Sashe na 7: Zunubin Solomon
980 zuwa 975 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa. 2 Sun fito daga al’ummai da Ubangiji ya ce wa Isra’ilawa, “Kada ku yi aurayya da su, domin tabbatacce za su juye zukatanku zuwa ga waɗansu alloli.” Duk da haka Solomon ya manne musu, ya nace, yana ƙaunarsu. 3 Ya auri mata ɗari bakwai, haifaffun gidan sarauta, da kuma ƙwarƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa suka karkatar da shi. 4 Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba. 5 Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. 6 Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba.
7 A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. 8 Ya yi haka domin dukan baƙin matansa, waɗanda suka ƙone turare suka kuma miƙa hadayu ga allolinsu.
9 Ubangiji ya yi fushi da Solomon domin zuciyarsa ya juye daga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana masa sau biyu. 10 Ko da yake ya hana Solomon bin waɗansu alloli, Solomon bai kiyaye umarnin Ubangiji ba. 11 Saboda haka Ubangiji ya ce wa Solomon, “Da yake halinka ke nan, ba ka kuma kiyaye alkawarina, da ƙa’idodina da na umarce ka ba, tabbatacce zan yage masarautar daga gare ka, in ba da ita ga ɗaya daga cikin bayinka. 12 Amma saboda Dawuda mahaifinka, ba zan yi haka a zamaninka ba. Zan yage ta daga hannun ɗanka. 13 Amma ba zan yage dukan masarautar daga gare shi ba, zan ba shi kabila ɗaya saboda Dawuda bawana, da kuma saboda Urushalima, wadda na zaɓa.”
14 Sai Ubangiji ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Hadad, mutumin Edom daga gidan sarautar Edom.
23 Allah kuwa ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Rezon, ɗan Eliyada, wanda ya gudu daga maigidansa, Hadadezer sarkin Zoba. 24 Rezon ya tattara mutane kewaye da shi, ya zama kuma shugaban ’yan tawaye sa’ad da Dawuda ya hallaka mayaƙan Zoba; ’yan tawayen suka tafi Damaskus, inda suka zauna, suka kuma yi mulki. 25 Rezon ya zama babban abokin gāban Isra’ila cikin dukan kwanakin mulkin Solomon. Ya ƙara rikici a kan rikicin Hadad. Rezon ya ƙi mulkin Isra’ila da dukan ransa. Saboda haka Rezon ya yi mulki a Aram ya kuma ƙi jinin Isra’ila.
26 Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa.
27 Ga yadda ya tayar wa sarki Solomon. Sarki Solomon ya gina madogaran gini, ya ciccika wurare a katangar birnin Dawuda mahaifinsa da ƙasa. 28 To, Yerobowam mutum ne mai fasaha. Sa’ad da Solomon ya ga yadda matashin yake aiki da himma, sai ya sa shi yă lura da dukan aikin gandu na gidan Yusuf.
29 Da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahiya, mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahiya yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai. 30 Sai Ahiya ya kama sabuwar rigar da yake saye da ita ya yage ta gida goma sha biyu. 31 Sa’an nan ya ce wa Yerobowam, “Ɗauki gida goma wa kanka, gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce ke nan, ‘Duba, zan yage masarauta daga hannun Solomon in ba ka kabilu goma. 32 Amma saboda bawana Dawuda da kuma birnin Urushalima, wadda na zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila, zai sami kabila guda. 33 Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.
34 “ ‘Amma ba zan ɗauki dukan masarautar daga hannun Solomon ba; na naɗa shi sarki, dukan kwanaki ransa saboda Dawuda bawana, wanda na zaɓa, wanda kuma ya kiyaye umarnai da farillaina. 35 Zan ɗauke masarautar daga hannuwan ɗansa ne, in ba ka kabilu goma. 36 Zan ba da ɗaya ga ɗansa don kullum Dawuda bawana yă kasance da fitila a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa Sunana. 37 Amma fa, ga kai, zan ɗauke ka, za ka kuwa yi mulki bisa dukan abin da zuciyarka take so; za ka zama sarki a bisa Isra’ila. 38 In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka. 39 Zan ƙasƙantar da zuriyar Dawuda saboda wannan, amma ba har abada ba.’ ”
40 Solomon ya yi ƙoƙari yă kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tsere zuwa Masar, zuwa wurin sarki Shishak, ya zauna a can sai bayan mutuwar Solomon.
1 Kalmomin Malami, ɗan Dawuda, Sarki a Urushalima.
2 “Ba amfani! Ba amfani!”
In ji Malami.
“Gaba ɗaya ba amfani!
Kome ba shi da amfani!”
3 Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar
da yake fama a duniya?
4 Zamanai sukan zo zamanai su wuce,
amma duniya tana nan har abada.
5 Rana takan fito rana ta kuma fāɗi,
ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.
6 Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa;
tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
7 Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku,
duk da haka teku ba ya cika.
Daga inda rafuffukan suke fitowa,
a can suke komawa kuma.
8 Dukan abubuwa suna kawo gajiya,
gaban magana.
Ido ba ya gaji da gani,
haka ma kunne yă ƙoshi da ji.
9 Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance,
abin da aka yi za a sāke yi kuma;
babu wani abu sabo a duniya.
10 Akwai wani abin da za a ce,
“Duba! Ga wani abu sabo”?
Abin yana nan, tun dā can,
ya kasance kafin lokacinmu.
11 Ba a tunawa da mutanen dā,
haka su ma da ba a haifa ba tukuna
waɗanda za su biyo bayansu
ba za a tuna da su ba.
12 Ni, Malami, sarki ne bisa Isra’ila a Urushalima. 13 Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane! 14 Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai.
15 Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba;
ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba.
16 Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.” 17 Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.
18 Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki;
yawan sani, yawan ɓacin rai.