Sashe na 7: Zunubin Solomon (continued)

980 zuwa 975 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mai Hadishi 4–5

1 Na sāke dubawa sai na ga zaluncin da ake yi a duniya.

Na ga hawayen waɗanda ake zalunta

kuma ba su da mai taimako;

masu iko suna goyon bayan masu zalunci,

ga shi ba su da mai taimako.

2 Sai na furta cewa matattu,

waɗanda suka riga suka mutu,

sun fi waɗanda suke a raye farin ciki,

waɗanda har yanzu suke da rai.

3 Amma wanda ya fi su duka

shi ne wanda bai riga ya kasance ba,

wanda bai ga muguntar

da ake yi a duniya ba.

4 Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

5 Wawa yakan kame hannuwansa

yă kuma lalatar da kansa.

6 Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai

da tafin hannu biyu cike da tashin hankali

da harbin iska kawai.

7 Na kuma ga wani abu marar amfani a duniya.

8 Akwai wani mutum shi kaɗai;

bai shi da ɗa ko ɗan’uwa.

Ba shi da hutu daga wahalarsa,

duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba.

Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala,

kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?”

Wannan ma ba shi da amfani,

harkar baƙin cikin ne kawai!

9 Biyu sun fi ɗaya,

gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

10 In ɗaya ya fāɗi,

abokinsa zai taimake shi yă tashi.

Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi

ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!

11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.

Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?

12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,

mutum biyu za su iya kāre kansu.

Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.

13 Gara saurayi wanda yake matalauci amma yake da hikima da sarkin da ya tsufa mai wauta, wanda ba ya karɓar shawara. 14 Yana yiwuwa saurayin yă fito daga kurkuku yă hau gadon sarauta, ko kuma dai an haife shi cikin talauci a ƙasarsa. 15 Na ga cewa dukan waɗanda suka rayu suka kuma yi tafiya a duniya sun bi saurayin, magājin sarkin. 16 Babu ƙarshe ga dukan mutanen da suka riga su. Amma waɗanda suka zo daga baya, ba su gamsu da magājin ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

5:1 Ka lura da matakanka sa’ad da ka tafi gidan Allah. Ka je kusa don ka saurara a maimakon miƙa hadaya kamar wawaye, waɗanda ba su san sun yi laifi ba.

2 Kada ka yi subul da bakinka,

kada zuciyarka tă yi garajen

furta wani abu a gaban Allah.

Allah yana sama

kai kuma kana duniya,

saboda haka, kada kalmominka su zama da yawa.

3 Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa,

haka jawabin wawa yake sa’ad da yake yawan magana.

4 Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka. 5 Gara kada ka yi alkawari, da ka yi amma ba ka cika ba. 6 Kada ka bar bakinka ya kai ga yin zunubi. Kada kuma ka kai ƙara wurin ɗan saƙon haikali cewa, “Alkawarin da na yi kuskure ne.” Me ya sa Allah yake fushi a kan abin da ka faɗa har yă lalatar da aikin hannuwanka? 7 Yawan buri da yawan magana ba su da amfani. Saboda haka, ka ji tsoron Allah.

8 In ka ga ana zaluntar matalauta a wani yanki, ba a yin adalci, ana kuma tauye hakki, kada ka yi mamakin waɗannan abubuwa; domin akwai wani jami’in da yake bisa da wani, a bisansu biyu kuwa akwai wani. 9 Kowa yakan amfana da bunkasar amfanin ƙasa, sarki kansa yana samun riba daga gonaki.

10 Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe;

duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu.

Wannan ma ba shi da amfani.

11 Kamar yadda kaya suke haɓaka,

haka ma masu amfani da su.

Kuma wane amfani ne suke ga mai shi

in ba ciyar da idanunsa a kansu ba?

12 Barcin ma’aikaci daɗi gare shi,

ko yă ci kaɗan ko da yawa,

amma yalwar mai arziki

ba ta barinsa yă iya yin barci.

13 Na ga wani mugun abu a duniya,

arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi,

14 ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara,

har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa,

babu abin da ya bar masa.

15 Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa,

kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma.

Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa

da zai riƙe a hannunsa.

16 Wannan ma mugun abu ne,

Yadda mutum ya zo, haka zai koma,

to, wace riba ce ya ci,

da yake ya yi wahalar iska ce kawai?

17 Duk rayuwarsa ya ci abinci a cikin duhu,

da ɓacin rai mai tsanani, da azaba, da fushi.

18 Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa. 19 Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah. 20 Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki.