asu za su cinye su kamar riga;

tsutsotsi za su cinye su kamar ulu.

Amma adalcina zai dawwama har abada,

cetona har dukan zamanai.”

9 Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi,

Ya hannun Ubangiji;

ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce,

kamar a zamanai na dā.

Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa,

wanda ya soki dodon ruwan nan?

10 Ba kai ba ne ka busar da teku,

ka busar da ruwan zurfafa masu girma,

wanda ya yi hanya a cikin zurfafan teku

saboda fansassu su ƙetare?

11 Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo.

Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi;

madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani.

Murna da farin ciki zai cika su,

baƙin ciki da nishi zai ɓace.

12 “Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku.

Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa,

’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,

13 har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku,

wanda ya shimfiɗa sammai

ya kuma kafa harsashen duniya,

har kuna zama da tsoro kowace rana

saboda fushin masu zalunci,

waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka?

Gama ina fushin mai zalunci?

14 Ba da daɗewa za a ’yantar da ’yan kurkuku;

ba za su mutu a kurkuku ba,

ba kuwa za su rasa abinci ba.

15 Gama ni ne Ubangiji Allahnku,

wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri,

Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

16 Na sa maganata a bakinka

na kuma rufe ka da inuwar hannuna,

Na shimfiɗa sammai,

na kafa harsashen duniya,

na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’ ”

17 Ki farka, ki farka!

Ki tashi, ya Urushalima,

ke da kika sha daga hannun Ubangiji

kwaf na fushinsa,

ke da kika shanye har ƙasar kwaf

kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.

18 Cikin dukan ’ya’yan da ta haifa;

cikin dukan ’ya’yan da ta yi reno

babu wani da zai kama hannunta.

19 Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki,

wa zai ta’azantar da ke?

Lalaci da hallaka, yunwa da takobi,

wa zai ƙarfafa ki?

20 ’Ya’yanki sun sume;

sun kwanta kusurwar kowane titi,

kamar barewar da aka kama da tarko.

Sun cika da fushin Ubangiji

da kuma tsawatawar Allahnki.

21 Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala,

wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi.

22 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

Allahnki, wanda ya kāre mutanensa,

“Duba, na ƙwace daga hannunki

kwaf da ya sa ki tangaɗi;

daga wannan kwaf, kwaf na fushina,

ba za ki ƙara sha ba.

23 Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba,

waɗanda suke ce miki,

‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’

Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa,

kamar titin da ake takawa a kai.”

52:1 Ki farka, ki farka, ya Sihiyona,

ki sanya wa kanki ƙarfi.

Ki sa rigarki na daraja,

Ya Urushalima, birni mai tsarki.

Marasa kaciya da maƙazanta

ba za su shi cikinki ba.

2 Ki kakkaɓe ƙurarki;

ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima.

Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki,

Ke kamammiyar Diyar Sihiyona.

3 Gama ga abin Ubangiji yana cewa,

“An sayar da ke ba da kuɗi ba,

kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”

4 Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

“Da farko mutanena suka gangara zuwa Masar don su zauna;

a baya-bayan nan, Assuriya sun zalunce su.

5 “Yanzu kuma me nake da shi a nan?”

In ji Ubangiji.

“Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome ba

kuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a,

Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo.

6 Saboda haka mutanena za su san sunana;

saboda haka a wannan rana za su san

cewa ni ne wanda ya faɗa wannan.

I, ni ne.”

7 Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu

a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi

waɗanda suke shelar salama,

waɗanda suke kawo labari mai daɗi,

waɗanda suke shelar ceto,

waɗanda suke ce wa Sihiyona,

“Allahnki yana mulki!”

8 Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu;

tare sun yi sowa ta farin ciki.

Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona,

za su gan shi da idanunsu.

9 Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya,

kangonki na Urushalima,

gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa,

ya fanshi Urushalima.

10 Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili

a idanun dukan al’ummai,

da kuma dukan iyakokin duniya za su gani

ceton Allahnmu.

11 Ku fita, ku fita daga can!

Kada ku taɓa wani abu marar tsarki!

Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki,

ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji.

12 Amma ba za ku fita a gaggauce ba

ko ku tafi da gudu;

gama Ubangiji zai ja gabanku,

Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku.