Sashe na 7: Zunubin Solomon (continued)
980 zuwa 975 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Na ce wa kaina, “Zo, zan gwada ka da jin daɗi don in ga abin da yake da kyau.” Amma wannan ma ya zama ba amfani. 2 Sai na ce, “Dariya hauka ce. Kuma me jin daɗi yake kawowa?” 3 Na yi ƙoƙari in sa raina yă yi farin ciki da ruwan inabi, in kuma rungumi wauta, hankalina kuma yana yin mini jagora da hikima. Na so in ga abin da yake da daraja ga mutane a duniya a ’yan kwanakinsu.
4 Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi. 5 Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu. 6 Na yi tankuna don in yi banruwan kurmin itatuwa. 7 Na sayi bayi mata da maza, ina kuma da waɗansu bayin da aka haifa a gidana. Ina da garkunan shanu da na tumaki da na awaki fiye da duk wanda ya taɓa zama a Urushalima kafin ni. 8 Na tara wa kaina azurfa da zinariya, ina da ma’ajin sarakuna da yankuna. Na samo wa kaina mawaƙa mata da maza, da dukan irin matan da kowane namiji zai so. 9 Na ƙasaita fiye da kowane mutumin da ya riga ni zama a Urushalima. Cikin dukan wannan, hikimata ba tă rabu da ni ba.
10 Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba;
ban hana zuciyata wani jin daɗi ba.
Zuciyata ta yi murna da dukan aikina,
wannan kuwa shi ne ladan dukan famata.
11 Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana,
da abin da na yi fama don in samu,
sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai;
babu wata riba a duniya.
12 Sai na juya ga tunanina don in lura da hikima,
da kuma hauka da wauta.
Me ya rage wa magājin sarki yă yi
fiye da abin da aka riga aka yi?
13 Na ga cewa hikima ta fi wauta,
kamar yadda haske ya fi duhu.
14 Mai hikima ya san inda ya nufa,
wawa kuwa yana tafiya a cikin duhu;
amma sai na gane
cewa ƙaddara ɗaya ce take samunsu.
15 Sai na yi tunani a zuciyata,
“Ƙaddarar wawa za tă same ni ni ma.
Wace riba ce hikimata za tă jawo mini?”
Na ce a zuciyata,
“Wannan ma ba shi da amfani.”
16 Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba;
nan gaba za a manta da su.
Yadda wawa zai mutu, haka ma mai hikima!
17 Don haka na ƙi jinin rayuwa, gama aikin da ake yi a duniya yana ɓata mini rai. Dukan abin da yake cikinta kuwa ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. 18 Na ƙi jinin dukan abubuwan da na yi wahala ina yi a duniya, gama dole in bar su wa na bayana. 19 Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani. 20 Saboda haka zuciyata ta fara karaya a kan dukan faman aikina a duniya. 21 Gama mutum zai yi aikinsa da dukan hikimarsa, da saninsa, da gwanintarsa, sa’an nan dole yă bar dukan abin da ya mallaka ga wani wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma ba shi da amfani, hasara ce mai yawa. 22 Me mutum zai samu daga aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin a duniya? 23 Dukan kwanakinsa aikinsa damuwa ce da ɓacin zuciya; ko da dare ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Wannan ma ba shi da amfani.
24 Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne, 25 gama in ba tare da shi ba, wa zai iya ci yă sha yă kuma ji daɗi? 26 Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
3:1 Akwai lokaci domin kowane abu,
da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2 Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,
lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3 Lokacin kisa da lokacin warkarwa,
lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4 Lokacin kuka da lokacin dariya,
lokacin makoki da lokacin rawa.
5 Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su,
lokacin runguma da lokacin dainawa.
6 Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya,
lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7 Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa,
lokacin yin shiru da lokacin magana.
8 Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya,
lokacin yaƙi da lokacin salama.
9 Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa? 10 Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane. 11 Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe. 12 Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai. 13 Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce. 14 Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi.
15 Duk abin da yana nan ya taɓa kasancewa,
kuma abin da zai kasance, ya taɓa kasancewa;
Allah kuma zai nemi bayanin abubuwan da suka wuce.
16 Sai na ga wani abu kuma a duniya,
a wurin shari’a, akwai mugunta a can,
a wurin adalci, akwai mugunta a can.
17 Sai na yi tunani a zuciyata,
“Allah zai shari’anta
masu adalci da masu mugunta,
gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki,
lokaci domin kowane abu.”
18 Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba. 19 Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani. 20 Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma. 21 Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”
22 Saboda haka na ga babu abin da ya fi kyau wa mutum fiye da yă more wahalar aikinsa, domin wannan ne rabonsa. Gama wa zai kawo shi yă ga abin da zai faru a bayansa?